TALIFIN NAZARI NA 50
WAƘA TA 48 Mu Riƙa Bauta wa Jehobah Kullum
Mu Zama Masu Sauƙin Kai Kamar Jehobah
“Tun da yake kun zama ꞌyaꞌya waɗanda Allah yake ƙauna, sai ku ɗauki misali daga wurin Allah.”—AFIS. 5:1.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga hanyoyi huɗu da za mu iya nuna sauƙin kai kamar Jehobah.
1. Me ya fi burge ka game da yadda Jehobah yake da sauƙin kai?
SHIN, kana ganin masu mulki a yau suna da sauƙin kai? Ba lallai ba. Amma Jehobah, wanda shi ne Maɗaukaki yana da sauƙin kai. (Zab. 113:5-8) Babu wanda yake da sauƙin kai kamar Jehobah. Kuma babu girman kai tattare da shi ko kaɗan. A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi huɗu da Jehobah yake bi da mu. Da yadda kowannensu ya nuna cewa Jehobah mai sauƙin kai ne sosai. Za mu kuma ga yadda Yesu ya nuna sauƙin kai kamar Jehobah. Tattauna waɗannan abubuwan za su taimaka mana mu ƙara kusantar Jehobah kuma mu daɗa zama da sauƙin kai kamar shi.
JEHOBAH YANA SHIRYE YA SAURARE MU
2. Mene ne Zabura 62:8 ya koya mana game da Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)
2 Yi wa mutane masu girman kai magana bai da sauƙi. Da yake suna ganin cewa sun fi sauran mutane, hakan yakan sa mutane su guje su. Amma ba haka Jehobah yake ba! Shi mai sauƙin kai ne. Don haka, yana so mu gaya masa dukan damuwarmu a cikin adduꞌa. (Karanta Zabura 62:8.) Kamar yadda uba mai ƙauna yake shirye ya saurari yaransa idan suna cikin damuwa, haka ma Jehobah yake so ya saurari adduꞌoꞌin bayinsa. Ya sa an rubuta adduꞌoꞌin bayinsa da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki. Hakan ya nuna cewa yana so ya saurare mu. (Yosh. 10:12-14; 1 Sam. 1:10-18) Amma me ya kamata mu tuna idan a wasu lokuta mun ga kamar ba za mu iya yin adduꞌa domin kurakurenmu ba?
Kamar yadda Jehobah yake yi, wani mahaifi yana sauraron ɗansa da ya fasa abin saka fulawa saꞌad da yake wasa (Ka duba sakin layi na 2)
3. Me ya sa za ka iya kasance da tabbaci cewa Jehobah yana so ka riƙa adduꞌa kullum?
3 Ko da muna ganin kamar Jehobah ba ya ƙaunarmu, zai dace mu yi adduꞌa gare shi. Me ya sa muka ce haka? A kwatancin mubazzari da Yesu ya bayar, ya ce Jehobah yana kama da uba mai ƙauna wanda ɗansa ya yi kurakure da yawa, har ɗan ya ga kamar ubansa ba zai taɓa gafarta masa ba. Mene ne uban ya yi da ɗansa ya dawo gida? Yesu ya ce, da uban ya hangi ɗansa, sai “ya gudu ya same shi, ya rungume shi, kuma ya yi masa sumba.” (Luk. 15:17-20) Haka Jehobah ma yake, idan muna adduꞌa don muna baƙin ciki ko don wani kuskuren da muka yi, yana saurarar mu. (Mak. 3:55-57) Jehobah yana tausaya mana, kuma kamar yadda uban ya gudu zuwa wurin ɗansa don ya tabbatar masa cewa yana ƙaunarsa, haka ma Jehobah yake yi. (Isha. 57:15) Ta yaya yake yin hakan a yau? Yana yin hakan ta wurin dattawa, da ꞌyan iyalinmu, da kuma ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. (Yak. 5:14, 15) Jehobah yana taimaka mana don yana so mu kusace shi.
4. Me ya sa zuwa wurin Yesu ya yi wa mutane sauƙi?
4 Yadda Yesu ya yi koyi da Ubansa. Yesu yana da sauƙin kai kamar Jehobah. Hakan ya sa saꞌad da yake duniya, mutane sun so zuwa wurinsa. Ba sa tsoron yi masa tambayoyi. (Mar. 4:10, 11) Idan ya nemi raꞌayinsu game da wani abu, suna gaya masa ainihin yadda suke ji. (Mat. 16:13-16) Kuma idan suka yi kuskure, ba sa tsoron cewa Yesu zai yi fushi da su don sun san shi mai alheri ne, mai jinƙai, da kuma haƙuri. (Mat. 17:24-27) Da yake Yesu ya yi koyi da Ubansa sosai, hakan ya taimaka wa mabiyansa su ƙara sanin Jehobah. (Yoh. 14:9) Misalin da Yesu ya kafa, ya koya musu cewa Jehobah mai sauƙin kai ne kuma yana so ya kusace su. Kuma Jehobah ba kamar shugabannin addinansu masu girman kai da marar tausayi ba ne.
5. Me ya sa zai yi wa mutane sauƙi su kusace mu idan mu masu sauƙin kai ne?
5 Yadda za mu yi koyi da Jehobah. Idan mu masu sauƙin kai ne, hakan zai sa ya yi wa mutane sauƙi su yi mana magana. Rashin nuna sauƙin kai yana sa mutum ya yi ƙishin wasu, ya ji kamar ya fi wasu, kuma ya ƙi gafartawa mutanen da suka yi masa laifi. Idan haka muke, mutane ba za su so su zama abokanmu ba. Amma sauƙin kai zai taimaka mana mu zama masu alheri da haƙuri da kuma gafartawa, hakan zai sa mutane su kusace mu. (Kol. 3:12-14) Dattawa musamman suna bukata su tabbata cewa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya za su iya zuwa wurinsu kuma su gaya musu yadda suke ji. Hakan zai yiwu ne idan suna kasancewa tare da ꞌyanꞌuwa. Shi ya sa zai fi kyau dattawa su halarci taro a Majamiꞌa Mulki maimakon ta naꞌura. Ƙari ga haka, zai dace su yi iya ƙoƙarinsu su riƙa zuwa waꞌazi gida-gida tare da ꞌyanꞌuwa. Yin hakan zai sa su saba da ꞌyanꞌuwa, kuma zai yi wa ꞌyanꞌuwa sauƙi su nemi taimakonsu a lokacin da suke bukata.
JEHOBAH YANA SHIRYE YA CANJA RAꞌAYINSA
6-7. Ka ba da misalan da suka nuna cewa Jehobah yana shirye ya canja raꞌayinsa idan da bukata.
6 Mutane masu girman kai suna ganin kamar sun fi kowa wayo, kuma ba su da niyyar canja raꞌayinsu. Amma ba haka Jehobah yake ba. Duk da cewa shi ne Maɗaukaki, shi mai sauƙin kai ne kuma yana a shirye ya canja raꞌayinsa. Ka yi laꞌakari da yadda ya bi da Maryamu ꞌyarꞌuwar Musa. Ita da Haruna sun faɗi abin da bai dace ba game da Musa. Kuma hakan laifi ne domin shi wakilin Jehobah ne. Abin da Maryamu ta yi ya nuna cewa ba ta daraja Jehobah ba. Hakan ya sa Jehobah fushi har ya sa ta kamu da cutar kuturta. Amma saꞌad da Haruna da Musa suka roƙi Jehobah ya warkar da ita, mene ne Jehobah ya yi? Da wani mai girman kai ne, da ba zai canja raꞌayinsa ba. Amma Jehobah mai sauƙin kai ne. Hakan ya sa ya saurare su kuma ya warkar da ita.—L. Ƙid. 12:1-15.
7 Jehobah ya kuma nuna cewa shi mai sauƙin kai ne a yadda ya bi da Sarki Hezekiya. Ta bakin annabi Ishaya, Jehobah ya gaya wa sarkin cewa zai mutu. Hezekiya ya yi kuka ya roƙi Jehobah ya warkar da shi. Jehobah ya saurare shi kuma ya gaya masa cewa zai ƙara masa shekaru 15. (2 Sar. 20:1, 5, 6) Babu shakka Jehobah yana tausaya mana. Kuma da yake shi mai sauƙin kai ne, yana da niyyar saurarar mu.
8. Waɗanne misalai ne suka nuna cewa Yesu mutum ne mai sanin ya kamata? (Markus 3:1-6)
8 Yadda Yesu ya yi koyi da Ubansa. Saꞌad da Yesu yake duniya, ya yi wa mutane alheri a duk lokacin da zai iya yin hakan. Alal misali, ya warkar da mutane a ranar Assabaci duk da cewa shugabannin addinai a lokacin sun ga kamar hakan bai dace ba. (Karanta Markus 3:1-6.) Har wa yau, Yesu ya ci-gaba da nuna sanin ya kamata a yadda yake yi wa ikilisiya ja-goranci. Alal misali, idan wani ya yi zunubi mai tsanani, yakan ba shi dama ya canja halinsa.—R. Yar. 2:2-5.
9. Ta yaya za mu nuna cewa mu masu sanin ya kamata ne? (Ka kuma duba hotunan.)
9 Yadda za mu yi koyi da Jehobah. Kamar Jehobah, wajibi ne mu nuna sanin ya kamata a yadda muke tunani da kuma abubuwan da muke yi. (Yak. 3:17) Alal misali, iyayen da suke koyi da Jehobah ba za su so yaransu su yi abin da ya fi ƙarfinsu ba. Yakubu ya nuna misali mai kyau a yin hakan kamar yadda yake a littafin Farawa 33:12-14. Iyaye masu sauƙin kai da kuma sanin ya kamata, ba za su sa yaransu su ji kamar wani ya fi wani ba. Ƙari ga haka, dattawa ma suna bukata su riƙa nuna sanin ya kamata. Alal misali, bai kamata ɗaya daga cikinsu ya ce sam sai an bi raꞌayinsa ba. A maimakon haka, zai dace ya bi raꞌayin sauran dattawan idan raꞌayinsu bai saɓa wa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ba. (1 Tim. 3:2, 3) Amma ba dattawa ne kawai suke bukata su yi hakan ba. Dukanmu muna bukatar mu yi ƙoƙari mu fahimci yadda wasu suke tunani da yadda suke ji, ko da raꞌayinmu dabam ne da nasu. (Rom. 14:1) Dukanmu a ikilisiya, muna bukatar mu yi ƙoƙari mu sa kowa ya ga cewa mu “masu sanin ya kamata” ne.—Filib. 4:5, NWT.
Mahaifi da ke nuna sanin ya kamata ba zai so yaransa su yi abin da ya fi ƙarfinsu a waꞌazi ba (Ka duba sakin layi na 9)
JEHOBAH, ALLAH NE MAI HAƘURI
10. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya nuna cewa shi mai haƙuri ne?
10 Masu girman kai, ba su da haƙuri. Amma ba haka Jehobah yake ba. Babu wanda ya kai shi haƙuri! Alal misali, a zamanin Nuhu, Jehobah ya ce zai jira har shekaru 120 kafin ya hallaka mugaye. (Far. 6:3) Hakan ya ba wa Nuhu dama ya reni yaransa kuma ya gina jirgi. Daga baya, Jehobah ya yi haƙuri ya saurari Ibrahim saꞌad da yake masa tambayoyi game da yadda zai hallaka Sodom da Gomora. Da wani mai girman kai ne, wataƙila da ya ce, ‘ba ka isa ka yi min irin tambayoyin nan ba.’ Amma da yake Jehobah mai sauƙin kai ne, ya yi haƙuri da Ibrahim.—Far. 18:20-33.
11. Bisa ga 2 Bitrus 3:9, me ya sa Jehobah ya ci-gaba da haƙuri har wa yau?
11 A yau ma, Jehobah ya ci-gaba da yin haƙuri. Yana jiran lokacin da ya shirya kafin ya kawo ƙarshen zamanin nan. Me ya sa Jehobah ya ci-gaba da yin haƙuri? Domin “ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.” (Karanta 2 Bitrus 3:9.) Shin, a banza ne Jehobah ya kasance da haƙuri? Aꞌa! Haƙurin da Jehobah yake yi, ya taimaka wa miliyoyin mutane su kusace shi. Kuma muna fatan cewa miliyoyin mutane za su ƙara yin hakan. Amma Jehobah ba zai ci-gaba da yin haƙuri da mugaye har abada ba. Ko da yake Jehobah yana ƙaunar dukan mutane, ba zai ci-gaba da barin su su yi yadda suka ga dama ba. Nan ba da daɗewa ba, zai kawo ƙarshen mugunta.—Hab. 2:3.
12. Ta yaya Yesu yake nuna cewa shi mai haƙuri ne kamar Jehobah?
12 Yadda Yesu ya yi koyi da Ubansa. Yesu ya yi dubban shekaru yana haƙuri kamar Jehobah. Yesu ya ga yadda Shaiɗan yake tabka ƙarya game da Jehobah da ꞌyanꞌadam masu aminci. (Far. 3:4, 5; Ayu. 1:11; R. Yar. 12:10) Ya kuma ga irin wahalar da mutane suke sha. Babu shakka, ya daɗe yana so “ya rushe ayyukan Shaiɗan”! (1 Yoh. 3:8) Me ya taimaka wa Yesu ya kasance da haƙuri kuma ya ci-gaba da jira har sai Jehobah ya ce lokaci ya yi da zai kawo ƙarshen dukan ayyukan Shaiɗan? Dalilin shi ne, Yesu mai sauƙin kai ne. Ya san cewa Jehobah ne kaɗai yake da ikon faɗan lokacin da ƙarshen zai zo.—A. M. 1:7.
13. Ta yaya Yesu ya yi haƙuri da manzaninsa, kuma me ya sa?
13 Yesu ya kuma nuna cewa shi maihaƙuri ne saꞌad da yake duniya. Ta yaya ya yi hakan? Ta wajen yin haƙuri da manzanninsa. Alal misali, saꞌad da manzanninsa suka yi ta gardama a kan waye ne babba a tsakaninsu, Yesu bai yi fushi da su ba. A maimakon haka, ya ci-gaba da yin haƙuri da su. (Luk. 9:46; 22:24-27) Yana da tabbaci cewa da shigewar lokaci, za su ƙara zama masu sauƙin kai. Kai kuma fa? Ka taɓa maimaita kuskure iri ɗaya? Tuna cewa muna da Sarki mai haƙuri da kuma sauƙin kai zai taimaka mana kada mu ga kamar tamu ta ƙare!
14. Me zai taimaka mana mu zama masu haƙuri?
14 Yadda za mu yi koyi da Jehobah. Idan muna tunani kamar yadda Yesu yake yi, hakan zai taimaka mana mu kasance da raꞌayin Jehobah a kome da muke yi. (1 Kor. 2:16) Me zai taimaka mana mu riƙa yin tunani kamar Yesu? Wani abin da zai taimaka mana shi ne, karanta labarin hidimar Yesu da ke Littafi Mai Tsarki. Saꞌan nan mu yi tunani a kan abin da Yesu ya yi, da dalilin da ya sa ya yi hakan. Ƙari ga haka, muna bukatar mu roƙi Jehobah ya taimaka mana don mu zama masu haƙuri da sauƙin kai kamar Yesu. Idan mun ci-gaba da yin tunani kamar Yesu, hakan zai taimaka mana mu ƙara yin koyi da Jehobah kuma mu zama masu haƙuri da mutane da kuma kanmu.—Mat. 18:26-30, 35.
JEHOBAH YANA DARAJA MASU SAUƘIN KAI
15. Ka ba da misalan da suka nuna cewa Jehobah yana daraja masu sauƙin kai. (Zabura 138:6)
15 Karanta Zabura 138:6. Ko da yake Jehobah ne Maɗaukaki mai iko duka, yana daraja masu sauƙin kai, kuma hakan babban gata ne! Akwai mutane da yawa da mutane za su iya ganin kamar su ba kome ba ne. Amma Jehobah ya san da zamansu kuma yana daraja su. Wasunsu ba sanannu ba ne, amma Jehobah ya sa labaransu a Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Deborah ta yi wa iyalin Ishaƙu da Yakubu hidima na tsawon shekaru 125! Ko da yake ba mu san abubuwa da yawa game da wannan mata mai aminci ba, Jehobah ya sa an rubuta yadda aka ƙaunace ta a Littafi Mai Tsarki. (Far. 24:59; 35:8) Ɗarurruwan shekaru bayan hakan, Jehobah ya naɗa wani yaro makiyayi mai suna Dauda ya zama sarkin Israꞌila. (2 Sam. 22:1, 36) Jim kaɗan bayan da aka haifi Yesu, Jehobah ya tura malaꞌiku zuwa wurin wasu makiyaya. Kuma ya ba su gatan zama mutane na farko da suka san cewa an haifi Yesu a Baitalami. (Luk. 2:8-11) Ƙari ga haka, a lokacin da Yusufu da Maryamu suka kai Yesu haikali, Jehobah ya ba wa wasu tsofaffi biyu wato, Simeyon da Anna gatan ganinsa. (Luk. 2:25-30, 36-38) A gaskiya, “ko da yake Yahweh yana can sama, yakan kula da masu sauƙin kai”!
16. Ta yaya Yesu ya yi koyi da yadda Jehobah yake daraja mutane?
16 Yadda Yesu ya yi koyi da Ubansa. Kamar Ubansa, Yesu ya daraja mutane masu sauƙin kai. Ya koya wa “marasa ilimi ne da kuma talakawa” gaskiya game da Mulkin Allah. (A. M. 4:13; Mat. 11:25) Yesu ya kuma warkar da marasa lafiya a hanyar da ta nuna cewa yana daraja su da kuma ƙaunar su. (Luk. 5:13) Ƙari ga haka, kafin ya mutu, ya wanke ƙafafun almajiransa, aikin da bayi ne kaɗai suke yi. (Yoh. 13:5) Kuma kafin ya koma sama, ya ba wa dukan mabiyansa har da mu ma gatan taimaka wa mutane su sami rai na har abada.—Mat. 28:19, 20.
17. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa muna daraja mutane? (Ka kuma duba hoton.)
17 Yadda za mu yi koyi da Jehobah. Za mu nuna cewa muna ƙauna da kuma daraja mutane idan muna yi wa kowa waꞌazi ba tare da nuna bambanci ba. Kuma za mu nuna cewa muna daraja ꞌyanꞌuwanmu, idan ba ma nuna mun fi su don wata baiwa ko aikin da muke da shi a ƙungiyar Jehobah. (Filib. 2:3) Jehobah yana farin ciki idan muna “zama a kan gaba wajen girmama” mutane a hanyoyin nan da dai sauransu.—Rom. 12:10; Zaf. 3:12.
Muna nuna cewa mu masu sauƙin kai ne kamar Jehobah idan muna yi wa kowa da kowa waꞌazi (Ka duba sakin layi na 17)a
18. Me ya sa kake so ka kasance da sauƙin kai kamar Jehobah?
18 Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu zama masu sauƙin kai kamar Jehobah, hakan zai sa ya yi wa mutane sauƙi su gaya mana ainihin yadda suke ji. Za mu zama masu sanin ya kamata da kuma masu haƙuri. Ƙari ga haka, za mu riƙa daraja mutane kamar yadda Jehobah yake yi. Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu zama masu sauƙin kai kamar Jehobah, hakan zai sa mu ƙara zama da daraja a gunsa!—Isha. 43:4.
WAƘA TA 159 Mu Ɗaukaka Jehobah
a BAYANI A KAN HOTUNA: ꞌYanꞌuwa mata biyu da suke koyi da Jehobah suna yin nazari da matan da ke kurkuku.