TALIFIN NAZARI NA 39
WAƘA TA 125 Masu Jinƙai Suna Farin Ciki!
Bayarwa Za Ta Sa Ka Farin Ciki
“Bayarwa tana sa mutum farin ciki fiye da karɓa.” —A. M. 20:35, NWT.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga hanyoyi da za mu iya bayarwa, da kuma yadda yin hakan zai sa mu ƙara yin farin ciki.
1-2. Me ya sa za mu ce Jehobah ya yi mana alheri sosai da ya halicce mu yadda za mu fi yin farin ciki idan muka bayar?
JEHOBAH ya halicci mutane yadda za su yi farin ciki idan suna yin alheri, fiye da idan su ne aka yi wa alherin. (A. M. 20:35) Amma hakan ba ya nufi cewa idan aka yi mana alheri, ba za mu yi farin ciki ba. Dukanmu mukan ji daɗi idan aka yi mana alheri ko aka ba mu wani abu. Amma za mu fi yin farin ciki idan mu ne muka bayar. A gaskiya, Jehobah ya yi mana alheri sosai da ya halicce mu a wannan hanyar. Me ya sa muka ce haka?
2 Wannan hayar da Jehobah ya halicce mu ya sa za mu iya yin abin da zai sa mu farin ciki. Kuma idan muka ƙara yin alheri, za mu ƙara yi farin ciki. Hakika, ba ƙaramin alheri ba ne Jehobah ya yi mana da ya halicce mu haka.—Zab. 139:14.
3. Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “Allah mai farin ciki” ne?
3 Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da cewa bayarwa tana sa mai yin ta farin ciki. Shi ya sa aka ce Jehobah “Allah mai farin ciki” ne. (1 Tim. 1:11, NWT) Shi ne ya fara yin alheri, kuma ba wanda ya kai shi bayarwa. Manzo Bulus ya ce “ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance.” (A. M. 17:28) Ba shakka, “kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta daga” wurin Jehobah ne.—Yak. 1:17.
4. Me zai taimaka mana mu ƙara yin farin ciki?
4 Dukanmu za mu so mu ƙara yin irin wannan farin cikin. Amma ta yaya za mu yi hakan? Mu zama masu bayarwa kamar Jehobah. (Afis. 5:1) A talifin nan, za mu ga yadda za mu yi haka, da kuma abin da za mu yi idan muna ganin kamar mutane ba sa godiya don alherin da muke musu. Hakan zai sa mu ci-gaba da yin alheri kuma mu ƙara yin farin ciki.
KA ZAMA MAI BAYARWA KAMAR JEHOBAH
5. Ta yaya Jehobah yake biyan bukatunmu?
5 Waɗanne abubuwa ne Jehobah yake ba mu? Ga wasu misalai. Jehobah yana biyan bukatunmu. Ko da yake ba dukan abubuwan jin daɗin rayuwa ne muke da su ba, Jehobah yana ba mu abin da muke bukata. Alal misali, yana sa mu sami abinci da kayan sakawa da kuma wurin kwana. (Zab. 4:8; Mat. 6:31-33; 1 Tim. 6:6-8) Dole ne Jehobah ya biya bukatunmu? Aꞌa. To me ya sa yake haka?
6. Mene ne muka koya daga Matiyu 6:25, 26?
6 Jehobah yana biyan bukatunmu ne don yana ƙaunar mu. Ka lura da abin da Yesu ya ce a Matiyu 6:25, 26. (Karanta.) Yesu ya yi kwatanci da tsuntsaye, ya ce: “Ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa tara a rumbuna. Duk da haka Ubanku na sama ne yake ciyar da su.” Sai Yesu ya yi tambaya, ya ce: “Ba ku fi su daraja ba?” Mene ne darasin? Bayin Jehobah suna da daraja a gare shi fiye da dabbobi. Tun da Jehobah yana biyan bukatun dabbobi, ba shakka zai biya mana namu! Kamar yadda mutum yakan biya bukatun ꞌyan iyalinsa don yana ƙaunar su, haka ma Jehobah yake mana.—Zab. 145:16; Mat. 6:32.
7. Ta yaya za mu zama masu bayarwa kamar Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)
7 Kamar Jehobah, mu ma za mu iya ba wa mutane abin da suke bukata don muna ƙaunar su. Alal misali, ka san wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da take bukatar abinci ko rigar sakawa? Jehobah zai iya taimaka wa irinsu ta wurin ka. An san Shaidun Jehobah da bayarwa musamman idan balaꞌi ya auku. Abin da ya faru ke nan a lokacin korona. ꞌYanꞌuwa sun taimaka wa masu bukata da abinci da riguna da dai sauransu. Da yawa kuma sun yi gudummawa don aikinmu a faɗin duniya. Kuma hakan ya sa an sami kuɗin ba da kayan agaji a wurare da dama a faɗin duniya. Ba shakka, ꞌyanꞌuwan nan sun bi abin da ke Ibraniyawa 13:16. Wurin ya ce: “Kada ku daina yin alheri da zumuntar tarayya ta abin da kuke da shi, gama irin waɗannan hadayu suke faranta wa Allah rai.”
Dukanmu za mu iya zama masu bayarwa kamar Jehobah (Ka duba sakin layi na 7)
8. Ta yaya Jehobah yake ba mu ƙarfi? (Filibiyawa 2:13)
8 Jehobah yana ba mu ƙarfi. Yana amfani da ikonsa marar iyaka don ya ba mu ƙarfin yin abin da ya dace. (Karanta Filibiyawa 2:13.) Ka taɓa roƙon Jehobah ya ba ka ƙarfin jimre wata matsala, ko kuma ƙarfin guje wa wata jaraba? Mai yiwuwa ma, ka taɓa roƙansa ya ba ka ƙarfin yin ayyukan da kake bukatar yi. Da Jehobah ya amsa adduꞌarka, ba mamaki kamar manzo Bulus, kai ma ka ji a ranka cewa: “Zan iya yin kome ta wurin . . . wanda yake ƙarfafa ni.”—Filib. 4:13.
9. Ta yaya za mu yi amfani da ƙarfinmu mu taimaka wa mutane kamar Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)
9 Ko da yake mu ajizai ne, za mu iya yin koyi da yadda Jehobah yake ƙarfafa bayinsa. Ba za mu iya ba wa mutane ƙarfinmu ba. Amma za mu iya yin amfani da ƙarfinmu mu taimaka musu. Alal misali, za mu iya taya ꞌyanꞌuwa tsoffi da marasa lafiya sayan abubuwa, da yin ayyukan gida. Za mu kuma iya yin shara da kuma kula da Majamiꞌar Mulki. Idan muna amfani da ƙarfinmu haka, za mu taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu sosai.
Za mu iya amfani da ƙarfinmu mu taimaka wa mutane (Ka duba sakin layi na 9)
10. Ta ya za mu ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu da abin da muke faɗa?
10 Ƙari ga haka, ka tuna cewa maganarka za ta iya ƙarfafa mutane. Ka san wani da za ka iya ƙarfafawa ta wajen yaba masa? Akwai wanda yake bukatar kalmomin da za su kwantar masa da hankali? Idan haka ne, ka yi ƙoƙari ka gaya musu abin da zai ƙarfafa su. Za ka iya zuwa gidansu, ko ka kira su a waya, ko ka yi rubutu a kati ka tura musu, ko ka aika musu saƙon email, ko saƙon tes. Kada ka yi ta damuwa a kan abin da za ka gaya wa mutumin. Ko da ꞌyan kalmomi ne ka faɗa daga zuciyarka, za su iya ƙarfafa ꞌyarꞌuwa ko ɗanꞌuwa ya ci-gaba da riƙe amincinsa, ko su sa ya ji sauƙi.—K. Mag. 12:25; Afis. 4:29.
11. Yaya Jehobah yake ba da hikimarsa?
11 Jehobah yana ba mu hikima. Yakub ya rubuta cewa: “In waninku yana bukatar hikima, sai ya roƙi Allah wanda yake ba kowa hannu sake ba tare da gori ba.” (Yak. 1:5) Kamar yadda ayar nan ta nuna, Jehobah ba ya yin rowa da hikimarsa. Yana bayarwa hannu sake. Kuma idan Jehobah ya ba wa mutum hikima, ba ya masa “gori.” Ba ya kunyatar da mu don mun nemi taimakonsa. A maimakon haka, shi da kansa ne ya ce mu roƙe shi.—K. Mag. 2:1-6.
12. Waɗanne dama ne muke da su na koya ma wasu abin da muka sani?
12 Mu kuma fa? Za mu iya yin koyi da Jehobah kuwa? Ƙwarai! (Zab. 32:8) A ƙungiyar Jehobah, ba ma rasa damar koya wa mutane abin da muka sani. Alal misali, za mu iya koya wa sabbi yadda za su yi waꞌazi. Dattawa za su iya taimaka wa bayi masu hidima da ꞌyanꞌuwa maza da suka yi baftisma su iya yin ayyuka da aka ba su da kyau. ꞌYanꞌuwa maza da mata da suka ƙware a aikin gine-gine da kula da wuraren ibadarmu, za su iya koyar da waɗanda ba su ƙware ba.
13. Ta yaya za mu bi misalin Jehobah saꞌad da muke koya wa mutane abin da muka sani?
13 Saꞌad da muke koya wa mutane abin da muka sani, zai dace mu bi misalin Jehobah. Mu tuna cewa, Jehobah yana ba da hikimarsa hannu sake. Mu ma idan mun iya wani abu, zai yi kyau mu so koya ma waɗanda ba su sani ba. Kada mu ɓoye wasu abubuwan da muka sani don muna tsoron cewa idan muka koya wa wani, a-kwana-a-tashi zai ɗauki matsayinmu. Ko kuma mu ce: ‘Ai, ba wanda ya koyar da ni! Don haka shi ma ya koya da kansa.’ Bai kamata bawan Jehobah ya yi irin wannan tunani ba. A maimakon haka, zai dace mu so koya wa mutane abin da muka sani, kuma mu yi duk abin da za mu iya don mu koyar da su. (1 Tas. 2:8) Muna fatan cewa, “su ma za su iya koya wa waɗansu.” (2 Tim. 2:1, 2) Idan dukanmu muna koya wa mutane abin da muka sani, mu da su za mu zama masu hikima, kuma mu ƙara yin farin ciki.
IDAN BA A GODE MANA YADDA MUKE SO BA
14. Mene ne yawancin mutane suke yi idan muka yi musu alheri?
14 Idan muka yi wa mutane alheri, yawancinsu sukan gode mana, musamman ꞌyanꞌuwanmu. Za su iya rubuta saƙon godiya su tura mana, ko kuma su gode mana ta wata hanya dabam. (Kol. 3:15) Idan aka gode mana don alherin da muka yi, mukan ji daɗi.
15. Me ya kamata mu tuna idan mutane ba su gode mana ba don alherin da muka yi musu?
15 Amma a wasu lokuta, mutane ba sa gode mana don alherin da muka yi musu. Bayan mun kashe kuɗi ko mun yi amfani da lokacinmu sosai don mu taimaka wa mutum, sai ya yi kamar bai damu da ƙoƙari da muka yi ba. Idan hakan ya faru, me zai taimaka mana mu ci-gaba da yin farin ciki? Mu tuna da abin da ke Ayyukan Manzanni 20:35. Bayarwa ce take sa mutum farin ciki ba godiya da aka yi masa ba. Wato ko da ba a gode mana ba, za mu iya yin farin ciki. Don haka, za mu iya ci-gaba da bayarwa da farin ciki ko da muna ganin kamar ba a nuna godiya. Me zai taimaka mana mu yi hakan? Ga wasu abubuwa.
16. Me zai taimaka mana mu ci-gaba da bayarwa da farin ciki?
16 Ka tuna cewa kana yin koyi da Jehobah. Yana yi wa mutane alheri ko da ba sa yin godiya. (Mat. 5:43-48) Jehobah ya yi alkawari cewa idan mu ma muna bayarwa ‘ba da nufi sai an biya mu ba,’ zai ba mu “lada mai yawa.” (Luk. 6:35) Saboda haka, in ba a gode mana ba, kar mu damu. Mu tuna cewa Jehobah zai ba mu lada don kowane abin alheri da muka yi wa mutane, da yake mu masu “bayarwa da daɗin rai” ne.—K. Mag. 19:17; 2 Kor. 9:7.
17. Ta yaya kuma za mu yi koyi da Jehobah saꞌad da muke yi wa mutane alheri? (Luka 14:12-14)
17 Wani abin da zai taimaka mana mu yi koyi da Jehobah shi ne, bin abin da Yesu ya faɗa a Luka 14:12-14. (Karanta.) Ba laifi ba ne mu yi wa mutanen da za su iya biyan mu alheri ba. Amma, bai kamata mu riƙa yi wa mutane alheri da zaton cewa za su biya mu ba. Idan mun lura cewa muna hakan, me ya kamata mu yi? Mu yi ƙoƙari mu bi abin da Yesu ya ce. Ta yaya? Ta wajen yin alheri ga wanda mun san ba zai iya biyan mu ba. Yin hakan zai sa mu farin ciki don muna koyi da Jehobah. Idan ba ma zaton cewa za a biya mu, za mu ci-gaba da yin farin ciki ko da mutane ba su gode mana ba.
18. Mene ne bai kamata mu yi ba, kuma me ya sa?
18 Kada mu ɗauka cewa mutane marasa godiya ne. (1 Kor. 13:7) Idan mutum bai gode mana ba, mu tambayi kanmu: ‘Mutumin nan marar godiya ne, ko dai ya manta ne?’ Wataƙila akwai wani abin da ya sa bai gode mana yadda muke zato ba. Wasu zuciyarsu tana cike da godiya amma ba su san yadda za su faɗe shi ba. Wasu kuma mai yiwuwa kunya suke ji, musamman idan a dā su ne suke taimaka wa mutane. Ko da mene ne dalilinsu, idan muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu, ba za mu yi saurin ɗauka cewa su marasa godiya ne ba, kuma za mu ci-gaba da bayarwa da farin ciki.—Afis. 4:2.
19-20. Me ya sa muke bukatar mu ƙara yin haƙuri? (Ka kuma duba hoton.)
19 Ka ƙara yin haƙuri. Sarki Sulemanu ya ce: “Ka bayar hannu sake, gama za ka same shi bayan kwanaki da yawa.” (M. Wa. 11:1) Abin da ya faɗa ya nuna cewa, a wasu lokuta mutane za su iya gode mana “bayan kwanaki da yawa.” Ga wani labari da ya nuna hakan.
20 Shekaru da yawa da suka wuce, wata matar mai kula da daꞌira ta yi rubutu a kati ta aika ma wata ꞌyarꞌuwa da ba ta daɗe da yin baftisma ba. Ta ƙarfafa ꞌyarꞌuwar ta ci-gaba da riƙe aminci. Wajen shekaru takwas bayan haka, sai ꞌyarꞌuwar ta aika mata saƙo. Ta ce: “Zan so in gode miki don abin da kika yi mini shekarun da suka shige. Na san ba ki san yadda hakan ya taimaka min ba. “[Kalmominki] sun ƙarfafa ni, amma nassin da kika ambata ne ya fi ratsa zuciyata, kuma ban manta da shi ba.”a Sai ta bayana wasu matsalolin da ta yi fama da su, kuma ta ce: “Akwai lokutan da na ji kamar gwamma in daina bauta wa Jehobah kawai. Amma idan na tuna da nassin nan, sai in ji ya ƙarfafa ni in ci-gaba da riƙe amincina.” Ta ƙara da cewa: “A cikin shekaru takwas ɗin nan, babu abin da ya ƙarfafa ni kamar saƙonki da nassin da kika ambata.” Ka yi tunanin irin farin ciki da matar mai kula da daꞌiran ta yi da ta sami wannan saƙon godiya “bayan kwanaki da yawa”! Mu ma wataƙila a-kwana-a-tashi wanda muka yi masa alheri zai zo ya yi mana godiya.
Wataƙila a-kwana-a-tashi wanda muka yi masa alheri zai zo ya yi mana godiya (Ka duba sakin layi na 20)b
21. Me ya sa kake so ka ci-gaba da bayarwa kamar Jehobah?
21 Kamar yadda muka tattauna, Jehobah ya halicce mu yadda za mu fi yin farin ciki idan muna bayarwa. Muna jin daɗi sosai idan muka taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu a ikilisiya. Ƙari ga haka, muna farin ciki idan suka gode mana don alherin da muka yi musu. Amma ko da wanda muka yi wa alheri bai gode mana ba, za mu yi farin ciki idan muka tuna cewa mun yi abin da ya dace. Kada ka manta cewa ko da me ka ba wa mutum, “Yahweh yana da iko ya ba ka abin da ya fi wannan yawa.” (2 Tar. 25:9) Don haka, Jehobah zai ba mu ladan da ta fi abin da muke bayarwa. Kuma me ya fi a ce Jehobah ya saka mana da alheri? Bari dukanmu mu ci-gaba da bayarwa kamar Ubanmu na sama.
WAƘA TA 17 “Na Yarda”
a Nassin shi ne 2 Yohanna 8. Wurin ya ce: “Saboda haka ku lura, domin kada dukan abin da kuka yi ya zama banza, a maimako ku sami cikakken ladanku.”
b BAYANI A KAN HOTUNA: Hoton ya kwatanta abin da ya faru lokacin da matar mai kula da daꞌiran ta aika ma ꞌyarꞌuwar saƙo mai ban ƙarfafa. Bayan shekaru da dama, sai ꞌyarꞌuwar ta amsa mata da saƙon godiya.