Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littattafan Hausa (1987-2027)
Fita
Shiga Ciki
Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Yau

Jumma’a, 16 ga Oktoba

Kada ku yarda irin wannan mace ta ja hankalinku zuwa hanyar rayuwarta, kada ku bi hanyoyinta.—K. Mag. 7:25.

Wannan labarin ya nuna abin da zai iya faruwa da kowannenmu. Mutum zai iya yin zunubi mai tsanani kuma ya ɗauka cewa abin ya faru ne ba labari wato bai yi zaton cewa hakan zai faru ba. Amma idan ya yi tunani da kyau, zai ga cewa akwai wasu kurakurai da ya yi da suka kai shi ga yin wannan zunubi. Wataƙila ya soma bin abokan banza, ko yana yin nishaɗi marar kyau, ko ya je inda bai dace Kirista ya je ba, ko ya shiga dandalin intane marar kyau. Wataƙila ma ya daina karanta Littafi Mai Tsarki, da yin adduꞌa, da yin waꞌazi. Kamar matashin nan a littafin Karin Magana, kurakurai da ya yi ne suka kai shi ga yin wannan zunubi. Mene ne darasin? Muna bukatar mu guji yin zunubi, amma kuma, yana da muhimmanci mu guji abubuwan da za su iya kai mu ga yin zunubi. Bayani da Sulemanu ya yi ke nan bayan da ya ba da labarin.—Mat. 5:29, 30. w24.07 16 sakin layi na 10-11

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026

Asabar, 17 ga Oktoba

Muna da wannan kaya mai-daraja cikin tukwane na ƙasa.—2 Kor. 4:​7, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

Mene ne wannan kaya mai daraja? Yana nufin waꞌazin Mulkin Allah da ke ceton rayukan mutane. (2 Kor. 4:1) Mene ne tukwane na ƙasa suke nufi? Suna nufin bayin Allah da suke gaya wa mutane labari mai daɗi. A lokacin manzo Bulus, ꞌyan kasuwa sukan yi amfani da tukwane na ƙasa don su kai abubuwa masu daraja kamar abinci, da ruwan inabi, da kuɗi zuwa inda ake bukatar su. Haka ma, Jehobah yana amfani da mu wajen kai wa mutane bisharar nan mai daraja. Da yake Jehobah yana tare da mu, zai ba mu ƙarfin da muke bukata don mu ci-gaba da yin waꞌazi. A wasu lokuta, za mu ji tsoro cewa mutane ba za su so su ji waꞌazinmu ba, ko kuma za su tsananta mana. Ta yaya za mu shawo kan irin wannan tsoron? Ka yi laꞌakari da adduꞌar da manzanni suka yi saꞌad da aka ce su daina yin waꞌazi. Ba su daina yin waꞌazi saboda tsoro ba, amma sun roƙi Jehobah ya ba su ƙarfin halin faɗin kalmarsa babu tsoro. Nan-da-nan Jehobah ya amsa adduꞌarsu. (A. M. 4:​18, 29, 31) Idan a wasu lokuta kana jin irin wannan tsoro, ka roƙi Jehobah ya sa ka ƙara ƙaunar mutane don ka iya shawo kan tsoron da kake ji. w24.04 16 sakin layi na 8-9

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026

Lahadi, 18 ga Oktoba

Ubanmu wanda yake cikin sama, a kiyaye sunanka da tsarki.—Mat. 6:9.

Ƙaunar da muke yi wa Jehobah tana sa mu tsarkake sunansa. Hakan yana nufi cewa muna so mu taimaka wa mutane su san cewa abubuwa da Shaiɗan ya faɗa game da Allah ƙarya ne. (Far. 3:​1-5; Ayu. 2:4; Yoh. 8:44) Muna marmarin gaya wa mutane gaskiya game da Allah yayin da muke waꞌazi. Muna so kowa-da-kowa ya san cewa halin da ya fi nunawa shi ne ƙauna, yana yin mulki cikin adalci da gaskiya, kuma Mulkinsa zai kawo ƙarshen dukan matsaloli da muke fuskanta. Saꞌan nan kowa a duniya zai zauna cikin salama da kwanciyar hankali. (Zab. 37:​10, 11, 29; 1 Yoh. 4:8) Idan muna gaya wa mutane abubuwan nan game da Jehobah, muna tsarkake sunansa ke nan. Kuma muna farin ciki don mun san aiki da ya kamata mu yi ke nan. w24.05 18 sakin layi na 12

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2026
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba