Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Agusta pp. 26-30
  • Duk da Cewa Ni Mai Kunya Ce, Na Zama Mai Waꞌazi a Ƙasar Waje

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Duk da Cewa Ni Mai Kunya Ce, Na Zama Mai Waꞌazi a Ƙasar Waje
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • NA SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI
  • NA SOMA MARMARIN YIN HIDIMA A ƘASAR WAJE
  • HIDIMA A ƘASAR DA AKE YAƘI
  • AN BA MU SABON AIKI
  • FAMA DA RASHIN LAFIYA
  • INA GODIYA GA JEHOBAH DON TAIMAKONSA
  • An Yi Nasara A Kamfen Na Musamman Da Aka Yi A Bulgeriya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Jehobah Ya ‘Daidaita Hanyoyina’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Bulgariya
    Labarai
  • Jehobah Ya Koyar da Ni Tun Ina Ƙarami
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Agusta pp. 26-30
Marianne Wertholz.

TARIHI

Duk da Cewa Ni Mai Kunya Ce, Na Zama Mai Waꞌazi a Ƙasar Waje

MARIANNE WERTHOLZ CE TA BA DA LABARIN

DA NAKE ƙarama, ina da kunya sosai kuma ina tsoron mutane. Amma Jehobah ya taimaka mini in ƙaunaci mutane kuma in zama mai waꞌazi a ƙasar waje. Ta yaya ya yi hakan? Da farko, ta wurin abubuwa masu kyau da mahaifina ya koya mini game da Jehobah. Na biyu, ta wurin misali mai kyau na wata ꞌyarꞌuwa mai shekara 16. Na uku, ta wurin maigidana. Ya ƙarfafa ni kuma ya yi haƙuri da ni. Bari in ba ku labarina.

An haife ni a 1951 a Biyana, Ostiriya, kuma iyayena ꞌyan Katolika ne. Ina da kunya sosai, amma na gaskata da Allah kuma ina yawan yin adduꞌa. Da nake shekara tara, babana ya fara nazari da Shaidun Jehobah; kuma daga baya, mamata ta soma.

Ni da ꞌyarꞌuwata Elisabeth (ita ce a baya)

Ba da daɗewa ba, mun soma zuwa Ikilisiyar Döbling da ke Biyana. Mun yi abubuwa da yawa tare a matsayin iyali. Muna yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare, da halartan taro, da kuma taimakawa a taron daꞌira. A wannan lokacin, babanmu ya taimaka min in ƙaunaci Jehobah sosai. Babanmu ya yi ta fatan cewa ni da ꞌyarꞌuwata za mu zama majagaba wata rana. Amma a lokacin, ba abin da nake so in yi ba ke nan.

NA SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI

Na yi baftisma a 1965, saꞌad da nake shekara 14. Amma yana yi min wuya in yi wa mutanen da ban sani ba waꞌazi. Ban da haka ma, ina yawan ganin ban kai wasu saꞌannina ba, kuma ina so in zama abokiyarsu. Saboda haka, ba da daɗewa ba bayan na yi baftisma, na soma ƙulla abokantaka da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. Ko da yake ina jin daɗin zama da su, na damu sosai domin na san cewa bai kamata in ƙulla abota da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah ba. Amma ya yi min wuya in rabu da su. Mene ne ya taimaka mini?

Marianne da Dorothée.

Na koyi abubuwa da yawa daga wurin Dorothée (ita ce a hagu)

A lokacin ne wata ꞌyar shekara 16 mai suna Dorothée ta zama mai shela a ikilisiyarmu. Na yi mamakin yadda take son fita waꞌazi. Ko da yake na ɗan girme ta, ba na fita waꞌazi kamar yadda take yi. Sai na ce wa kaina: ‘Iyayena Shaidu ne, amma Dorothée ce kaɗai take bauta wa Jehobah a iyalinsu. Ga shi tana zama da mamarta da ba ta da lafiya, duk da haka, tana yawan fita waꞌazi!’ Misalinta ya sa na so in ƙara ƙwazo a ibadata ga Jehobah. Ba da daɗewa ba, ni da Dorothée muka soma hidimar majagaba. Da farko, mun soma hidimar majagaba na ɗan lokaci tare, daga baya muka soma hidimar majagaba na kullum. Ita ce ta taimaka min in sami wadda na soma nazari da ita. Daga baya, ya soma yi min sauƙi in yi wa mutane waꞌazi a gidajensu, ko a kan titi, ko kuma a wasu wurare dabam.

Bayan na yi shekara ɗaya ina hidimar majagaba, wani ɗanꞌuwa mai suna Heinz ya zo ikilisiyarmu. Ya koyi gaskiya game da Jehobah a Kanada, lokacin da ya ziyarci ɗanꞌuwansa da Mashaidi ne. An tura shi a matsayin majagaba na musamman a ikilisiyarmu da ke Biyana. Na so shi nan take da na gan shi. Amma yana so ya zama mai waꞌazi a ƙasar waje, ni kuma ba na so. Saboda haka da farko, ban nuna masa ina son sa ba. Daga baya, mun soma soyayya, muka yi aure kuma muka soma hidimar majagaba a Ostiriya.

NA SOMA MARMARIN YIN HIDIMA A ƘASAR WAJE

A yawancin lokaci, Heinz yakan gaya min yadda yake son yin hidima a ƙasar waje. Ko da yake bai tilasta min in kasance da raꞌayinsa ba, ya taimaka min in yi tunani ta wajen yi min wasu tambayoyi kamar, “Tun da ba mu haihu ba, za mu iya faɗaɗa hidimarmu ga Jehobah?” Amma da yake ni mai kunya ce sosai, na ji tsoron zama mai waꞌazi a ƙasar waje. Ko da yake ina jin kunya sosai, na soma hidimar majagaba, amma na ga kamar ba zan iya yin hidima a ƙasar waje ba. Duk da haka, maigidana ya ci-gaba da taimaka min in yi tunani ko za mu iya zuwa yin hidima a ƙasar waje. Ya ƙarfafa ni in mai da hankali ga taimaka wa mutane, maimakon damuwa da kasawata. Shawarar da ya ba ni ta taimaka mini sosai.

Maigidana Heinz yana gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro a wata ƙaramar ikilisiya da ake yaren Serbo-Croatia, a Salzburg, Ostiriya a 1974

A sannu a hankali, na soma gani kamar zan iya yin hidima a ƙasar waje, sai muka cika fom na zuwa Makarantar Gilead. Amma wani ɗanꞌuwa da ke hidima a reshen ofishinmu ya gaya min cewa, ina bukatar in inganta yadda nake yin Turanci. Bayan na yi shekara uku ina ƙoƙarin inganta yadda nake yin Turanci, mun yi mamaki da aka ce mu yi hidima a wata ikilisiya da ake yaren Serbo-Croatia da ke Salzburg, Ostiriya. Mun yi shekaru bakwai muna waꞌazi ga mutanen da ke wannan yaren. Daga baya, maigidana ya zama mai kula da daꞌira, kuma mun yi shekara ɗaya muna ziyartar ikilisiyoyi da ke yaren. Yaren Serbo-Croatia yana da wuya, amma muna da daliɓai da yawa.

A 1979, ꞌyanꞌuwa da ke ja-goranci a reshen ofishinmu sun ce mana mu je Bulgeriya na ɗan lokaci. Da yake an hana aikinmu a wurin, sun ce mu yi kamar mun je “hutu” ne. Sun ce mana kar mu yi waꞌazi, amma sun ba mu wasu ƙananan littattafai da za mu yi ƙoƙari mu ba wa ꞌyanꞌuwa mata biyar a ɓoye da suke zama a Sofiya, babban birnin Bulgeriya. Na ji tsoro sosai, amma Jehobah ya taimaka min in kwantar da hankalina. Ganin yadda ꞌyanꞌuwa matan nan suke farin ciki da kuma nuna ƙarfin zuciya, duk da cewa za a iya sa su a kurkuku, ya taimaka min in kasance da ƙarfin zuciya wajen yin kowane aikin da ƙungiyar Jehobah ta ba ni.

Da shigewar lokaci, mun sake cika fom na makarantar Gilead, sai aka kira mu. Mun ɗauka cewa za mu halarci makarantar da ake gudanar da Turanci a ƙasar Amurka. Amma a Nuwamba 1981, ƙungiyarmu ta soma gudanar da makarantar Gilead a ƙasar Jamus. Kuma da yake an gudanar da ajin a yaren Jamusanci, na fahimci kome da kome. Amma yanzu tambayar ita ce, a ina ne za a tura mu hidima?

HIDIMA A ƘASAR DA AKE YAƘI

An tura mu hidima a ƙasar Kenya! Amma ꞌyanꞌuwa da ke kula da reshen ofishinmu a ƙasar Kenya sun tambaye mu ko za mu so mu yi hidima a ƙasar Yuganda. Shekaru goma kafin wannan lokacin, wani soja mai suna Idi Amin ya kwace mulki a ƙasar Yuganda. Saꞌad da yake mulki, ya sa an kashe duban mutane, kuma miliyoyin mutane sun sha wahala sosai. Ana nan kuma a 1979, sai aka kwace mulki daga hannunsa. Shi ya sa da farko mun ji tsoron zuwa wannan ƙasar. Amma a makarantar Gilead, an ƙarfafa mu mu riƙa dogara ga Jehobah. Saboda haka, mun amince za mu je.

A lokacin, rayuwa a Yuganda bai da sauƙi. Abubuwa da dama ba sa aiki. Babu ruwa, babu wutan lantarki, babu network. Ana yawan sata da harbe-harbe musamman da dare. Saboda haka, idan dare ya yi ba mai fita. Kowa na alla-alla gari ya waye don kada a zo a yi musu sata ko kuma a kashe su. Duk da matsalolin nan, ꞌyanꞌuwa maza da mata a Yuganda sun ci-gaba da bauta wa Jehobah da farin ciki!

Muna dafa abinci a gidan su Ɗanꞌuwa Waiswa

A 1982, ni da maigidana mun isa Kampala, babban birnin Yuganda. Mun yi wata biyar muna zama a gidan Ɗanꞌuwa Sam Waiswa da matarsa Christina, tare da yaransu biyar da kuma danginsu guda huɗu. A yawancin lokuta, sau ɗaya suke cin abinci a rana. Duk da haka, sun karɓe mu hannu bibbiyu, kuma suna ba mu ɗan abin da suke da shi. Zama da su Waiswa, ya taimaka mana mu koyi abubuwa da suka amfane mu daga baya. Alal misali, mun koyi yadda za mu riƙa yin wanka da ruwa kaɗan, kuma mu tara ruwan don mu yi amfani da shi a bayan gida. A 1983, mun sami gida a wani wuri a Kampala inda ba a tashin hankali sosai.

Mun ji daɗin yin waꞌazi a Kampala ba kaɗan ba. Na tuna cewa akwai watan da muka rarraba mujallu fiye da 4,000! Amma abin da ya fi sa mu farin ciki shi ne ganin yadda mutane suke saurarar mu. Sun san darajar Allah, kuma suna son tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki. Ina nazari da mutane aƙalla 10 zuwa 15, maigidana ma hakan. Kuma mun koyi abubuwa da yawa daga wurin ɗalibanmu. Alal misali, ko da yake suna taka zuwa taron ikilisiya kowane mako, hakan ba ya damun su kuma suna farin ciki.

Tsakanin 1985 da 1986, an yi yaƙi sau biyu a Yuganda. Muna yawan ganin yara ɗauke da mayan bindigogi. Ana sa su tare hanya a matsayin sojoji, su riƙa bincika mutane da ababan hawa. A wannan lokacin, mukan roƙi Jehobah ya taimaka mana mu yi waꞌazi ba tare da tsoro ba, kuma mu iya guje wa wurare masu haɗari. Kuma Jehobah ya amsa adduꞌarmu. Mukan manta cewa ana yaƙi a duk lokacin da muka haɗu da wanda yake so ya koyi game da Jehovah.

Ni da maigidana da Tatjana (ita ce a tsakiya)

Mun kuma ji daɗin yi wa baƙin da suke zama a Yuganda waꞌazi. Alal misali, mun haɗu kuma mun soma nazari da Murat Ibatullin da matarsa Dilbar. Sun fito ne daga Tatarstan, wani wuri a ƙasar Rasha. Murat likita ne. Su biyu sun yi baftisma kuma suna bauta wa Jehobah da aminci. Daga baya, na haɗu da wata mata ꞌyar ƙasar Yukiren mai suna Tatjana Vileyska da ta so ta kashe kanta. Bayan ta yi baftisma, ta koma ƙasar Yukiren kuma ta yi hidima a sashen fassara yaren Yukiren a reshen ofishinmu.a

AN BA MU SABON AIKI

A 1991 saꞌad da ni da maigidana muka je hutu a ƙasar Ostiriya, mun sami wasiƙa daga reshen ofishinmu da ke ƙasar. A wasiƙar, an gaya mana cewa za a ba mu sabon aiki. An ce za mu soma yin hidima a ƙasar Bulgeriya. Shekaru da yawa kafin wannan lokacin, an sa wa aikinmu takunkumi a wasu ƙasashe a Turai. Daga baya an ɗaga takunkumin, kuma aka ba mu damar yin waꞌazi a ƙasashen nan. Ƙasar Bulgeriya na ɗaya daga cikinsu. Kamar yadda na ambata ɗazu, ni da maigidana mun taɓa kai littattafanmu a ɓoye zuwa wannan ƙasar lokacin da aka hana aikinmu. Amma yanzu, an tura mu wajen mu je mu yi waꞌazi.

An gaya mana cewa mu wuce ƙasar Bulgeriya daga inda muke, kada mu koma ƙasar Yuganda. Don haka, ba mu koma mun tattara kayanmu ko mu yi wa ꞌyanꞌuwa ban kwana a Yuganda ba. Maimakon haka, mun wuce reshen ofishinmu da ke Jamus muka ɗauki mota, muka kama hanya zuwa Bulgeriya. An tura mu hidima a wani rukuni da ke da masu shela 20 a Sofiya.

Mun yi fama da sabbin ƙalubale a Bulgeriya. Da farko, ba mu iya yaren da ake yi a wurin ba. Ƙari ga haka, littattafanmu da ake da su a yaren Bulgeriya su ne, The Truth That Leads to Eternal Life, wato, Gaskiya Mai-bishe Zuwa Rai Madawwami da kuma My Book of Bible Stories, wato, Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki. Kuma ya yi mana wuya mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Duk da haka, mun ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo a rukuninmu kuma mun samu ci-gaba. Amma membobin cocin Orthodox na Bulgeriya ba su so waꞌazinmu ba, kuma sun soma tsananta mana.

A 1994, gwamnatin Bulgeriya ta sauƙe rajistar da ta yi mana. Kuma mutane da yawa suna ganin cewa mu wani rukuni ne mai haɗari sosai. An kama wasu ꞌyanꞌuwanmu. Kuma ƙaffofin yaɗa labarai sun yaɗa ƙarya cewa Shaidun Jehobah suna kashe yara, kuma suna sa membobinsu su kashe kansu. Hakan ya sa yin waꞌazi ya yi wa ni da maigidana wuya. Idan mun je waꞌazi, muna haɗuwa da mutanen da suke mana koran kare, wasu sukan kira mana ꞌyanꞌsanda, wasu kuma sukan jefe mu da wasu abubuwa. Ba a iya turo mana littattafai, kuma samun wurin yin taro yana da wuya sosai. A wani lokaci saꞌad da muke taron yanki, ꞌyanꞌsanda sun zo sun ta da hayaniya, kuma suka dakatar da taron. Ni da maigidana ba mu saba ganin irin wannan muguntar ba. Mutane a nan sun yi dabam sosai da mutanen da ke Yuganda! Domin a can suna son yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma duk da abubuwan nan da suka faru, mun ci-gaba da yin farin ciki. Me ya taimaka mana?

Kasancewa tare da ꞌyanꞌuwa maza da mata da ke wurin ya taimaka mana sosai. Sun so gaskiyar da suka koya kuma suna jin daɗi cewa muna tare da su. Mun ci-gaba da kula da kuma taimaka wa juna. Ni da maigidana mun koyi cewa, za mu iya kasancewa da farin ciki a kowane aikin da aka ba mu, idan muka fi mai da hankali ga mutanen da ke wurin maimakon matsalolin da muke fama da su.

Marianne da Heinz Wertholz.

Ni da maigidana a reshen ofishinmu da ke Bulgeriya, a 2007

Bayan wasu shekaru, abubuwa sun yi sauƙi. Gwamnati ta sake yi wa ƙungiyarmu rajista a 1998, kuma an fassara littattafai da yawa zuwa yaren Bulgeriya. Saꞌan nan a 2004, an gina kuma an keɓe mana sabon reshen ofishi. A yau, akwai ikilisiyoyi 57 da ke da masu shela 2,953 a Bulgeriya. A rahoton shekara-shekara na 2024, mutane 6,475 ne suka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. A dā, ꞌyanꞌuwa mata biyar ne kawai a Sofiya, amma yanzu akwai ikilisiyoyi tara! A gaskiya, mun ga cikar annabcin da Ishaya ya yi cewa, “mafi ƙanƙanta a cikinki kuma zai zama alꞌumma mai” yawa.—Isha. 60:22.

FAMA DA RASHIN LAFIYA

Na yi fama da rashin lafiya dabam-dabam a rayuwata. Sau da yawa likitoci sun gano cewa wasu abubuwa sun kumbura a jikina har ma a ƙwaƙwalwata. An yi min jinya mai zafi da zai shanye wasu kumburin. Kuma wani likita a ƙasar Indiya ya yi mini tiyata na tsawon awa 12 don ya cire wanda yake kaina. Bayan tiyatar, mun ɗan zauna a reshen ofishi da ke Indiya don in samu sauƙi. Daga baya, sai muka koma Bulgeriya.

Ana nan, sai maigidana ya soma fama da wata cuta da ake kira Huntingtonꞌs disease. Cutar ta sa yana yi masa wuya ya yi tafiya da magana, kuma gaɓoɓin jikinsa suna rawa. A kwana a tashi, jikinsa sai ƙara tsanani yake yi, kuma ya bukaci in taimaka masa sosai. A wasu lokuta nakan gaji sosai, kuma in yi ta damuwa cewa wataƙila ba zan iya ci-gaba da kula da shi ba. Amma wani ɗanꞌuwa matashi mai suna Bobi yana yawan zuwa gidanmu don su je waꞌazi tare. Bobi bai damu da abin da mutane za su faɗa ba idan suka ga yadda maigidana ba ya iya magana da kyau, da kuma yadda gaɓoɓin jikinsa suke rawa. Bobi yana taimaka mini a duk lokacin da na gaji. Duk da cewa ba mu haifi yara ba don mu iya faɗaɗa hidimarmu ga Jehobah, Jehobah ya ba mu Bobi a matsayin ɗa!—Mar. 10:​29, 30.

Ban da haka ma, maigidana ya yi fama da cutar kansa. Kuma a 2015, maigidana da nake ƙauna ya rasu. Na yi kewar mijina sosai. A kullum kamar mafarki ne nake yi. Ina yawan tunani game da shi, kuma ina ganin kamar bai mutu ba! (Luk. 20:38) A koyaushe, ina yawan tuna da shawarwari masu kyau da ya ba ni, da yadda yake min magana da alheri. Ina matukar farin ciki don yadda muka yi shekaru muna bauta wa Jehobah tare.

INA GODIYA GA JEHOBAH DON TAIMAKONSA

Jehobah ya taimaka mini in jimre ƙalubale dabam-dabam da na fuskanta. Ya taimaka mini in shawo kan kunyar da nake ji. Kuma in zama mai waꞌazi a ƙasar waje da ke ƙaunar mutane. (2 Tim. 1:7) Da taimakon Jehobah, ni da ƙanwata muna hidima ta cikakken lokaci a yanzu. Ita da maigidanta suna kula da daꞌirar da ake yaren Sabiya a Turai. Jehobah ya amsa adduꞌar da mahaifinmu ya yi lokacin da muke yara!

Yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana kwantar mini da hankali. A duk lokacin da nake cikin matsala, nakan ƙara “nacewa cikin” adduꞌa kamar yadda Yesu ya yi. (Luk. 22:44) Hanya ɗaya da Jehobah yake amsa adduꞌata ita ce ta wurin ’yan’uwa da ke ikilisiyarmu a Sofiya. Suna ƙauna ta, da kuma nuna mini alheri. Suna yawan gayyata ta in kasance tare da su, kuma suna gaya mini cewa suna alfahari da ni. Hakan yana sa ni farin ciki sosai.

Ina yawan tunani game da lokacin da za a yi tashin matattu. A zuciyata, ina ganin dukan ꞌyanꞌgidanmu a cikin aljanna. Ga iyayena suna tsaye a bakin kofar gidanmu. Suna nan a ƙuruciyarsu kamar yadda suke lokacin da suka yi aure. Ga ꞌyarꞌuwata tana dafa abinci. Ga maigidana kuma yana tsaye kusa da dokinsa. Yin irin wannan tunanin yana sa ni farin ciki sosai, kuma yana taimaka mini in jimre. A gaskiya, ina gode wa Jehobah sosai don wannan begen.

Idan na yi tunani a kan dukan abubuwa masu kyau da Jehobah ya ba ni, da kuma waɗanda zai ba ni a nan gaba, nakan ji kamar yadda Dauda ya ji a Zabura 27:​13, 14. A wurin Dauda ya ce: “Na tabbatar da wannan, zan ɗanɗana alherin Yahweh, a wannan duniyar masu rai. Sa zuciya ga Yahweh, ka ƙarfafa, ka kasance da ƙarfin zuciya! I, sa zuciya ga Yahweh!”

a Ka duba Awake! na 22 ga Disamba 2000, shafi na 20-24 don ka ga labarin Tatjana Vileyska.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba