TALIFIN NAZARI NA 51
WAƘA TA 132 Yanzu Mun Zama Ɗaya
Yadda Za Ku Shirya Bikin Auren da Zai Ɗaukaka Jehobah
“Sai dai a yi kome yadda ya kamata, a shirye kuma.”—1 KOR. 14:40.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda waɗanda suke so su yi aure za su ɗaukaka Jehobah a ranar aurensu.
1-2. Yaya Jehobah yake so ranar aurenku ta kasance?
KUN riga kun yi wa juna alkawarin aure? Idan haka ne, muna taya ku murna! Mai yiwuwa kun soma shirya yadda bikin aurenku zai kasance. Jehobah yana son ku ji daɗin bikin aurenku.a Kuma ku ci-gaba da yin farin ciki bayan hakan.—K. Mag. 5:18; W. Waƙ. 3:11.
2 Yana da muhimmanci ku ɗaukaka Jehobah a bikin aurenku. Me ya sa muka ce hakan? Kuma ta yaya za ku iya yin hakan? Ko da yake an shirya wannan talifin don waɗanda suke shirin aure ne, abubuwan da ke ciki za su taimaka wa dukanmu mu ɗaukaka Jehobah idan aka gayyace mu zuwa bikin aure, ko kuma idan waɗanda suke son su yi aure sun nemi shawararmu.
ME YA SA ZAI DACE KU ƊAUKAKA JEHOBAH?
3. Mene ne waɗanda suke shirin yin aure suke bukatar su yi, kuma me ya sa?
3 Waɗanda suke shirin yin aure suna bukatar su tabbata cewa komen da suke so su yi ya jitu da ƙaꞌidodin Jehobah da ke Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Domin Jehobah ne ya fara ɗaura aure. Shi ne ya haɗa auren Adamu da Hauwaꞌu. (Far. 1:28; 2:24) Saboda haka, waɗanda suke so su yi aure suna bukatar su tabbata cewa aurensu ya ɗaukaka Jehobah.
4. Wane dalili ne kuma zai sa waɗanda suke shirin yin aure su ɗaukaka Jehobah?
4 Akwai wani dalili kuma da ya sa kuke bukatar ku kasance da raꞌayin Jehobah saꞌad da kuke shirin yin aure. Dalilin shi ne, Jehobah ne Ubanku na sama da kuma abokinku da babu kamar sa. (Ibran. 12:9) Babu shakka, kuna son dangantakar da ke tsakaninku ta ci-gaba. Ba za ku so wani abin da zai ɓata wa Jehobah rai ya faru a ranar aurenku, ko wata rana dabam ba. (Zab. 25:14) Idan kun yi tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi muku, da kuma waɗanda zai yi muke a nan gaba, hakan zai sa ku ɗaukaka shi a ranar aurenku?—Zab. 116:12.
TA YAYA ZA KU ƊAUKAKA JEHOBAH?
5. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka wa waɗanda suke so su yi aure su tsai da shawarwari masu kyau?
5 Littafi Mai Tsarki bai ba da jerin abubuwan da Kiristoci za su yi a bikin aurensu ba. Saboda haka, waɗanda suke so su yi aure za su iya shirya shi yadda suke so bisa ga yanayinsu, ko kuma alꞌadarsu. Ban da haka ma, wajibi ne Kiristocin da suke so su yi aure su bi dokar da gwamnati ta kafa a yankinsu. (Mat. 22:21) Amma, ko da yaya ne waɗanda suke so su yi aure suka zaɓi su yi bikinsu, idan sun bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki, za su ɗaukaka Jehobah kuma su sa shi farin ciki. Tambayar ita ce, waɗanne ƙaꞌidodi ne ya kamata ku yi laꞌakari da su?
6. Me ya sa yake da muhimmanci waɗanda suke so su yi aure su bi dokar gwamnati game da aure?
6 Ku bi dokar da gwamnati ta kafa. (Rom. 13:1, 2) A yawancin ƙasashe, akwai dokar da gwamnati ta kafa don waɗanda suke so su yi aure. Zai dace waɗanda suke so su yi aure su yi bincike don su gane abin da ya kamata su yi. Idan kuna da tambaya game da dokokin nan, za ku iya tambayar dattawa.b
7. Mene ne za ku yi don kome ya tafi daidai a bikin aurenku?
7 Ku tabbata cewa kome ya tafi daidai a bikin. (1 Kor. 10:31, 32) Ku yi ƙoƙari ku sa bikin aurenku ya nuna cewa kuna da halaye masu kyau da ruhu mai tsarki yake bayarwa, ba halayen mutanen duniya ba. (Gal. 5:19-26) Da yake namiji ne yake da hakkin yin ja-goranci a iyali, shi ne zai tabbata cewa kome ya tafi daidai, kuma an ji daɗin bikin. To, mene ne zai taimaka hakan ya yiwu? Idan aka yi jawabi daga Littafi Mai Tsarki cikin ƙauna, da daraja, hakan zai sa kowa ya san cewa aure kyauta ce daga wurin Jehobah. Jawabin zai kuma taimaka wa dukan waɗanda suka halarci bikin su gane cewa aure ba abin wasa ba ne. Yawancin ꞌyanꞌuwa sukan zaɓi a yi jawabin a Majamiꞌar Mulki idan zai yiwu. Idan kuna so ku yi amfani da Majamiꞌar Mulki, ku rubuta wa dattawa tun da wuri don su ba ku izinin yin amfani da shi.
8. Ta yaya za ku tabbata cewa bikin aurenku ya ɗaukaka Jehobah? (Romawa 13:13)
8 Karanta Romawa 13:13. Idan kuna so ku yi liyafa bayan jawabin, ta yaya za ku guji yin sa yadda mutanen duniya suke yi? Kalmar Girkanci da aka fassara zuwa “bukukuwan iskanci,” ta ƙunshi bukukuwan da ake shan giya da yawa, da kuma shan kiɗa har can cikin dare. Idan za ku ba da giya a bikin aurenku, ku ɗauki matakan da za su sa mutane ba za su sha da yawa ba.c Idan za a yi kiɗa da waƙa, a yi shi yadda ba zai hana mutane hira da juna ba. Ku bincika waƙoƙin da za a yi a wurin da kyau don kada wani ya ji wani iri.
9. Wane shiri ne waɗanda suke so su yi aure za su yi game da abubuwan da za a faɗa da kuma abubuwan da za a yi a bikin?
9 A wasu wurare a lokacin bikin aure, iyalai da kuma abokan amarya da angon sukan tashi su faɗi wasu abubuwa game da su. A wasu wurare kuma, akan nuna hotuna ko bidiyoyin amarya da angon, ko kuma wasu abubuwa dabam. Waɗannan abubuwan suna sa mutane su ji daɗi, kuma su riƙa tunawa da bikin. Amma ko da mene ne kuka zaɓa, ku tabbata cewa abu ne da zai ƙarfafa mutane. (Filib. 4:8) Ku tambayi kanku: ‘Abin zai nuna cewa muna daraja mutane? Zai sa mutane su ɗauki zaman aure da muhimmanci?’ Mafi muhimmanci ma: ‘Zai ɗaukaka Jehobah?’ Ko da yake za a iya faɗan abubuwan da za su sa mutane dariya, ba zai dace a faɗi abubuwan iskanci ko lalata ba. (Afis. 5:3) Idan ꞌyan iyalinku ko abokanku za su yi magana a bikin, ku gaya musu abubuwan da kuke so su faɗa da waɗanda ba kwa so.
10. Me ya sa zai dace waɗanda suke shirin aure kada su wuce gona da iri? (1 Yohanna 2:15-17)
10 Kada ku wuce gona da iri. (Karanta 1 Yohanna 2:15-17.) Jehobah yana farin ciki idan bayinsa suka ɗaukaka shi maimakon su ɗaukaka kansu. Saboda haka, zai dace kada waɗanda suke shirin yin aure su kashe kuɗi da yawa, ko kuma su yi bikin da zai nuna cewa suna “taƙama da abubuwan rayuwa.” Ta yaya za ku amfana idan ba ku wuce gona da iri a bikin aurenku ba? Ku yi laꞌakari da abin da Ɗanꞌuwa Mike daga Norway ya ce, “Da yake ba mu kashe kuɗi da yawa ba, ba wanda yake bin mu bashi, kuma mun ci-gaba da hidimar majagaba. Ko da yake aurenmu ɗan daidai-daidai ne, mun ji daɗinsa kuma ya yi kyau sosai.” Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Tabitha daga Indiya ta ce: “Da yake mun yi aurenmu ɗan daidai-daidai, hakan ya rage mana yawan damuwa. Ni da wanda zan aura da kuma iyalanmu ba mu sami saɓani sosai ba.”
Ko da a ina ne muke zama, Kiristoci za su iya yin auren da ba sai sun kashe kuɗi da yawa ba kuma a ji daɗinsa (Ka duba sakin layi na 10-11)
11. Wane irin kaya ne zai dace amarya da ango su saka a ranar aurensu? (Ka kuma duba hotunan.)
11 Shin, kun zaɓi irin kayan da za ku sa a ranar aurenku? Babu shakka, za ku so ku yi kyau a ranar. Hakan na da kyau. Domin ko a Littafi Mai Tsarki ma, an faɗi yadda amarya da ango suke yin shiri sosai don su yi kyau. (Isha. 61:10) Ko da yake kayan da za ku sa a ranar aurenku zai iya yin dabam da wanda kuka saba sakawa. Duk da haka, zai yi kyau ku sa waɗanda suka dace, da ba za su sa mutane su ji wani iri ba. (1 Tim. 2:9) Ku yi hankali kada rigunan da za ku sa, ko kuma adon da za ku yi, su zama abubuwan da suka fi muhimmanci a ranar aurenku.—1 Bit. 3:3, 4.
12. Me ya sa zai dace waɗanda za su yi aure su guji alꞌadun da suka saɓa wa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki?
12 Ku guji alꞌadun da suka saɓa wa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. (R. Yar. 18:4) Yawancin alꞌadun da ake bi saꞌad da ake bikin aure suna da alaƙa da sihiri, ko addinan ƙarya, ko kuma camfi. Jehobah ya gaya mana dalla-dalla cewa mu guji irin waɗannan abubuwan. (2 Kor. 6:14-17) Idan akwai wata alꞌada da mutane a yankinku suke bi da kuke shakkar sa, ku yi ƙoƙari ku san tushensu. Kuma ku san ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka muku ku tsai da shawara a kan abubuwan da za ku iya yi a ranar aurenku.
13. Ta yaya waɗanda suke shirin yin aure za su yi koyi da Jehobah a batun kyaututtuka da ake bayarwa a ranar aure?
13 A yankinku, mutane suna ba wa amarya da ango kyaututtuka ne? Mutane da yawa sukan ba da kyauta daidai da aljihunsu ne. An ƙarfafa Kiristoci su riƙa bayarwa kuma hakan na sa su farin ciki. (K. Mag. 11:25; A. M. 20:35) Amma, bai kamata waɗanda suke shirin yin aure su sa mutane dole su ba su kyaututtuka ba, ko kuma su sa su ji kamar abin da suka bayar ya yi kaɗan. Muna koyi da Jehobah kuma ba ma rena abin da mutane suka ba mu ko da kaɗan ne muddin sun yi hakan da zuciya ɗaya.—2 Kor. 9:7.
YADDA ZA KU GUJE KO KU MAGANCE MATSALOLI
14. Waɗanne matsaloli ne wasu da suke shirin aure suke fama da su?
14 Yayin da kuke shirin aure a hanyar da zai ɗaukaka Jehobah, za ku iya fuskantar matsaloli. Alal misali, zai iya yi muku wuya ku shirya aurenku a hanyar da ba za ku kashe kuɗi da yawa ba. Wani ɗanꞌuwa mai suna Charlie daga Solomon Islands ya ce: “Ya yi mana wuya sosai mu san waɗanda za mu gayyata zuwa bikin aurenmu. Muna da abokai da yawa, kuma a alꞌadarmu ya kamata mu gayyaci dukansu!” ꞌYarꞌuwa Tabitha da aka ambata ɗazu ta ce: “A yankinmu ana yawan tara jamaꞌa sosai a bikin aure. Ya ɗau lokaci sosai kafin iyayenmu suka yarda cewa mutane 100 ne kawai za mu gayyata.” Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Sarah daga Indiya ta ce: “Wasu mutane sukan mai da hankali a kan yawan arzikinsu, da kuma raꞌayin mutane game da su. Wasu dangina sun kashe kuɗi sosai a bikin aurensu. Hakan ya sa wasu sun so in yi bikina fiye da nasu.” Me zai taimaka muku ku shawo kan irin matsalolin nan da dai sauransu?
15. Me ya sa adduꞌa take da muhimmanci saꞌad da kuke shirin aurenku?
15 Ku riƙa yin adduꞌa saꞌad da kuke shirye-shiryen aurenku. Za ku iya gaya wa Jehobah abubuwan da kuke fama da su, ko kuma yadda kuke ji a zukatanku. (Filib. 4:6, 7) Za ku iya roƙonsa ya taimaka muku ku tsai da shawarwarin da suka dace, ku kasance da kwanciyar hankali, kuma ku iya nuna ƙarfin zuciya a lokacin da kuke bukata. (1 Bit. 5:7) Yayin da kuke ganin yadda Jehobah yake amsa adduꞌoꞌinku, hakan zai sa ku ƙara dogara gare shi. ꞌYarꞌuwa Tabitha da aka ambata ɗazu ta ce: “Ni da wanda zan aura muna ganin kamar za mu yi gardama da juna, ko da iyalanmu saꞌad da muke shiri. Saboda haka, a duk lokacin da za mu tattauna game da bikin, mukan fara da adduꞌa. Mun ga taimakon Jehobah kuma ba mu yi gardama da juna ba.”
16-17. Ta yaya tattaunawa da kyau zai taimaka muku saꞌad da kuke shirin aure?
16 Ku nuna kuna daraja juna saꞌad da kuke tattaunawa. (K. Mag. 15:22) Idan kuna shirin yin aure, kuna bukatar ku tsai da shawarwari da yawa. Alal misali, za ku zaɓi ranar da za a yi bikin auren, da yawan kuɗin da za ku kashe, da iya mutanen da za su zo bikin, da dai sauransu. Kafin ku yanke shawara, zai dace ku ji raꞌayin juna, ku bincika ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka, kuma ku yi laꞌakari da duk wata shawara da ꞌyanꞌuwan da suka manyanta suka ba ku. Saꞌad da kuke tattaunawa da juna da kuma danginku game da abin da kuke so, ku yi hakan da alheri, da kuma sanin ya kamata. Ƙari ga haka, ku kasance da niyyar canja raꞌayinku. Idan iyayenku suna so ku yi wani abin da bai taka kara ya karya ba, kuma ba laifi ba ne, ku yi ƙoƙari ku yi abin da suka ce. Su ma ranar farin ciki ne a gare su. Idan ba za ku iya yin abin da suka ce ba, ku bayyana musu dalilin cikin alheri da kuma ƙauna. (Kol. 4:6) Ku taimaka wa danginku su fahimci cewa burinku shi ne ku yi auren da zai ɗaukaka Jehobah.
17 Idan iyayenku ba Shaidu ba ne, zai iya yi muku wuya ku bayyana musu abin da kuke so kuma su fahimci raꞌayinku. Amma abu ne da zai yiwu. Wani ɗanꞌuwa mai suna Santhosh daga Indiya ya ce: “Danginmu sun so mu yi wasu abubuwan da ake yi a addinin Hindu a bikin aurenmu. Bai yi wa ni da ꞌyarꞌuwar da zan aura sauƙi mu bayyana wa danginmu abin da muke so ba. Mun yarda cewa za mu yi wasu abubuwan da suke so da ba su saɓa wa ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki ba. Alal misali, mun canja abincin da muka yi niyyar bayarwa zuwa wanda suke so. Kuma ba mu yi waƙa ko rawa ba don ba su saba da ganin hakan ba.”
18. Me zai taimaka muku ku tabbata cewa kome ya tafi sumul a ranar aurenku? (1 Korintiyawa 14:40) (Ka kuma duba hoton.)
18 Ku yi shiri da kyau. Idan kuka yi shiri da kyau, hakan zai rage muku yawan damuwa a ranar aurenku. (Karanta 1 Korintiyawa 14:40.) Wani ɗanꞌuwa mai suna Wayne daga Taiwan ya ce: “ꞌYan kwanaki kafin aurenmu, mun tattauna da ꞌyanꞌuwan da suke so su taimaka mana da wasu ayyuka. Mun yi magana a kan wasu abubuwan da za a yi a ranar, kuma muka gwada yadda za a yi wasu daga cikinsu don mu tabbata cewa kome ya tafi daidai a ranar.” Ku yi ƙoƙari ku yi kome a kan lokaci don ku nuna kun daraja waɗanda kuka gayyata.
Yin shiri da kyau zai taimaka kome ya tafi sumul a ranar auren (Ka duba sakin layi na 18)
19. Me zai taimaka bikin aurenku ya kasance da tsari?
19 Yin tunani da wuri a kan abin da zai iya faruwa a bikin aurenku, zai taimaka muku ku guji matsaloli da yawa. (K. Mag. 22:3) Alal misali, idan a yankinku mutane sukan je bikin aure ko da ba a gayyace su ba, ku yi tunanin abin da za ku iya yi domin kada hakan ya faru. Ku tabbata cewa kun bayyana wa danginku da ba Shaidu ba abubuwan da za su iya gani a wurin bikin, da kuma wasu alꞌadun da ba ma yi. Za ku iya nuna musu talifin nan “Me Ake Yi a Bikin Daurin Auren Shaidun Jehobah?” da ke jw.org/ha. Wani abin da zai taimaka bikin ya kasance da tsari shi ne, ku sa wani ɗanꞌuwa da ya manyanta ya zama muku “uban bikin.” (Yoh. 2:8) Idan kun gaya masa yadda kuke son abubuwa su gudana a ranar, zai taimaka muku ku iya cim ma hakan.
20. Mene ne ya kamata waɗanda suke shirin yin aure su tuna game da ranar aurensu?
20 Hankalin mutum zai iya tashi saꞌad da yake shirye-shiryen aure. Amma ku tuna cewa, rana ɗaya ne kawai za a yi bikin. Rana ce da za ku soma bauta wa Jehobah tare da wanda kuke ƙauna. Saboda haka, ku yi iya ƙoƙarinku ku yi bikin aurenku daidai wa daida. Ku dogara ga Jehobah. Da taimakonsa, za ku iya shirya auren da za ku ji daɗinsa kuma ba za ku yi da na sani ba.—Zab. 37:3, 4.
WAƘA TA 107 Mu Yi Koyi da Allah a Nuna Ƙauna
a MAꞌANAR WASU KALMOMI: A yawancin alꞌadu, waɗanda suke so su yi aure suna yi wa Allah da juna alkawari cewa za su zauna tare har abada. Bayan haka, wasu sukan yi liyafa. A wuraren da ba a yin waɗannan abubuwan, yana da muhimmanci waɗanda suke so su yi aure su bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki a ranar aurensu.
b Don samun ƙarin bayani game da yadda Kiristoci suke ɗaukan dokar gwamnati game da aure, ka duba talifin nan “Aure Mai Daraja A Gaban Allah Da Mutum” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2006.
c Ka duba bidiyon nan Zai Dace In Ba da Giya a Bikina?, a jw.org/ha.