TARIHI
Jehobah Ya Koyar da Ni Tun Ina Ƙarami
WANI ɗanꞌuwa ya miƙa mini wata takarda. A takardar an rubuta cewa, “David Splane, 8 ga Afrilu, 1953: ‘Yin Waꞌazi Game da Armageddon.’” Sai na tambaye shi, “Mene ne wannan?” Sai ɗanꞌuwan ya ce, “Aikin da za ka yi ne a Makarantar Hidima ta Allah.”a Sai na gaya masa cewa, “Ai ban gaya wa kowa cewa ina so in yi aiki a makarantar ba!”
Amma kafin in yi nisa, bari in soma labarin daga farko. An haife ni a lokacin da ake yaƙin duniya na biyu a Calgary, da ke ƙasar Kanada. Wajen shekaru 75 da suka shige, wata majagaba na kullum mai suna Donald Fraser ta zo waꞌazi a gidanmu, kuma mahaifiyata ta yarda ta soma yin nazari. Abin da ta koya daga Littafi Mai Tsarki ya burge ta sosai. Amma ba ta zuwa taro kowane lokaci don tana fama da rashin lafiya mai tsanani. Duk da haka, ta yi ƙoƙari ta yi baftisma a 1950. Abin baƙin cikin shi ne, ta mutu shekara biyu bayan ta yi baftisma. A lokacin, mahaifina ba Mashaidi ba ne, amma ya yarda wani ɗanꞌuwa ya ba da jawabin janaꞌizar.
ꞌYan kwanaki bayan janaꞌizar, wata ꞌyarꞌuwa da ta tsufa mai suna Alice ta gayyace ni zuwa taro. Ta san ni ne domin takan gan ni tare da mahaifiyata a taron ƙarshen mako. Sai na tambayi mahaifina ko zan iya zuwa taron. Ya yarda, kuma ya ce zai bi ni sau ɗaya don ya je ya gai da ɗanꞌuwan da ya ba da jawabin janaꞌizar mahaifiyata. Da mahaifina ya halarci taron tsakiyar mako, ya ji daɗin taron sosai. Da yake mahaifina ya koyi yadda ake ba da jawabai a makaranta, ya ji daɗin yadda ꞌyanꞌuwan suka ba da jawabansu. Sai mahaifina ya yanke shawara cewa zai riƙa halartar taron kowane mako. Da shigewar lokaci, sai ya soma halartar sauran taron.
A lokacin, ɗanꞌuwan da ke kula da Makarantar Hidima ta Allah yakan soma taron da kiran sunayen dukan ꞌyanꞌuwa da suka ba da sunayensu don su yi aiki a makarantar ɗaya bayan ɗaya. Kuma duk wanda ya ji sunansa zai amsa. Wata rana, na gaya wa ɗanꞌuwan cewa zan so a kira sunana a taro na gaba. Ɗanꞌuwan ya yaba mini sosai. Amma bai gaya mini abin da yin hakan ya ƙunsa ba.
Ban san cewa yadda na ba da sunana, yana nufin cewa ina so in riƙa ba da jawabi a taro ba. Abin da nake so shi ne, a kira sunana kawai! A taro na gaba an kira sunana kuma na amsa. Bayan taron, ꞌyanꞌuwa sun yaba mini. Makonni bayan hakan, aka ba ni takardar da na ambata da farko da ke nuna aikin da zan yi a taro.
Na ji tsoro sosai! Domin a lokacin, irin wannan aikin yakan ɗau minti shida zuwa minti takwas. Kuma ba kawai karanta Littafi Mai Tsarki ba ne. Amma mahaifina ya taimaka mini in shirya aikin da aka ba ni, kuma ya sa in gwada yin jawabin har sau ashirin kafin ranar da zan ba da jawabin. Bayan da na gama jawabin, ɗanꞌuwan da ke kula da makarantar ya ba ni shawarwari masu kyau. Tun ina ƙarami, Jehobah ya yi amfani da mahaifina, da ꞌyanꞌuwa maza da mata a ikilisiya, da kuma ƙungiyarsa wajen koyar da ni.
JEHOBAH YA CI-GABA DA KOYAR DA NI
A lokacin da na soma fita waꞌazi, ꞌYarꞌuwa Alice da na ambata ɗazu ta taimaka mini in koyi yadda zan riƙa yi wa mutane waꞌazi. A lokacin an gaya mana cewa, idan muna so mu yi wa mutum waꞌazi, mu karanta masa nassosi uku, kuma mu ba shi littafi. Idan lokaci ya kai da ni ne zan yi wa mutum waꞌazi, ꞌYarꞌuwa Alice za ta gabatar da kanta, kuma ta soma yi wa mutumin waꞌazi. Saꞌan nan, za ta ce in karanta nassi na farko. Daga nan, sai in ci-gaba da yin waꞌazin, in karanta nassi na biyu da na uku kuma in ba da littafin. Daga baya, na koyi yadda zan riƙa soma yin waꞌazi da kaina. Bayan mahaifina ya yi baftisma a kusan ƙarshen shekara ta 1954, ya ci-gaba da taimaka mini in iya yin waꞌazi da kyau. Mahaifina ya yi ƙoƙari ya taimaka mini in ƙaunaci Jehobah. Ba ya wasa da halartan taro da kuma fita waꞌazi. Kowanne ƙarshen mako, na san cewa za mu halarci taro kuma mu fita waꞌazi.
A shekaru 12 da na yi a makarantar boko, na koyi abubuwa da yawa da suka taimaka mini a rayuwa. Alal misali, na koyi lissafi da kuma Turanci da kyau. Yadda ake yin Turanci da kuma rubuta labarai da na koya sun taimaka mini a hidimar da nake yi yanzu tare da Sashen Rubuce-rubuce.
A yawancin lokuta, mutane sukan tambaye ni abin da ya sa na cika son waƙa. Da nake tasowa, iyayena suna son waƙa sosai. A lokacin da nake shekara bakwai, an kai ni inda zan koyi buga kayan kiɗa. Amma malamata ta gaya wa mahaifina cewa, a ganinta ba zan iya koya ba. Ta gaya masa cewa zai fi kyau in daina ɓata lokacina. Na san abin da ya sa ta faɗi hakan. A lokacin ban damu da abin da ake koya mini ba.
Bayan ꞌyan watanni, mahaifina ya nemo mini wata malama kuma. A wannan karon, ba buga kayan kiɗi kawai na koya ba, har da yadda ake rera waƙa. Kuma na koyi yadda ake yin su da kyau. A lokacin da nake ɗan yaro, muryata tana da daɗin ji, kuma na ci wasu gasa da aka yi. Burina a lokacin shi ne in zama malamin da ke koyar da waƙa don in iya kula da kaina yayin da nake hidimar majagaba. Amma na gano cewa yin hakan zai ci lokacina sosai, domin ina bukatar in koyi abubuwa game da waƙa sosai kuma in shirya jarabawa da dama. Saboda haka, a 1963 na bar burina na zama malamin da ke koyar da waƙa, kuma na soma hidimar majagaba na kullum.
YIN HIDIMAR MAJAGABA NA SA MUTUM FARIN CIKI
Bayan na yi shekara ɗaya ina yin hidimar majagaba na kullum, an tura ni Kapuskasing a ƙasar Kanada a matsayin majagaba na musamman. Ɗanꞌuwa Daniel Skinner da aka tura mu hidimar tare ya girme ni sosai. Ya koya mini abubuwa da yawa game da yadda ake gudanar da ayyuka a ikilisiya. Saꞌad da nake shekara 20, na soma hidima a Kwamitin Hidima na Ikilisiya. Ina farin ciki cewa ƙungiyarmu ta soma nanata muhimmancin koyar da matasa. Idan sun yi iya ƙoƙarinsu, Jehobah zai yi amfani da su ko da ba su yi girma sosai ba!
A wasu lokuta, zama a Kapuskasing bai da sauƙi. Wuri ne da ake yin balaꞌin sanyi. Ni da Ɗanꞌuwa Dan muna yawan zuwa koꞌina tare. Amma daga baya, na haɗu da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Linda Cole da ta zama matata.
Linda tana da ƙwazo sosai a waꞌazi, kuma tana nazari da mutane da yawa. Tana bayarwa hannu sake, tana da kirki kuma tana son jamaꞌa. Mahaifiyarta mai suna Goldie ꞌyarꞌuwa ce mai aminci. Da farko, mahaifinta mai suna Allen ya tsani Shaidun Jehobah. Duk da cewa mahaifinta ya ci-gaba da tsananta wa mahaifiyarta, ba ta karaya ba. Ta ci-gaba da kai Linda da ƙanenta John da Gordon zuwa taro, kuma ta koya musu yadda za su riƙa yin waꞌazi. Akwai lokacin da Linda da John da Gordon da mahaifiyarsu suka yi hidimar majagaba. Bayan shekaru da yawa, mahaifinsu ya zama Mashaidi kuma ya yi aiki tuƙuru a ikilisiya.
A 1965, an gayyace ni in halarci makarantar dattawa da bayi masu hidima na wata ɗaya a Bethel da ke Kanada. A makarantar ne aka ce in cika fom na zuwa makarantar Gilead. Ban taɓa tsammani zan iya yin waꞌazi a ƙasashen waje ba. Amma na cika fom ɗin. Daga baya, an gayyace ni zuwa aji na 42. A makarantar, malamanmu sukan gaya mana wuraren da muke ƙoƙari, da kuma wuraren da muke bukatar gyara. Tun daga farko malamanmu sun gaya mini cewa in yi ƙoƙari in koyi yadda ake gudanar da ayyuka dabam-dabam a ƙungiyarmu. A lokacin shekaruna 21 ne. Abin da suka gaya mini ya taimaka mini sosai a rayuwa.
Wani abin da aka koya mana a Gilead shi ne yin magana a gidan rediyo da telibijin da kuma jaridu. Na ji daɗin abin da aka koya mana a wannan sashen sosai. A lokacin, ban san cewa zan yi amfani da abubuwan da na koya a nan gaba ba. Zan bayyana yadda suka taimaka mini a gaba.
HIDIMA A SENEGAL
ꞌYan kwanaki bayan mun sauke karatu, an tura ni da Ɗanꞌuwa Michael Höhle, yin hidima a ƙasar Senegal a Afrika. A lokacin, masu shela wajen 100 ne suke ƙasar gabaki ɗaya.
Bayan na yi watanni a hidimar, an ce in soma yin aiki na rana ɗaya a mako a reshen ofishinmu da ke ƙasar. Reshen ofishin wani ƙaramin ɗaki ne da ke gidan da masu waꞌazi a ƙasashen waje suke zama. Duk da cewa wurin ya yi ƙarami sosai, Ɗanꞌuwa Emmanuel Paterakis, wanda shi ne mai kula da ofishin Shaidun Jehobah a lokacin ya ci-gaba da tuna mini cewa, reshen ofishin ne ke wakiltar ƙungiyar Jehobah a ƙasar. Akwai ranar da Ɗanꞌuwa Emmanuel ya ce mu tura wa ꞌyanꞌuwa masu waꞌazi a ƙasashen waje a Senegal wasiƙar ƙarfafa. A lokacin, rubuta wasiƙu da keken rubutu wato typewriter bai da sauƙi kuma yana da tsada sosai. Ƙari ga haka, jan aiki ne domin muna bukatar mu tabbata cewa ba mu yi kuskure ba!
Da muka gama rubuta wasiƙun a ranar kuma ina shirin komawa gida, Ɗanꞌuwa Emmanuel Paterakis ya miƙa mini wata wasiƙa. Ya gaya mini cewa ƙungiyarmu ta rubuto mini wasiƙa. Da na buɗe wasiƙar, sai na ga cewa ɗaya daga cikin wasiƙun da muka rubuta ne. Wannan abin da ya faru ya koya mini cewa in riƙa daraja ƙungiyarmu ko da reshen ofishin ƙarami ne ko kuma babba.
Ni da wasu ꞌyanꞌuwa da suke waꞌazi a ƙasashen waje a Senegal a 1967
Na ƙulla abota da ꞌyanꞌuwa da yawa a ikilisiya, kuma ina yawan kasancewa da su ranar Asabar da yamma. Ba zan taɓa manta da lokacin nan ba! Har ila ina ji daga wurinsu. Saꞌad da nake Senegal, na koyi Faransanci kuma hakan ya taimaka mini yayin da nake zuwa ofisoshinmu da ke wurare dabam-dabam a duniya.
A 1968, ni da Linda mun yi wa juna alkawarin aure. Na yi watanni ina neman aiki don in ga ko ni da Linda za mu ci-gaba da zama a Senegal bayan mun yi aure. Amma an ƙi a ba ni aiki don ni ba ɗan ƙasa ba ne. A ƙarshe, na koma Kanada kuma muka yi aure. Sai aka ce mu soma hidima a matsayin majagaba na musamman a wani ƙaramin gari mai suna Edmundston, a New Brunswick, kusa da iyakar Quebec.
A ranar aurenmu a 1969
HIDIMA A NEW BRUNSWICK DA KUMA QUEBEC
Babu masu shela a Edmundston kuma ɗalibanmu kaɗan ne. Yawancin mutanen da ke garin ꞌyan Katolika ne kuma hakan yakan shafi kome da suke yi. Kusan kowane gida an rubuta cewa, ba ma son Shaidun Jehobah su shigo. A lokacin, ba ma damuwa da abin da suka rubuta. Don haka, muna shiga kowane gida. Kowane mako, cocin Katolika sukan rubuta a jarida cewa, mu je mu nemo Shaidun Jehobah kuma mu yi kacakaca da su. Mu huɗu ne Shaidun Jehobah a Edmundston, wato ni da matata Linda da Victor Norberg da matarsa Velda. Saboda haka, mun san cewa da mu ne suke yi!
Ba zan taɓa manta da karo na farko da mai kula da daꞌira ya ziyarce mu a wurin ba. Bayan ya yi mako ɗaya da mu ya gaya mana cewa: “Wani abu da nake ganin za ku iya yi saꞌad da kuke nan shi ne, ku taimaka wa mutane su canja raꞌayinsu game da Shaidun Jehobah.” Daga lokacin, abin da muka mai da hankali a kai ke nan, kuma haƙarmu ta cim ma ruwa! A sannu a hankali, mutane sun soma ganin bambancin da ke tsakanin Shaidun Jehobah da shugabannin Katolika masu girman kai. A yanzu, akwai ƙaramar ikilisiya a birnin.
Bayan mun yi wajen shekara ɗaya a Edmundston, sai aka ce mana mu je mu taimaka wa wata babbar ikilisiya da ke birnin Quebec. Bayan mun ji daɗin hidimarmu na wata shida a wurin, sai na zama mai kula da daꞌira.
Mun yi shekaru 14 muna hidimar mai kula da daꞌira a Quebec. Mun ji daɗin hidimar sosai a lokacin! Ana samun ci-gaba sosai a waꞌazin da ake yi a Quebec a lokacin. Kuma idan muka ziyarci ikilisiyoyi, muna yawan ganin iyalai da suke nazari kuma suna samun ci-gaba!
AKWAI ꞌYANꞌUWA MASU AMINCI DA BA ZA MU MANTA DA SU BA
Mun ji daɗin tarayya da ꞌyanꞌuwa da ke ɓangaren Kanada da ake Faransanci. ꞌYanꞌuwan nan ba sa ɗaukan abu da zafi-zafi, kuma su masu farin ciki ne. Amma ba a kowane lokaci ba ne yake yi musu sauƙi su soma bauta wa Jehobah domin danginsu sukan tsananta musu sosai. Wasu iyayen da ba Shaidu ba sukan gaya wa yaransu cewa, “Idan ba su daina yin nazari da Shaidun Jehobah ba za su kore su daga gida!” Duk da haka, yaran sun ci-gaba da riƙe amincinsu ga Jehobah. Babu shakka, Jehobah yana alfahari da su!
Zan kuma so in ambata wasu ꞌyanꞌuwa maza da mata masu aminci da suka yi hidimar majagaba na kullum da kuma majagaba na musamman a Quebec. Yawancinsu sun zo daga wasu wurare a Kanada. Saboda haka, suna bukatar su koyi Faransanci. Ban da haka ma, suna bukatar su fahimci alꞌadun mutanen, da yadda suke tunani domin yawancin mutanen ꞌyan Katolika ne, kuma hakan yakan shafi rayuwarsu gabaki ɗaya.
A yawancin lokuta, akan tura majagaba na musamman hidima a inda babu masu shela. Gidaje a wuraren na da tsada, kuma samunsu bai da sauƙi. Ƙari ga haka, samun ɗan aikin da mutum zai iya yi yana da wuya sosai domin mutanen ba sa son Shaidun Jehobah. A wasu lokuta, maꞌaurata sukan zauna da wasu ꞌyanꞌuwa a gida ɗaya. Sukan kai huɗu, shida ko takwas ko fiye da hakan don su iya biyan kuɗin haya. Waɗannan ꞌyanꞌuwan suna aiki tuƙuru. Idan sun soma nazari da wani, suna iya ƙoƙarinsu su taimaka masa. A yanzu, akwai masu shela da yawa a Quebec. Saboda haka, an tura ꞌyanꞌuwan zuwa wuraren da ake bukatar masu shela.
A duk lokacin da muka ziyarci ikilisiya saꞌad da muke hidimar mai kula da daꞌira, mukan yi ƙoƙari mu yi waꞌazi da matasa ran Asabar da safe. Hakan yakan ba mu dama mu san irin matsalolin da suke fama da su. A yanzu, wasu daga cikinsu suna waꞌazi a ƙasashen waje ko kuma wasu hidima dabam.
A lokacin, wasu ikilisiyoyi ba sa iya biyan bukatunmu na makon. Don haka a wasu lokuta, kuɗin da muke da shi yakan kasa mana kafin wata ya ƙare. A irin wannan lokacin, mukan dogara ga Jehobah domin shi kaɗai ne ya san irin yanayin da muke ciki. Jehobah bai taɓa barin mu ba. Yakan sa mu sami abin da muke bukata don mu ziyarci wata ikilisiya.
ABIN DA NA KOYA DAGA WURIN ꞌYANꞌUWA
Kamar yadda na ambata ɗazu, a Gilead an koya mana yadda za mu riƙa aiki da ƙafofin yaɗa labarai. Hakan ya taimaka mini sosai lokacin da nake Quebec. A lokacin, mun sami damar yin waꞌazi a gidajen rediyo da telibijin da kuma jaridu. A yawancin lokuta, akan ce in yi aiki tare da Ɗanꞌuwa Léonce Crépeault, wanda shi mai kula da daꞌira ne kuma ya ƙware a irin wannan aikin. Idan muka haɗu da manyan mutane da ke ƙafofin yaɗa labarai, ba ya nuna musu cewa ya san game da aikin sosai. A maimakon haka, yakan gaya musu cewa: “Mai girma, ni da abokina masu waꞌazi ne. Ba mu san yadda ake magana a telibijin ko a gidan rediyo ba. Amma ƙungiyarmu ta turo mu mu sanar wa jamaꞌa game da wani babban taron da Shaidun Jehobah suke so su yi. Za mu yi farin ciki idan kun taimaka mana.” Hakan ya sa ƙafofin yaɗa labarai da yawa sun taimaka mana.
Daga baya, an ce in soma aiki da Ɗanꞌuwa Glen How. Shi ɗaya ne daga cikin lauyoyinmu da suke aiki a kan batutuwa masu wuya da ƙafofin yaɗa labarai sukan yi magana a kai. Abin da na koya a Gilead da kuma yadda na yi aiki tare da Ɗanꞌuwa Léonce ya taimaka mini sosai. Ƙari ga haka, yin aiki da Ɗanꞌuwa How babban gata ne sosai. Ba ya tsoro idan ya je kotu kāre ƙungiyarmu. Mafi muhimmanci ma, shi mutum ne mai tsoron Allah.
A 1985, an tura mu hidimar mai kula da daꞌira a yammacin Kanada kusa da inda mahaifina yake zama, hakan ya ba mu dama mu iya kula da shi. Amma bayan wata uku, ya mutu. Mun ci-gaba da yin hidima a wurin har zuwa 1989 lokacin da aka gayyace mu yin hidima a Bethel da ke Amurka. Hakan ya ba mu mamaki sosai. Wannan yana nufin cewa za mu daina hidimar mai kula da daꞌira bayan mun yi shekaru 19 muna hidimar. A lokacin da muke hidimar mai kula da daꞌira, mun zauna a ɗarurruwan gidajen ꞌyanꞌuwa, kuma mun ci abinci dabam-dabam tare da su. Muna godiya sosai ga dukan ꞌyanꞌuwa da suka ba mu masauki kuma suka ciyar da mu!
MUN ƘAURA ZUWA AMURKA
Da muka soma hidima a Brooklyn, an ce in yi aiki a Sashen Kula da Hidima. Ba zan taɓa manta da abubuwan da na koya a wurin ba. Ɗaya daga cikin abubuwan da na koya shi ne, in riƙa tabbatar da gaskiyar batu kafin in ɗau mataki. A 1998, na soma aiki da Sashen Rubuce-Rubuce. Kuma har wa yau, ina kan koyan abubuwa a wurin. Na yi shekaru ina aiki tare da Ɗanꞌuwa John Barr, wanda shi ne ke kula da Sashen Rubuce-Rubuce a lokacin. Ba zan taɓa manta da abubuwan da na koya daga wurinsa ba. Shi ɗanꞌuwa ne da ya yi koyi da Yesu Kristi.
Ni da matata da Ɗanꞌuwa John Barr da matarsa Mildred
Ina farin ciki sosai yayin da nake aiki da ꞌyanꞌuwa maza da mata masu sauƙin kai a Sashen Rubuce-Rubuce. A kowane lokaci, sukan roƙi Jehobah ya taimaka musu a hidimarsu. Kuma sun san cewa, ruhu mai tsarki ne yake taimaka musu su cim ma duk wani abin da suka cim ma, ba baiwa ko hikimarsu ba.
Lokacin da nake yi wa mawaƙan Watchtower ja-goranci a taron shekara-shekara na 2009
Ina miƙa wa ꞌyanꞌuwa Littafi Mai Tsarki a taron ƙasashe da aka yi a Seoul, Koriya ta Kudu a 2014
Ni da matata mun sami gatan zuwa ƙasashe 110 inda ꞌyanꞌuwanmu suke. Mun ga yadda ꞌyanꞌuwanmu da suke hidima a ƙasashen waje, da mambobin Kwamitin da Ke Kula da Reshen Ofishinmu, da kuma wasu da ke hidima ta cikkaken lokaci suke ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu. Ban da haka ma, mun ga yadda ꞌyanꞌuwa a ƙasashen nan sun ci-gaba da riƙe amincinsu kuma suna bauta wa Jehobah da ƙwazo duk da cewa a wasu lokuta suna fama da yaƙi, da taɓarɓarewar tattalin arziki, da kuma tsanantawa. Babu shakka, Jehobah yana ƙaunar su sosai!
Matata ta yi shekaru tana taimaka mini in iya yin ayyukana da kyau. Tana da faraꞌa sosai kuma tana son taimaka wa mutane. Ƙari ga haka, ba ya mata wuya ta soma yi wa mutane magana. Ta taimaka wa mutane da yawa su soma bauta wa Jehobah har da waɗanda sun daina bauta masa. Ina alfahari da ita domin ita kyauta ce da Jehobah ya ba ni! Yanzu da muka tsufa, muna godiya sosai don yadda ꞌyanꞌuwa maza da mata matasa suke taimaka mana a hanyoyi dabam-dabam.—Mar. 10:29, 30.
Idan na yi tunani a kan abubuwan da suka faru a rayuwata shekaru tamanin da suka shige, nakan gode wa Jehobah. Raꞌayina ɗaya ne da mai zabura da ya ce: “Ya Allah, tun ina ƙarami, ka koya mini ayyukanka na ban mamaki, har wa yau kuma ina shelarsu.” (Zab. 71:17) Ina son in ci-gaba da yin hakan har iya rayuwata.
a A yau, ana yin irin wannan aikin a taron tsakiyar mako.