Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Maris pp. 8-13
  • Ka Yi Koyi da Yadda Jehobah da Yesu Suke Tunani

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Koyi da Yadda Jehobah da Yesu Suke Tunani
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MU YI KOYI DA YADDA JEHOBAH YAKE TUNANI
  • MU ZAMA MASU TAWALIꞌU
  • KA “RIƘA YIN TUNANIN DA YA DACE”
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Mu Zama Masu Sauƙin Kai Kamar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ya Kasance da Aminci a Lokacin Gwaji
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Maris pp. 8-13

TALIFIN NAZARI NA 10

WAƘA TA 31 Ka Bi Allah!

Ka Yi Koyi da Yadda Jehobah da Yesu Suke Tunani

“Tun da yake Almasihu ya sha wahala a jiki, ku ma ku ɗauki irin wannan tunani domin ku jimre shan wahala.”—1 BIT. 4:1.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga darussa masu kyau da Bitrus ya koya daga yadda Yesu yake tunani da kuma abin da za mu iya koya daga darussan.

1-2. Yaya ne ya kamata mu ƙaunaci Jehobah, kuma ta yaya Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah da dukan tunaninsa?

YESU ya bayyana dokar Allah da ta fi muhimmanci saꞌad da ya ce: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka.” (Luk. 10:27) Wannan ya nuna cewa muna bukatar mu ƙaunaci Jehobah da dukan abin da muke da shi. Hakan ya ƙunshi abin da muke so, da yadda muke ji, da kuma ƙarfinmu. Ya kuma ƙunshi abin da muke tunani a kai. Gaskiyar ita ce, ba za mu iya gama gane yadda Jehobah yake tunani ba. Amma yin nazari game da yadda Yesu yake tunani zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake tunani, domin Yesu yana tunani kamar yadda Jehobah yake yi.—1 Kor. 2:16.

2 Yesu ya ƙaunaci Jehobah da dukan tunaninsa. Ya san abin da Allah yake so ya yi, kuma ya yi niyyar yin hakan, ko da zai sha wuya. Da yake Yesu ya fi son yin abin da zai sa Jehobah farin ciki, bai bar wani abu ya kasance da muhimmanci a rayuwarsa fiye da hakan ba.

3. Mene ne manzo Bitrus ya koya daga wurin Yesu, kuma me ya ƙarfafa Kiristoci su yi? (1 Bitrus 4:1)

3 Bitrus da sauran manzannin, sun sami wata dama ta musamman wato, kasancewa na dogon lokaci da Yesu. Kuma hakan ya ba su damar sanin yadda yake tunani. Shi ya sa da Bitrus yake rubuta wasiƙarsa ta farko, ya ƙarfafa Kiristoci su riƙa yin tunani irin na Kristi. (Karanta 1 Bitrus 4:1.) Ainihin furucin da Bitrus ya yi amfani da shi a ayar nan da aka fassara zuwa “ku ɗauki,” ya nuna yadda sojoji sukan ɗaura makamai a jikinsu saꞌad da suke shiri don yaƙi. Saboda haka, idan Kirista ya koyi yadda Yesu yake tunani, hakan zai taimaka masa ya zama a shirye wajen yaƙan shaꞌawar yin abin da bai dace ba da kuma halin duniyar nan da Shaiɗan yake mulki.—2 Kor. 10:​3-5; Afis. 6:12.

4. Me za mu tattauna a wannan talifin?

4 Yaya Yesu yake tunani kuma ta yaya za mu yi koyi da shi? A talifin nan za mu ga: (1) yadda za mu bi irin tunanin Jehobah, don tunaninmu ya jitu da na ꞌyanꞌuwa, (2) yadda za mu zama masu tawaliꞌu, da kuma (3) yadda za mu dogara ga Jehobah don ya taimaka mana mu riƙa tunanin da ya dace.

MU YI KOYI DA YADDA JEHOBAH YAKE TUNANI

5. Mene ne Bitrus ya yi da ya nuna cewa tunaninsa bai jitu da na Jehobah ba?

5 Akwai lokacin da Bitrus ya yi wani abin da ya nuna cewa tunaninsa bai jitu da na Jehobah ba. Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa zai je Urushalima kuma za a bashe shi ga malaman addinai, zai sha wuya a hannunsu kuma za a kashe shi. (Mat. 16:21) Bitrus ya san cewa Yesu ne Almasihu da ya zo ya ceci bayin Allah. Don haka, ya yi masa wuya ya amince cewa Jehobah zai bar Yesu ya sha wuya har a kashe shi. (Mat. 16:16) Sai Bitrus ya ja Yesu gefe ya ce masa: “Allah ya sawwaƙe, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba.” (Mat. 16:22) Yesu bai yarda da abin da Bitrus ya faɗa ba, domin tunaninsa bai jitu da na Jehobah ba.

6. Ta yaya Yesu ya nuna cewa tunaninsa ya jitu da na Jehobah?

6 Yesu ya san yadda Jehobah yake tunani kuma yana koyi da hakan. Yesu ya gaya wa Bitrus cewa: “Ka rabu da ni, kai Shaiɗan! Kai mai sa tuntuɓe ne a gare ni, gama kana tunani kamar mutum ne, ba kamar Allah ba.” (Mat. 16:23) Ko da yake Bitrus yana yi wa Yesu fatan alheri ne, Yesu ya ƙi bin shawararsa, domin ya san cewa idan zai yi nufin Jehobah, dole ya sha wuya kuma ya mutu. Hakan ya koya wa Bitrus cewa ya kamata ya riƙa tunanin da ya jitu da nufin Jehobah. Wannan darasi ne mai muhimmanci da ya kamata mu koya, ko ba haka ba?

7. Ta yaya Bitrus ya nuna cewa yana son tunaninsa ya riƙa jituwa da na Jehobah? (Ka duba hoton.)

7 Daga baya, Bitrus ya nuna cewa yana son tunaninsa ya riƙa jituwa da na Jehobah. Hakan ya faru ne lokacin da aka umurce shi ya je ya yi wa alꞌumman da ba Israꞌilawa ba waꞌazi. Allah ya gaya wa Bitrus ya je ya yi wa Koneliyus waꞌazi, kuma Koneliyus yana cikin waɗanda suka soma zama Kiristoci daga sauran alꞌumma. A lokacin, Yahudawa ba sa maꞌamala da waɗanda ba Yahudawa ba, don haka Bitrus yana bukatar ya canja tunaninsa don ya iya yin wannan aikin da Allah ya ba shi. Da Bitrus ya gane yadda Allah yake ɗaukan mutane daga sauran alꞌumma, sai ya canja raꞌayinsa game da su. Hakan ya sa da Koneliyus ya ce masa ya zo gidansa, bai ƙi zuwa ba. (A. M. 10:​28, 29) Ya yi wa Koneliyus da iyalinsa waꞌazi, kuma dukansu sun yi baftisma.—A. M. 10:​21-23, 34, 35, 44-48.

Koneliyus yana nuna wa Bitrus da waɗanda suke tare inda za su bi su haura zuwa wani daki a gidansa.

Bitrus yana shigan gidan Koneliyus (Ka duba sakin layi na 7)


8. Ta yaya za mu nuna cewa tunaninmu ya jitu da na Jehobah? (1 Bitrus 3:8)

8 Shekaru da yawa bayan wannan lokacin, Bitrus ya ƙarfafa Kiristoci cewa: “Bari dukanku ku haɗa hankalinku ya zama ɗaya,” wato, tunaninsu ya jitu da na juna. (Karanta 1 Bitrus 3:8.) A matsayinmu na bayin Jehobah, tunaninmu zai jitu da na juna idan ya jitu da na Jehobah kamar yadda yake a Kalmarsa. Alal misali, Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa su sa alꞌamuran Mulkin farko a rayuwarsu. (Mat. 6:33) Hakan zai iya sa wani mai shela ya yanke shawarar soma hidima ta cikakken lokaci. Maimakon mu gaya masa cewa ya tausaya wa kansa ko kuma cewa ba zai zama masa da sauƙi ba, zai dace mu ƙarfafa shi kuma mu kasance a shirye don mu taimaka masa.

MU ZAMA MASU TAWALIꞌU

9-10. Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi mai tawaliꞌu ne sosai?

9 A dare na ƙarshe da Yesu ya yi da almajiransa kafin a kashe shi, ya koya musu wani darasi mai muhimmanci. Ya nuna wa Bitrus da sauran almajiran yadda za su zama masu tawaliꞌu. Kafin wannan lokacin, Yesu ya gaya wa Bitrus da Yohanna su je su shirya wurin da za su ci abinci na ƙarshe tare da shi kafin ya mutu. Mai yiwuwa, wasu abubuwan da suka tabbata cewa akwai a wurin su ne, daro da kuma tawul da za a iya wanke ƙafafu da su kafin a ci abincin. Amma waye ne a cikinsu zai ƙasƙantar da kansa kuma ya wanke ƙafafun sauran?

10 Yesu bai yi jinkirin yin wannan aikin ba. Ya nuna cewa shi mai tawaliꞌu ne sosai. Babu shakka, almajiransa sun yi mamaki da suka ga Yesu yana wannan aiki da bawa ne ya saba yi. Yesu ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗauko tawul ya ɗaura kewaye da jikinsa, ya zuba ruwa a daro, sai ya soma wanke ƙafafunsu. (Yoh. 13:​4, 5) Yesu ya wanke ƙafafun dukan manzaninsa 12 har da na Yahuda Iskariyoti wanda ya bashe shi. Babu shakka yin hakan ya ɗau lokaci. Duk da haka, Yesu ya kammala aikin. Sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Kun gane abin da na yi muku? Kuna ce da ni Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, domin haka nake. Tun da yake ni da nake Ubangijinku da Malaminku na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma ya kamata ku wanke wa juna.”—Yoh. 13:​12-14.

Zama masu tawaliꞌu . . . ta ƙunshi ainihin yadda muke ɗaukan kanmu da sauran mutane

11. Ta yaya Bitrus ya nuna cewa ya zama mai tawaliꞌu? (1 Bitrus 5:5) (Ka kuma duba hoton.)

11 Bitrus ya koyi tawaliꞌu daga wurin Yesu. Bayan da Yesu ya koma sama, Bitrus ya warkar da wani mutum da shi gurgu ne tun da aka haife shi. (A. M. 1:​8, 9; 3:​2, 6-8) Saꞌad da yake yin wannan abin mamakin, mutane da yawa sun taru da suka ga abin da ke faruwa. (A. M. 3:11) Shin, Bitrus ya karɓi yabo daga wurin mutanen ne? Aꞌa. Duk da cewa ya yi girma a inda mutane suke son ɗaukaka, bai yi hakan ba. A maimakon haka, ya kasance da tawaliꞌu kuma ya gaya musu cewa su yabi Jehobah da Yesu. Ya ce musu: “Ta ikon sunan Yesu ne, wato ta wurin ba da gaskiya gare shi, shi ne ya ba mutumin nan ƙarfi.” (A. M. 3:​12-16) Daga baya, Bitrus ya rubuta wa Kiristoci wasiƙa a kan muhimmancin zama masu tawaliꞌu. Ainihin kalmomin da Bitrus ya yi amfani da su na nufin mutum ya saka tawaliꞌu kamar yadda ake saka riga. Hakan ya tuna mana da lokacin da Yesu ya ɗaura tawul a jikinsa kuma ya wanke ƙafafun manzanninsa.—Karanta 1 Bitrus 5:5.

Bitrus da Yohanna suna tsaye a haikali. Bitrus ya miƙa hannu sama, saꞌad da wani mutum da shi gurgu ne tun da aka haife shi ya warke. Mutumin yana tsaye kusa da su.

Bayan da Bitrus ya yi wani abin mamaki, ya ce Jehobah da Yesu ne suka cancanci yabo. Mu ma za mu nuna cewa mu masu tawaliꞌu ne ta wajen yi wa mutane alheri ba tare da neman yabo ko wani abu ba (Ka duba sakin layi na 11-12)


12. Ta yaya za mu ci-gaba da zama masu tawaliꞌu kamar Bitrus?

12 Mu ma za mu iya yin koyi da Bitrus kuma mu ci-gaba da zama masu tawaliꞌu. Zai dace mu tuna cewa zama masu tawaliꞌu ya wuci abin da muke faɗa da baki kawai. Kalmar da Bitrus ya yi amfani da ita da aka fassara zuwa tawaliꞌu ta ƙunshi ainihin yadda muke ɗaukan kanmu da sauran mutane. Muna yi wa mutane alheri domin muna ƙaunarsu da kuma Jehobah, ba don muna son mu burge mutane ba ne. Idan muna yin kome tsakaninmu da Allah, ko da mutane suna ganin ƙoƙarinmu ko aꞌa, hakan na nuna cewa mu masu tawaliꞌu ne.—Mat. 6:​1-4.

KA “RIƘA YIN TUNANIN DA YA DACE”

13. Mene ne yin “tunanin da ya dace” ya ƙunsa?

13 Mene ne yin “tunanin da ya dace” ya ƙunsa? (1 Bit. 4:​7, NWT) Idan mutum yana tunanin da ya dace, zai nemi sanin raꞌayin Jehobah a duk lokacin da yake tsai da shawara. Irin wannan mutumin ya san cewa babu abin da ya kai dangantakarsa da Jehobah muhimmanci. Ba ya ji da kansa, kuma ba ya ganin cewa ya fi kowa sanin abubuwa. Yana nuna cewa ya dogara ga Jehobah ta wurin yin adduꞌa kullum.

14. Me Bitrus ya yi a karon nan da ya nuna cewa bai dogara ga Jehobah ba?

14 A dare na ƙarshe da Yesu ya yi kafin ya mutu, ya gargaɗi almajiransa cewa: “Dukanku za ku gudu ku bar ni a daren nan.” Amma Bitrus ya buga kirji ya ce, “Ko dukansu sun gudu domin abin da zai faru da kai, ni ba zan gudu ba sam.” Bayan haka, Yesu ya gaya ma wasu cikin almajiransa cewa: “Ku yi tsaro, ku kuma yi adduꞌa.” (Mat. 26:​31, 33, 41) Amma Bitrus bai bi wannan shawarar da Yesu ya bayar ba. Da a ce ya yi hakan, da mai yiwuwa ya yi ƙarfin zuciya ya gaya wa mutane cewa shi almajirin Yesu ne. A maimakon haka, ya yi musun sanin Yesu kuma hakan ya sa shi bakin ciki sosai.—Mat. 26:​69-75.

15. Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana dogara ga Jehobah a daren da ya mutu?

15 Yesu ya dogara ga Jehobah a kome da yake yi. Ko da yake shi bai taɓa yin zunubi ba, ya nemi taimakon Jehobah a kai a kai ta wajen yin adduꞌa. Shi ya sa ya kasance da ƙarfin zuciyar yin abin da Jehobah yake so ya yi. (Mat. 26:​39, 42, 44; Yoh. 18:​4, 5) Babu shakka, Bitrus ya lura da yadda Yesu ya yi adduꞌa sau da yawa a daren da ya mutu, kuma bai manta da shi ba.

16. Ta yaya Bitrus ya nuna cewa yana tunanin da ya dace? (1 Bitrus 4:7)

16 Da shigewar lokaci, Bitrus ya koyi yadda zai dogara ga Jehobah ta wajen yin adduꞌa. Saꞌad da Yesu ya tashi daga mutuwa, ya gaya wa Bitrus da sauran manzannin cewa ruhu mai tsarki zai taimaka musu su ci-gaba da yin waꞌazi. Kuma Yesu ya gaya musu cewa su zauna a Urushalima su jira har lokacin da hakan zai faru. (Luk. 24:49; A. M. 1:​4, 5) Mene ne Bitrus ya yi saꞌad da yake jira? Shi da sauran ꞌyanꞌuwa sun yi ta “yin adduꞌa.” (A. M. 1:​13, 14) Daga baya a wasiƙarsa ta farko, Bitrus ya ƙarfafa Kiristoci su kasance da tunanin da ya dace kuma su nuna sun dogara ga Jehobah ta wajen yin adduꞌa. (Karanta 1 Bitrus 4:7.) Bitrus ya koyi yadda zai riƙa dogara ga Jehobah kuma ya taimaka wa ꞌyanꞌuwa maza da mata da yawa.—Gal. 2:9.

17. Mene ne muke bukatar mu dinga yi komen baiwarmu? (Ka kuma duba hoton.)

17 Idan muna son mu kasance da tunanin da ya dace, wajibi ne mu riƙa yin adduꞌa ga Jehobah. Za mu yi hakan ko da muna ganin abin da muke so mu yi bai da wuya ko kuma abu ne da muka iya sosai. Mafi muhimmanci ma, idan muna so mu yanke wata shawara ta musamman, za mu nemi taimakon Jehobah da tabbaci cewa ya san abin da muka fi so.

Bitrus ya nuna cewa ya koyi dogara ga Jehobah ta wajen yin adduꞌa. Mu ma za mu nuna cewa muna tunanin da ya dace ta wurin neman taimakon Jehobah, musamman a lokacin da muke so mu yanke wata shawara mai muhimmanci (Ka duba sakin layi na 17)a


18. Ta yaya za mu sa tunaninmu ya jitu da na Jehobah?

18 Muna godiya sosai cewa Jehobah ya halicce mu yadda za mu iya yin koyi da halayensa. (Far. 1:26) Gaskiyar ita ce, ba za mu iya yin koyi da Jehobah babu kuskure ba. (Isha. 55:9) Amma, kamar Bitrus, za mu ci-gaba da sa tunaninmu ya jitu da na Jehobah ta wajen koyi da yadda yake tunani, da zama masu tawaliꞌu, da kuma yin tunanin da ya dace.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya za mu riƙa yin tunanin da ya jitu da na Jehobah?

  • Ta yaya za mu zama masu tawaliꞌu?

  • Ta yaya za mu zama masu yin “tunanin da ya dace”?

WAƘA TA 30 Jehobah Ubana, Allahna da Abokina

a BAYANI A KAN HOTO: Wata ꞌyarꞌuwa tana adduꞌa a zuciyarta saꞌad da take jira a yi mata intabiyu a wurin da ta je neman aiki.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba