Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Agusta pp. 20-25
  • Za Ka Iya Guje wa Shaꞌawoyi Marasa Kyau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Guje wa Shaꞌawoyi Marasa Kyau
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • IRIN TUNANIN DA SHAIƊAN YAKE SO MU YI
  • YADDA MUKE JI DON MU AJIZAI NE
  • ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKA MAKA KA YI NASARA
  • “MU CI-GABA DA BINCIKA KANMU”
  • Ka Yi Tsaro don Kada Ka Fadi Cikin Jarraba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Ci-gaba da Bin Yesu Bayan Ka Yi Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Abin da Jehobah Ya Yi don Ya Cece Mu Daga Zunubi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Agusta pp. 20-25

TALIFIN NAZARI NA 35

WAƘA TA 121 Mu Riƙa Kame Kanmu

Za Ka Iya Guje wa Shaꞌawoyi Marasa Kyau

“Kada ku yarda zunubi ya yi mulki a cikin jikin nan naku mai mutuwa, har ya sa ku ku bi muguwar shaꞌawarsa.”—ROM. 6:12.

ABIN DA ZA MU KOYA

Wannan talifin zai taimaka mana (1) kada mu karaya idan tunani marar kyau ya shiga zuciyar mu, da kuma (2) yadda za mu guje masa.

1. Mene ne dukanmu muke fama da shi?

KA TAƁA yin shaꞌawar yin abin da Jehobah ba ya so? Idan haka ne, kada ka karaya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa mutum ba.” (1 Kor. 10:13) Hakan yana nufin cewa kowace irin shaꞌawa marar kyau da kake fama da ita, wasu ma suna fama da hakan. Amma kar ka damu, Jehobah yana tare da kai, da taimakonsa za ka yi nasara.

2. Waɗanne irin jarrabobi ne wasu ꞌyanꞌuwa da kuma wasu ɗalibanmu suke fama da su. (Ka kuma duba hotunan.)

2 Littafi Mai Tsarki ya kuma ce: “Kowane mutum dai yakan sami jarraba saꞌad da mugun kwaɗayinsa ya ruɗe shi, ya kuma sha kansa.” (Yak. 1:14) Kowane mutum yana da abin da zai iya jarrabtar sa. Wasu Kiristoci za su iya yin fama da jarrabar yin lalata tsakanin mace da namiji, ko luwaɗi, ko maɗigo. Wasu kuma da suka daina kallon hotuna ko bidiyoyin batsa za su iya yin fama da jarrabar komawa gidan jiya. Wasu kuma da suka daina buguwa da giya da kuma shan miyagun kwayoyi, su ma suna fama da jarrabar sake komawa. Kaɗan ke nan cikin shaꞌawoyi marasa kyau da wasu ꞌyanꞌuwa da kuma wasu ɗalibanmu suke fama da su. A wasu lokuta, mukan ji kamar yadda manzo Bulus ya ji saꞌad da ya ce: “Idan ina so in yi nagarta, sai in ga mugunta tare da ni.”—Rom. 7:21.

Za mu iya fuskantar jarraba a koꞌina, kuma a kowane lokaci (Ka duba sakin layi na 2)c


3. Idan kana yawan fama da wata jarraba, wane irin tunani ne za ka iya yi?

3 Idan kana yawan fama da wata jarraba, za ka iya ganin kamar ba za ka iya shawo kanta ba, ko ka ga kamar Jehobah ba zai amince da kai ba. Idan haka ne kake ji, ka san cewa irin wannan tunanin ba daidai ba ne. Don mu ga dalilin da ya sa aka ce hakan, za mu tattauna tambayoyi guda biyu a talifin nan: (1) Waye ne yake so mu ga kamar ba za mu iya shawo kan wata jarraba ba, ko kuma mu ga kamar Jehobah ba zai amince da mu ba? (2) Ta yaya za mu shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau?

IRIN TUNANIN DA SHAIƊAN YAKE SO MU YI

4. (a) Me ya sa Shaiɗan yake so mu ga kamar ba za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau ba? (b) Me ya tabbatar mana cewa za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau?

4 Shaiɗan yana so mu ga kamar ba za mu iya shawo kan wata jarraba ba. Yesu ma ya san da hakan, shi ya sa ya gaya wa mabiyansa su yi adduꞌa cewa: “Kada ka kai mu cikin jarraba, amma ka cece mu daga mugun nan.” (Mat. 6:13) Shaiɗan ya ce ꞌyanꞌadam ba za su yi abin da Jehobah yake so ba idan aka jarrabce su. (Ayu. 2:​4, 5) Me ya sa Shaiɗan ya yi irin wannan ƙaryar? Shaiɗan ne halitta na farko da shaꞌawarsa ta sa shi ya yi abin da Jehobah ba ya so. Saboda haka, yana ganin kamar idan aka jarrabce mu, kamar shi, ba za mu riƙe amincinmu ga Jehobah ba. Shaiɗan ya ga kamar zai iya sa har Ɗan Allah marar zunubi ya faɗa cikin jarraba. (Mat. 4:​8, 9) Amma gaskiya ne cewa ba za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau ba? Ba gaskiya ba ne! Kamar yadda Manzo Bulus ya faɗa: ‘Muna da ƙarfin yin kome domin Allah yana ba mu ƙarfi.’—Filib. 4:​13, NWT.

5. Ta yaya muka san cewa Jehobah yana da tabbaci cewa za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau?

5 Jehobah ba kamar Shaiɗan ba ne. Jehobah yana da tabbaci cewa za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau. Ta yaya muka san hakan? Jehobah da kansa ya ce mutane da yawa za su riƙe amincinsu kuma za su tsira a lokacin ƙunci mai girma. Ka ɗan yi tunani a kan abin da hakan yake nufi. Jehobah ya ce mutane da yawa za su shiga sabuwar duniya “sanye da fararen riguna.” Hakan yana nufin cewa Jehobah yana ganin su a matsayin masu tsarki, kuma mun san cewa Jehobah ba ya ƙarya. (R. Yar. 7:​9, 13, 14) Saboda haka, Jehobah yana da tabbaci cewa za mu iya guje wa shaꞌawoyi marasa kyau.

6-7. Mene ne kuma Shaiɗan yake so mu gaskata?

6 Wani abu kuma da Shaiɗan yake so mu gaskata shi ne cewa, shaꞌawoyi marasa kyau da suke shiga zuciyarmu za su sa Jehobah ba zai amince da mu ba, kuma ba za mu sami rai na har abada ba. Ka ɗan sake yin tunani a kan dalilin da ya sa Shaiɗan yake so mu gaskata da wannan ƙaryar. Ya san cewa shi ne Jehobah ba zai taɓa amincewa da shi ba, ba zai samu rai na har abada ba, kuma za a halaka shi. (Far. 3:15; R. Yar. 20:10) Saboda haka, Shaiɗan yana kishin mu don ya san cewa muna da begen yin rayuwa har abada. Shi ya sa yake iya ƙoƙarinsa ya sa mu ga kamar ba mu da bege. Gaskiyar ita ce, yanayinmu ba ɗaya ba ne da na Shaiɗan. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Jehobah yana so ya taimaka mana mu iya yin rayuwa har abada. Domin “ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.”—2 Bit. 3:9.

7 Idan muna ganin kamar ba za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau ba, ko muna ganin ba za mu shiga aljanna ba don shaꞌawoyi marasa kyau da suke shiga zuciyar mu. Zai dace mu tuna cewa abin da Shaiɗan yake so ke nan. Sanin hakan, zai sa mu ƙudurta cewa ba za mu faɗa a tarkonsa ba.—1 Bit. 5:​8, 9. 

YADDA MUKE JI DON MU AJIZAI NE

8. Ban da aikata abubuwa marasa kyau, mene ne ake nufi da zunubi? (Zabura 51:5) (Ka kuma duba “Ma’anar Wasu Kalmomi.”)

8 Ban da Shaiɗan, akwai wani abu kuma da zai iya sa mu ji kamar ba za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau ba, ko kuma mu ga kamar Jehobah ba zai taɓa amincewa da mu ba. Me ke nan? Zunubin da muka gāda daga wajen iyayenmu na farko.a—Ayu. 14:4; karanta Zabura 51:5.

9-10. (a) Yaya Adamu da Hauwaꞌu suka ji bayan sun yi zunubi? (Ka kuma duba hoton.) (b) Yaya muke ji don zunubin da muka gāda?

9 Bari mu ga yadda Adamu da Hauwaꞌu suka ji saꞌad da suka yi zunubi. Bayan da suka yi wa Jehobah rashin biyayya sun ɓoye, kuma sun yi ƙoƙari su rufe jikinsu. Zunubin da suka yi ya sa sun ji kunya kuma hankalinsu ya tashi sosai. Ƙari ga haka, Adamu da Hauwaꞌu ba za su sake zama da dangantaka mai kyau da Jehobah ba. Kuma babu abin da za su yi da zai hana hankalinsu tashiwa ko kuma jin kunya, domin su masu zunubi ne.

10 Gaskiyar ita ce akwai ɗan bambanci tsakanin yanayin da muke ciki da na Adamu da Hauwaꞌu. Bambancin shi ne, Adamu da Hauwaꞌu ba su amfana daga fansar da Yesu ya bayar ba, amma mu mun amfana. Fansar ta sa ana iya gafarta mana zunubanmu kuma muna iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah. (1 Kor. 6:11) Duk da haka, mun gāji zunubi da kuma ajizanci. Saboda haka, mu ma hankalinmu yakan tashi kuma mu ji kunya. Littafi Mai Tsarki ya ce, zunubi ya shafi kowa da kowa har ma da ‘waɗanda zunubansu ba na karya doka ba ne kamar yadda na Adamu ya kasance.’ (Rom. 5:14) Amma ko da yake mun gāji zunubi, bai kamata mu yi tunani cewa ba za mu iya yin abin da ya dace ba, ko kuma ba za mu taɓa samun begen yin rayuwa a nan gaba ba. Mene ne zai taimaka mana mu guji irin tunanin nan?

Adamu da Hauwaꞌu cike da kunya suna fitowa daga lambun Adnin, sun sa kayan da aka yi da fatar dabba.

Zunubi ya tayar wa Adamu da Hauwaꞌu hankali sosai kuma sun ji kunya (Ka duba sakin layi na 9)


11. Idan muka ji wata murya tana gaya mana cewa ba za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau ba, me ya kamata mu yi kuma me ya sa? (Romawa 6:12)

11 Da yake mu ajizai ne, a wasu lokuta za mu ga kamar ba za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau ba. Za mu iya jin wata murya a zuciyarmu tana cewa, “ba za mu iya ba,” amma kada mu yarda da hakan. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu yarda zunubi ya yi “mulki” a kanmu. (Karanta Romawa 6:12.) Hakan yana nufin cewa idan muka yi shaꞌawar yin abin da bai dace ba, za mu iya zaɓan ko za mu yi ko aꞌa. (Gal. 5:16) Jehobah yana da tabbaci cewa za mu iya guje wa jarraba; shi ya sa ya ce mu yi hakan. (M. Sha. 30:​11-14; Rom. 6:6; 1 Tas. 4:3) Babu shakka, za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau.

12. Idan muna ganin kamar Jehobah ba zai amince da mu ba don shaꞌawoyi marasa kyau suna shiga zuciyarmu, me ya kamata mu yi kuma me ya sa?

12 Haka ma, idan muna ganin kamar Jehobah ba zai amince da mu ba don yadda shaꞌawoyi marasa kyau suke shiga zuciyarmu, mu tuna cewa zuciyarmu ce take ruɗin mu, kuma kada mu yarda da hakan. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya san mu ajizai ne. (Zab. 103:​13, 14) Ya san kome da kome game da mu, har da yadda zunubin da muka gāda yake shafan kowannenmu. (1 Yoh. 3:​19, 20) Idan ba mu bar shaꞌawoyi marasa kyau su shawo kanmu har mu aikata su ba, Jehobah zai amince da mu. Me ya tabbatar mana da hakan?

13-14. Idan shaꞌawoyi marasa kyau suka shiga zuciyar mutum, hakan yana nufin cewa Jehobah ba zai amince da shi ba? Ka bayyana.

13 Littafi Mai Tsarki ya nuna bambancin da ke tsakanin kasancewa da shaꞌawoyi marasa kyau da kuma aikata su. Ba za mu iya hana shaꞌawoyi marasa kyau shiga zukatanmu ba, amma za mu iya hana kanmu yin su. Alal misali, wasu Kiristoci a Korinti a ƙarni na farko ꞌyan luwaɗi ne a dā. Shi ya sa Bulus ya gaya musu cewa: “Haka waɗansunku ma suke dā.” Hakan yana nufin cewa shaꞌawar yin luwaɗi bai sake shiga zuciyarsu ba? Ba lallai ba, domin irin wannan halin yana da wuya mutum ya bari. Amma Jehobah ya amince da Kiristocin da suka kame kansu kuma suka guji aikata abin da suke shaꞌawar sa. Yana ganin su a matsayin waɗanda aka “tsabtace.” (1 Kor. 6:​9-11) Haka ma Jehobah yake ɗaukan ka.

14 Ko da wace irin shaꞌawa ce kake fama da ita, za ka iya shawo kanta. Ko da ba za ka iya hana shaꞌawar shiga zuciyarka ba, za ka iya kame kanka kuma ka guji yin “abin da jiki da zuciya suke zuga” ka ka yi. (Afis. 2:3) To, waɗanne abubuwa ne za su iya taimaka maka ka yi nasara?

ABUBUWAN DA ZA SU TAIMAKA MAKA KA YI NASARA

15. Idan kana so ka yi nasara wajen shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau, me ya sa bai kamata ka ruɗi kanka ba?

15 Idan kana so ka yi nasara wajen shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau, wajibi ne ka san abubuwan da za su iya tayar maka da irin waɗannan shaꞌawoyin. Kuma ka yi hankali don kada ka ruɗi kanka. (Yak. 1:22) Alal misali, wani mai shan giya da yawa zai iya ga kamar abin da yake yi ba laifi ba ne sosai, don yana ganin wasu ma suna sha fiye da shi. Ko kuma wani da ke kallon batsa zai iya ɗaura ma wasu laifi ya ce, ‘da a ce matata tana nuna mini ƙauna sosai, da ba zan yi shaꞌawar kallon batsa ba.’ Idan ka fara irin wannan tunanin, hakan zai sa ya yi maka sauƙi ka faɗa cikin jarraba. Saboda haka, ka guji ba da irin hujjojin nan. Domin idan ka yi abin da bai dace ba, laifinka ne.—Gal. 6:7.

16. Waɗanne abubuwa ne ya kamata mu yi da za su taimaka mana mu yi abin da ya dace?

16 Ban da sanin abubuwan da za su iya tayar mana da shaꞌawoyi marasa kyau, muna bukatar mu yanke shawara cewa ba za mu taɓa bari su shawo kanmu ba. (1 Kor. 9:​26, 27; 1 Tas. 4:4; 1 Bit. 1:​15, 16) Ka yi tunani a kan abin da yake sa shaꞌawoyi marasa kyau suke shiga zuciyarka, da kuma lokacin da hakan yake faruwa. Zai iya yiwuwa wani abin da kake yi ne, ko akwai lokaci a rana da hakan yake faruwa. Alal misali, yana yi maka wuya ka guje wa jarraba lokacin da ka gaji, ko kuma a tsakar dare? Ka yi shiri don ka san abin da za ka yi idan ka fuskanci jarraba. Zai dace ka yi hakan kafin ka fuskanci jarrabar. —K. Mag. 22:3.

17. Mene ne labarin Yusuf ya koya mana? (Farawa 39:​7-9) (Ka kuma duba hotunan.)

17 Ka yi laꞌakari da abin da Yusuf ya yi lokacin da matan Fotifar ta so ya kwana da ita. Ya ƙi abin da ta ce ba tare da ɓata lokaci ba. (Karanta Farawa 39:​7-9.) Mene ne hakan ya nuna? Yusuf ya riga ya yanke shawarar yin abin da ya dace kafin matar Fotifar ta yi ƙoƙarin rinjayar sa ya kwana da ita. Kai ma za ka iya yanke shawarar yin abin da ya dace kafin ka fuskanci jarrabar. Ta hakan, zai yi maka sauƙi ka yi abin da ka riga ka yanke shawarar za ka yi.

Hotuna: Na 1. Yusuf yana guduwa daga matar Fotifar, kuma tana riƙe da rigarsa a hannunta. Na 2. Wani ɗanꞌuwa matashi ya ƙi ya yarda ma wata ꞌyar makarantarsu da ta so su yi lalata.

Mu guji jarraba nan da nan kamar yadda Yusuf ya yi! (Ka duba sakin layi na 17)


“MU CI-GABA DA BINCIKA KANMU”

18. Wane abu ne kuma ya kamata mu yi don mu yi nasara a kan shaꞌawoyi marasa kyau? (2 Korintiyawa 13:5)

18 Idan muna so mu yi nasara wajen shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau, muna bukatar mu riƙa “gwada kanku,” wato mu ci-gaba da bincika kanmu don mu ga ko muna samun ci-gaba. (Karanta 2 Korintiyawa 13:5.) Zai dace mu riƙa yin laꞌakari da abubuwan da muke tunani a kai da abubuwan da muke yi, kuma mu yi gyara in da bukata. Alal misali, ko da ka guje wa wata jarraba, ya kamata ka tambayi kanka: ‘Har tsawon wane lokaci ne na ɗauka kafin in guje wa wannan jarrabar?’ Idan ba ka guje wa jarrabar nan da nan ba, kada ka damu. A maimakon haka, ka yi tunanin yadda za ka yi hakan nan da nan a nan gaba. Za ka iya tambayar kanka: ‘Idan shaꞌawoyi marasa kyau suka shiga zuciyata, zan iya guje wa tunanin ba tare da ɓata lokaci ba? Abubuwan da nake kallo ko karanta ko saurara suna sa guje wa jarraba ya yi min wuya? Ina saurin kawar da idanuna daga kallon abubuwan da ba su dace ba? Na fahimci cewa ƙaꞌidodin da Jehobah ya bayar don amfanina ne ko da hakan zai bukaci in ƙara kame kaina?’—Zab. 101:3.

19. Ta yaya ƙananan shawarwarin da muke yankewa za su iya sa ya yi mana wuya mu guje wa shaꞌawoyi marasa kyau?

19 Idan kana bincika kanka, kada ka yi ƙoƙarin kāre abubuwa marasa kyau da kake yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciyar mutum ta fi kome ruɗu, cike take kuma da mugunta ƙwarai.” (Irm. 17:9) Yesu ya ce, a zuciya ne “mugayen tunani suke fitowa.” (Mat. 15:19) Alal misali, mutumin da ya daina kallon hotunan batsa, bayan wani lokaci zai iya gani kamar kallon wasu irin hotuna “ba laifi ba ne” tun da mutanen ba tsirara suke ba. Ko kuma ya gani kamar ba laifi ba ne ya riƙa yin tunani a kan shaꞌawoyi marasa kyau idan har bai aikata su ba. Idan mutum yana irin wannan tunanin, yana nan kamar yana shirin aikatawa ne. (Rom. 13:14) Ta yaya za mu guji yin hakan? Mu lura kuma mu guji yanke ƙananan shawarwarin da za su iya sa mu yi abin da bai dace ba.b Mu guji irin tunanin da zai iya sa mu yi ƙoƙarin kāre kanmu idan muka yi abin da bai da kyau.

20. Me zai faru da shaꞌawoyi marasa kyau a nan gaba, kuma me zai taimaka mana a yanzu?

20 Kamar yadda muka gani, Jehobah zai iya taimaka mana mu guji faɗawa cikin jarraba. Kuma domin fansar da Yesu ya bayar, za a iya gafarta mana zunubanmu. Ƙari ga haka, muna da begen yin rayuwa har abada a cikin aljanna. Za mu yi farin ciki sosai idan muka sami damar bauta wa Jehobah ba tare da ƙoƙarin yin nasara a kan shaꞌawoyi marasa kyau ba! Kafin wannan lokacin, muna da tabbaci cewa za mu iya shawo kan shaꞌawoyi marasa kyau kuma Jehobah zai amince da mu. Da taimakon Jehobah, za mu yi nasara!

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne zai iya taimaka mana idan mun ga kamar ba za mu iya guje wa jarraba ba, ko kuma kamar Jehobah ba zai amince da mu don shaꞌawoyi marasa kyau da suke shiga zuciyarmu ba?

  • Ta yaya za mu guji barin zunubi ya yi mulki a kanmu?

  • Ta yaya za mu ci-gaba da “gwada” kanmu?

WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!

a MA’ANAR WASU KALMOMI: A Littafi Mai Tsarki, idan aka ce mutum ya yi “zunubi,” wani lokaci ana nufin ya yi abin da ba daidai ba kamar sata, zina, ko kuma kisa. (Fit. 20:​13-15; 1 Kor. 6:18) A wasu ayoyi kuma, ana nufin ajizanci ko zunubin da muka gāda daga wurin iyayenmu ko da ba mu yi wani abin da ba daidai ba.

b Ka lura cewa matashin da ke Karin Magana 7:​7-23 ya yanke wasu ƙananan shawarwari da ba su dace ba. Hakan ne ya kai shi ga yin lalata.

c BAYANI A KAN HOTUNA : Hagu: Saꞌad da wani ɗanꞌuwa yake zaune a wurin shan shayi, ya ga wasu maza biyu suna soyayya. Dama: Wata ꞌyarꞌuwa ta ga wasu mutane biyu suna shan taba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba