Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Disamba pp. 8-13
  • Littafin Ayuba Zai Taimaka Mana Saꞌad da Muke Ba da Shawara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafin Ayuba Zai Taimaka Mana Saꞌad da Muke Ba da Shawara
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA ABOKAN AYUBA UKU SUKA YI MASA MAGANA
  • YADDA ELIHU YA YI WA AYUBA MAGANA
  • YADDA ZA KA CI-GABA DA AMFANA DAGA LITTAFIN AYUBA
  • Jehobah Ya Warkar da Shi
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Darussa Daga Littafin Ayuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Littafin Ayuba Zai Iya Taimaka Mana a Lokacin da Muke Shan Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • “Kun Ji Labarin Jimrewar Ayuba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Disamba pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 49

WAƘA TA 44 Adduꞌar Wanda Ke Cikin Wahala

Littafin Ayuba Zai Taimaka Mana Saꞌad da Muke Ba da Shawara

“Yanzu, ya Ayuba, ina roƙonka, ka ji dukan kalmomina.”—AYU. 33:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda littafin Ayuba zai taimaka mana mu ba da shawara a hanyar da ta dace.

1-2. Me ya sa taimaka wa Ayuba ba zai yi wa abokansa uku da Elihu sauƙi ba?

SAꞌAD DA Ayuba ya rasa dukan dukiyarsa, labarin abin da ya faru da shi ya bazu a yankinsu. Da abokansa uku suka ji abin da ya faru, sun kama hanya zuwa Uz don su ƙarfafa shi. Sunayensu su ne, Elifaz, Bildad, da Zofar. Amma abin da suka gani ya ba su mamaki.

2 Ka yi laꞌakari da yanayin da suka sami Ayuba a ciki. Ayuba ya rasa komen da yake da shi. Ya rasa garkunan tumakinsa, da na shanayensa, da na rakumansa, da kuma na jakunansa. An kashe kusan dukan bayinsa, kuma dukan yaransa sun mutu saꞌad da gidan da suke ciki ya rushe. Ban da haka, Ayuba da kansa ma bai tsira ba. Ƙuraje masu zafin tsiya sun cika jikinsa. Da maza ukun suka hango Ayuba, sun gan shi zaune cikin toka yana baƙin ciki. Mene ne suka yi? Sun yi kwanaki bakwai ba su ce kome ba, duk da cewa sun ga yanayi mai wuya da yake ciki. (Ayu. 2:​12, 13) Ana nan sai wani mutum da bai kai su shekaru ba mai suna Elihu ya zo kuma ya zauna kusa da inda suke. A ƙarshe, sai Ayuba ya soma magana. Ya ce ya laꞌanci ranar da aka haife shi kuma ya ce gwamma ya mutu. (Ayu. 3:​1-3, 11) Babu shakka, Ayuba yana bukatar taimako! Amma taimaka masa ba zai zama da sauƙi ba don yanayin da yake ciki. Abin da mutanen nan za su faɗa da kuma yadda za su yi hakan, zai nuna ko su abokan ƙwarai ne kuma sun damu da yanayin da Ayuba yake ciki.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Jehobah ya sa Musa ya rubuta abubuwan da abokan Ayuba da Elihu suka faɗa da abubuwan da suka yi. Akwai alama cewa wasu abubuwan da Elifaz ya faɗa, raꞌayin wani aljani ne. Amma abubuwan da Elihu ya faɗa, raꞌayin Jehobah ne. (Ayu. 4:​12-16; 33:​24, 25) Shi ya sa a littafin Ayuba, za mu iya ganin shawarwari masu kyau da kuma waɗanda ba su da kyau. A wannan talifin, za mu ga yadda littafin Ayuba zai taimaka mana saꞌad da muke so mu ba wa wani shawara. Da farko, za mu ga irin shawarwarin da bai kamata mu bayar ba daga misalin abokan Ayuba uku. Saꞌan nan, za mu ga yadda za mu ba da shawara mai kyau daga misalin Elihu. A kowane yanayi, za mu ga yadda mai yiwuwa Israꞌilawa suka amfana daga labarin, da kuma yadda mu ma a yau za mu amfana.

YADDA ABOKAN AYUBA UKU SUKA YI MASA MAGANA

4. Me ya sa abokan Ayuba suka gagara taimaka masa? (Ka kuma duba hoton.)

4 Littafi Mai Tsarki ya ce, da abokan Ayuba suka ji abin da ya faru da shi, sun “kai masa ziyara domin su taꞌazantar da shi.” (Ayu. 2:11) Amma sun gagara cim ma hakan. Me ya sa? Ga dalilai uku. Da farko, ba su saurari Ayuba da kyau ba, kuma ba su yi ƙoƙarin fahimtar yanayin da yake ciki ba. Alal misali, sun ɗauka cewa zunubansa ne suka sa yake shan wahala.a (Ayu. 4:7; 11:14) Na biyu shi ne, yawancin abubuwan da suka gaya wa Ayuba, bai taimaka masa ba ko kaɗan. Ko da yake abin da suka faɗa ya yi kamar abin da ya dace ne. (Ayu. 13:12) Kuma sun faɗi abubuwa da dama da ya sa Ayuba ya ji zafi sosai a zuciyarsa. Alal misali, sau biyu Bildad ya gaya wa Ayuba cewa, shi mai surutu ne. (Ayu. 8:2; 18:2) Kuma a wasu lokuta ma sun zage shi. Alal misali, Zofar ya ce Ayuba “marar tunani” ne. (Ayu. 11:12) Na uku kuma shi ne, ko da yake mai yiwuwa ba su yi wa Ayuba tsawa ba, abubuwan da suka faɗa da yadda suka yi maganar, sun nuna cewa ba sa daraja Ayuba kuma ba su damu da yanayin da yake ciki ba. (Ayu. 15:​7-11) A taƙaice, abin da ya fi damun abokan Ayuba nan uku shi ne, nuna masa laifinsa maimakon su ƙarfafa shi.

Ɗaya daga cikin abokan Ayuba uku yana masa baƙar magana, yayin da biyun suna zaune suna kallon su. Ayuba yana zaune a ƙasa, jikinsa cike da ƙuraje yana sauraron abin da ake gaya masa.

Saꞌad da kake ba wa wani shawara, kada ka nuna kamar ka fi shi. Ka yi iya ƙoƙarinka ka taimaka masa (Ka duba sakin layi na 4)


5. Mene ne sakamakon abubuwan da abokan Ayuba suka gaya masa?

5 Abubuwan da abokan Ayuba suka gaya masa ba su taimaka masa ba. A maimakon haka, yanayinsa ya daɗa muni. (Ayu. 19:2) Sun yi ta ƙoƙarin gaya masa cewa zunubansa ne suka sa yake shan wahala. Shi kuma yana ta kāre kansa don ya nuna cewa shi mutumin kirki ne. Hakan ya sa ya faɗi wasu abubuwan da ba su kamata ba. (Ayu. 6:​3, 26) Abokan Ayuba ba su gaya masa abubuwan da suka jitu da raꞌayin Jehobah ba, kuma ba su tausaya masa ba. Hakan ya sa Shaiɗan ya yi amfani da su wajen sa Ayuba ya yi sanyin gwiwa. (Ayu. 2:​4, 6) Ta yaya mai yiwuwa labarin nan ya taimaka wa mutane a dā, kuma ta yaya zai taimaka mana a yau?

6. Waɗanne darussa ne mai yiwuwa dattawan Israꞌila suka koya daga labarin Ayuba?

6 Yadda mai yiwuwa Israꞌilawa suka amfana. Bayan da Jehobah ya ba wa Israꞌilawa dokokinsa, ya zaɓi dattawa su yi musu ja-goranci kuma su taimaka musu su bi dokokin. (M. Sha. 1:​15-18; 27:1) Dattawan suna bukata su saurara da kyau, kafin su ba da shawara ko kuma su yanke hukunci. (2 Tar. 19:6) Suna bukatar su yi tambayoyi don su gane ainihin batun, maimakon su ɗauka cewa sun san kome da kome. (M. Sha. 19:18) Kuma idan wani ya zo neman taimako a wurinsu, suna bukata su riƙa magana da alheri. Me ya sa? Domin rashin yin hakan zai iya sa mutumin ya ƙi gaya musu ainihin abin da ke zuciyarsa. (Fit. 22:​22-24) Waɗannan su ne mai yiwuwa darussan da dattawan Israꞌila suka koya daga labarin Ayuba.

7. Ban da dattawan Israꞌila, su waye ne za su iya ba da shawara, kuma ta yaya mai yiwuwa suka amfana daga labarin Ayuba? (Karin Magana 27:9)

7 Ba dattawan Israꞌila ne kawai za su iya ba wa wani shawara ba. Kowa ma zai iya ba da shawara game da yadda mutum zai kusaci Jehobah. Ko yaro ko babba ko namiji ko tamace. Kowa zai iya yi wa wani gyara idan ya yi abin da bai dace ba. (Zab. 141:5) Abin da aboki na ƙwarai yake yi ke nan. (Karanta Karin Magana 27:9.) Labarin abokan Ayuba ukun nan, mai yiwuwa ya taimaka wa Israꞌilawa su san abubuwan da bai kamata su yi, ko su faɗa ba saꞌad suke ba wa wani shawara.

8. Waɗanne abubuwa uku ne ya kamata mu tuna saꞌad da muke ba wa mutane shawara? (Ka kuma duba hotunan.)

8 Yadda mu ma za mu amfana. A matsayinmu na Kiristoci, muna so mu taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu saꞌad da suke fama da matsaloli. Amma don mu cim ma hakan, wajibi ne mu guji abubuwan da abokan Ayuba uku suka yi. Da farko, zai dace mu tabbata cewa mun gane batun ciki da waje kafin mu ba da shawara. Na biyu, kada mu riƙa gaya wa mutane raꞌayinmu kamar yadda Elifaz ya yi. Maimakon haka, mu ba da shawara bisa ga abin da ke Littafi Mai Tsarki. (Ayu. 4:8; 5:​3, 27) Na uku, mu guji yi wa mutane maganar da za ta ɓata musu rai ko kuma mu kushe su. Ka tuna cewa wasu abubuwan da Elifaz da abokansa suka faɗa gaskiya ne. Wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya ma yi ƙaulin ɗaya daga cikin abin da suka faɗa. (Ka duba Ayuba 5:13 da 1 Korintiyawa 3:19.) Duk da haka, yawancin abubuwan da suka faɗa game da Allah ba gaskiya ba ne, kuma hakan ya ɓata wa Ayuba rai. Shi ya sa Jehobah ya ce ƙarya ne suka faɗa game da shi. (Ayu. 42:​7, 8) Idan muna ba wa mutane shawara, muna bukatar mu mai da hankali don kada mu faɗa abubuwan da za su sa su ga kamar Jehobah ba ya ƙaunar bayinsa, ko kuma shi mugu ne. Bari mu ga abin da za mu iya koya daga misalin Elihu.

Hotuna: Wani ɗanꞌuwa yana ba wa wani ɗanꞌuwa da ya yi fushi shawara. Na 1. Wani ɗanꞌuwa yana sauraron wani ɗanꞌuwan da ya yi fushi. Kuma su biyun suna zaune a waje suna shan iska kuma suna shan ruwan lemo. Na 2. Ɗanꞌuwan da ke sauraron ɗayan ya buɗe Littafi Mai Tsarki. Na 3. Ya karanta wa ɗayan wata aya, shi kuma ya natsu yana sauraronsa.

Saꞌad da kake ba da shawara, (1) ka fahimci yanayin mutumin da kyau, (2) ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki, kuma (3) ka yi magana da alheri (Ka duba sakin layi na 8)


YADDA ELIHU YA YI WA AYUBA MAGANA

9. Ka bayyana dalilin da sa Ayuba yake bukatar taꞌaziyya bayan da abokansa uku suka daina magana da kuma yadda Jehobah ya taimaka masa.

9 Ayuba da abokansa ukun sun yi ta gardama na dogon lokaci. Sun yi magana sosai har kalmominsu sun cika surori 28 a Littafi Mai Tsarki. Kuma yawancin abubuwan da suka yi ta faɗa sun nuna cewa suna magana ne cikin fushi da kuma ɓacin rai. Hakan ya sa Ayuba ya ci-gaba da zama a cikin ƙunci da baƙin ciki! Yana bukatar wanda zai taꞌazantar da shi kuma ya taimaka masa ya canja raꞌayinsa. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Ayuba? Ya yi amfani da Elihu don ya ba shi shawara. Me ya sa Elihu ya jira har sai da suka gama gardama kafin ya yi magana? Shi da kansa ya ce: “A shekaru dai ni yaro ne, ku tsofaffi ne a gare ni. Wannan ya sa na ji nauyi” yin magana. (Ayu. 32:​6, 7) Elihu ya san cewa tsofaffi suna da hikima don sun daɗe a duniya, kuma sun ga abubuwa da dama fiye da waɗanda ba su kai su shekaru ba. Amma bayan da ya saurari Ayuba da abokansa ukun nan, Elihu ya ga cewa bai kamata ya ci-gaba da yin shuru ba. Sai ya ce: “Ba wai zaman tsoho ne yakan kawo hikima ba, ba kuma yawan shekaru ne yakan kawo ganewar yin shariꞌar gaskiya ba.” (Ayu. 32:9) Bayan haka, mene ne Elihu ya ƙara faɗa, kuma ta yaya ya yi hakan?

10. Mene ne Elihu ya yi kafin ya ba wa Ayuba shawara? (Ayuba 33:​6, 7)

10 Kafin Elihu ya yi wa Ayuba magana, ya jira har sai da Ayuba ya daina fushi kuma yana shirye ya saurare shi. Ta yaya ya yi hakan? Elihu ya natsu. Abin da ya sa yake bukata ya natsu shi ne, Littafi Mai Tsarki ya ce shi ma ya yi fushi da farko. (Ayu. 32:​2-5) Natsuwa ya taimaka masa ya yi wa Ayuba magana da alheri kamar aboki na ƙwarai. Alal misali, ya gaya wa Ayuba cewa: “Ga shi, ni da kai ɗaya ne a gaban Allah.” (Karanta Ayuba 33:​6, 7.) Ƙari ga haka, abin da ya faɗa ya nuna cewa Elihu ya saurari Ayuba da kyau. Kafin ya ba wa Ayuba shawara, ya taƙaita wasu abubuwa shida da Ayuba ya faɗa. (Ayu. 32:11; 33:​8-11) Kuma ya yi abu makamancin hakan a wasu lokutan da ya ba wa Ayuba shawara.—Ayu. 34:​5, 6, 9; 35:​1-4.

11. Ta yaya Elihu ya ba wa Ayuba shawara? (Ayuba 33:32)

11 Saꞌad da Elihu yake ba wa Ayuba shawara, ya yi hakan a hanyar da ta nuna cewa ya daraja shi. Alal misali, mai yiwuwa Elihu ya tuna yadda ya ji lokacin da Ayuba da abokansa suke gardama. Ya yi ta so ya yi magana amma bai sami damar yin hakan ba. Don haka, ya ba wa Ayuba dama ya yi magana saꞌad da yake ba shi shawara. (Ayu. 32:4; Karanta Ayuba 33:32.) Elihu ya nuna wa Ayuba wasu abubuwan da ya yi da kuma faɗa da ba daidai ba. Kuma Elihu ya tuna masa da hikimar Jehobah, da ikonsa, da adalcinsa, da kuma ƙaunarsa marar canjawa. (Ayu. 36:​18, 21-26; 37:​23, 24) Shawarwarin da Elihu ya ba wa Ayuba sun sa Ayuba ya kasance a shirye ya karɓi shawarwarin da Jehobah zai ba shi. (Ayu. 38:​1-3) Ta yaya abin da Elihu ya yi mai yiwuwa ya amfani mutane a dā, kuma ta yaya zai amfane mu a yau?

12. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da annabawa wajen taimaka wa mutanensa, kuma ta yaya Israꞌilawa suka amfana daga misalin Elihu?

12 Yadda Israꞌilawa suka amfana. Jehobah yana yawan amfani da annabawansa wajen koyar da Israꞌilawa da kuma ja musu kunne. Alal misali, a lokacin alƙalai, Jehobah ya yi amfani da annabiya Deborah wajen ba wa Israꞌilawa umurni. Ban da haka ma, Jehobah ya yi amfani da Samaꞌila tun yana ƙarami wajen ba wa mutanensa umurnai. (Alƙa. 4:​4-7; 5:7; 1 Sam. 3:​19, 20) Ƙari ga haka, a lokacin sarakunan Israꞌilawa, Jehobah ya yi ta amfani da annabawansa don su taimaka wa Israꞌilawa su ci-gaba da bauta masa da aminci. Kuma idan suka yi masa rashin biyayya, yakan tura annabawan su ja musu kunne. (2 Sam. 12:​1-4; A. M. 3:24) Misalin Elihu mai yiwuwa ya taimaka wa maza da mata masu aminci su san abin da za su faɗa da kuma yadda za su yi hakan, saꞌad da suke ba wa wani shawara.

13. Ta yaya Kiristoci a yau za su iya ƙarfafa juna?

13 Yadda mu ma za mu amfana. A matsayinmu na Kiristoci, muna taimaka wa mutane su san abin da Allah yake so ta wajen gaya musu abin da ke Littafi Mai Tsarki. Muna kuma amfani da kalmomin da suka dace, wajen ƙarfafa da kuma taꞌazantar da ꞌyanꞌuwanmu. (1 Kor. 14:3) Wajibi ne dattawa su riƙa yin magana da alheri ko da wanda suke ƙoƙarin yi wa magana ya yi fushi ko ya faɗi abin da bai dace ba.—1 Tas. 5:14; Ayu. 6:3.

14-15. Ka ba da misalin yadda dattawa za su iya koyi da Elihu.

14 Alal misali, a ce wani dattijo ya ji cewa wata ꞌyarꞌuwa tana fama da baƙin ciki. Sai shi da wani dattijo suka je su ƙarfafa ta. Da suka isa wurin, sai ꞌyarꞌuwar ta gaya musu cewa ko da yake tana zuwa waꞌazi da taro, ba ta farin ciki. Mene ne dattawan za su yi?

15 Da farko, ba mamaki za su yi ƙoƙari su san ainihin dalilin da ya sa take baƙin ciki. Don su fahimce ta da kyau, suna bukatar su yi mata wasu tambayoyi kuma su saurare ta saꞌad da take magana. Wataƙila abin da take gani shi ne, Jehobah ba ya ƙaunar ta, ko kuma mai yiwuwa tana damuwa a kan yadda za ta biya bukatunta na yau da kullum. (Luk. 21:34) Ban da haka, dattawan za su yaba mata don abubuwa masu kyau da take yi. Kamar yadda take zuwa taro da kuma waꞌazi duk da cewa tana fama da baƙin ciki. Ƙari ga haka, da zarar sun fahimci yanayinta da kyau, kuma sun gane abin da ke sa ta baƙin ciki, za su yi amfani da Littafi Mai Tsarki don su ƙarfafa ta.—Gal. 2:20.

YADDA ZA KA CI-GABA DA AMFANA DAGA LITTAFIN AYUBA

16. Ta yaya za mu ci-gaba da amfana daga littafin Ayuba?

16 Akwai darussa da dama da za mu iya koya daga littafin Ayuba. A talifin da ya shige, mun ga dalilin da ya sa Allah ya ƙyale mutane su sha wahala. Mun kuma ga yadda littafin Ayuba zai taimaka mana mu kasance da aminci saꞌad da muke shan wahala. Kuma kamar yadda muka gani a wannan talifin, dukanmu za mu iya ba da shawara mai kyau ta wajen bin misalin Elihu maimakon abokan Ayuba uku. Kafin ka ba wa wani shawara zai dace ka bincika darussan da ke littafin Ayuba. Idan kuma ka daɗe da karanta littafin Ayuba, zai yi kyau ka sake karantawa. Ba mamaki za ka sake samun ƙarin darussa daga wannan littafin.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne zai dace mu guje wa saꞌad da muke ba da shawara?

  • Mene ne za mu iya koya daga yadda Elihu ya ba wa Ayuba shawara?

  • Ta yaya za mu ci-gaba da amfana daga littafin Ayuba?

WAƘA TA 125 Masu Jinƙai Suna Farin Ciki!

a Wataƙila wani aljani ne ya sa Elifaz ya ce, Jehobah yana ganin babu mai adalci kuma ba wani ɗanadam da zai iya yin abin da Jehobah yake so. Elifaz ya kasance da wannan raꞌayi marar kyau. Kuma ya maimaita hakan sau uku saꞌad da yake yi wa Ayuba magana.—Ayu. 4:17; 15:​15, 16; 22:2.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba