An Yi Nasara A Kamfen Na Musamman Da Aka Yi A Bulgeriya
“Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aiko ma’aikata cikin girbinsa.”—MAT. 9:37, 38.
WAƊANNAN kalaman Yesu sun yi daidai da yanayin da ke Bulgeriya, kyakkyawar ƙasa ta Balkan da ke kudu maso gabashin Turai! Da akwai bukatan ƙarin ma’aikata sosai don su yaɗa bishara ga fiye da mutane miliyan bakwai da ke zaune a ƙasar. Da akwai masu shela 1,700 a Bulgeriya, amma ba za su iya yin wa’azi a dukan yankin ba. Saboda haka, Hukumar Mulki ta amince ta gayyaci Shaidu ’yan ƙasar Bulgeriya daga ƙasashen Turai da yawa su zo su saka hannu a yin kamfen na musamman a shekara ta 2009. An tsara za a yi kamfen ɗin cikin makonni bakwai a lokacin rani, kuma a kammala a lokacin Taron Gunduma na “Ku Yi Tsaro” da aka yi a birnin Sofia, a ranar 14-16 na Agusta, 2009.
Amsa Mai Ban Mamaki
’Yan’uwan da ke ofishin reshe a Sofia suna tunanin ko mutane nawa ne daga Faransa, Jamus, Girka, Italiya, Poland, da Spain za su ba da kansu. Hakan na nufin cewa mutum zai biya kuɗin kansa zuwa Bulgeriya kuma ya ɗauki lokacin hutunsa don yin wa’azi. Abin farin ciki ne cewa adadin mutanen da suke son zuwa ya ci gaba da ƙaruwa har suka kai mutane 292! Tun da yake mutane da yawa sun ba da kansu, zai yiwu a aika waɗannan da suka ba da kansu zuwa birane uku dabam-dabam na Bulgeriya: Kazanlak, Sandanski, da Silistra. Masu kula da da’ira a Bulgeriya sun gayyaci majagaba na yankin da masu shela su ma su tallafa wa kamfen ɗin. A ƙarshe, mutane 382 da suka ba da kansu suna wa’azi da himma a yankunan da ba a yawan wa’azin bishara a cikinsu.
An aika da ’yan’uwa daga ikilisiyoyi na kusa su shirya masauki tun da wuri. Sun yi hayar gidaje da hotal marasa tsada. Waɗannan ’yan’uwa sun yi aiki tuƙuru don su taimaka wa masu zuwa su samu masauki kuma su kula da bukatunsu. A dukan birane uku, an yi hayar wuraren da za a yi taro. An yi shiri don ’yan’uwan da suka zo ziyara su gudanar da taron ikilisiya. Abin farin ciki ne a ga cewa masu shela 50 suna taro don yabon Jehobah a wuraren da babu ko Mashaidi ɗaya.
Waɗanda suka zo daga wasu ƙasashe don kamfen ɗin suna da himma sosai. A lokacin rani, ana zafi sosai a Bulgeriya. Amma, babu abin da zai hana waɗannan ’yan’uwa maza da mata masu himma yin wa’azi. An ba da shaida sosai a cikin makonni uku na farko a Silistra, birnin da ke Kogin Danube, da ke da mazauna fiye da 50,000. Saboda haka, ’yan’uwan sun yaɗa bishara zuwa ƙauyuka na kusa, har Tutrakan, ƙauyen da ke kilomita 55 a yammacin Silistra. Suna soma hidimarsu da ƙarfe tara da rabi na safe. Bayan hutun rana, sau da yawa suna ci gaba har ƙarfe 7 na dare, ko fiye da haka. Hakan nan ma, domin himma na waɗannan da suka ba da kansu, an yaɗa kamfen da aka yi a biranen Kazanlak da Sandanski zuwa ƙauyuka da birane na kusa.
Menene Aka Cim Ma?
An ba da shaida sosai a waɗannan makonni bakwai. Kamar yadda aka faɗa a zamanin manzanni, mazauna waɗannan birane sun ce, ‘kun gama biranenmu da koyarwarku.’ (A. M. 5:28) Shaidu da suka yi wannan wa’azin sun ba da mujallu 50,000 kuma sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane guda 482. Abin farin ciki, a ranar 1 ga Satumba ta shekara na 2009 an kafa ikilisiya a Silistra, kuma akwai rukunoni a Kazanlak da Sandanski. Abin farin ciki ne a ga mutane da suka ji bishara a lokaci na farko sa’ad da ake wannan kamfen suna samun ci gaba sosai a ruhaniya.
A mako na farko na kamfen ɗin, wata majagaba na musamman ’yar ƙasar Bulgeriya daga Spain ta yi wa Karina wa’azi, wata budurwa a Silistra da take sayar da jaridu a kan titi. Karina ta nuna tana son saƙon kuma ta halarci taro. Ta yarda a riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Mijinta mutumi ne da ya gaskata cewa ba Allah, saboda haka ta ce su yi nazarin Littafi Mai Tsarki a wurin da mutane suke hutu. An yi nazarin da ’ya’yanta mata biyu. ’Yarta ta fari, Daniela, tana son koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai. Ta karanta littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwar? cikin mako guda kuma nan da nan ta yi abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da kada a yi amfani da sifofi a bauta. Sai ta fara yi wa abokanta wa’azi. Bayan makonni uku kaɗai da ta halarci taronta na farko, ta gaya wa ’yar’uwar da take nazari da ita cewa: “Ina ji kamar na zama Mashaidiya. Menene zan yi don ni ma in soma wa’azi?” Daniela ta samu ci gaba sosai, tare da mamarta da ƙanwarta.
A Kazanlak, wani ɗan’uwa ɗan Bulgeriya mai suna Orlin, wanda ya zo daga Italiya don kamfen ɗin, yana kan hanyarsa ta komawa masaukinsa bayan wa’azi. A hanya, Orlin ya yi wa matasa maza biyu wa’azi da suke zama a kan benci a wurin da mutane suke hutawa. Ya ba su littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwar? kuma ya shirya zai koma musu ziyara washegari. A wannan ziyara, Orlin ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Svetomir kuma sun ci gaba washegari. A cikin kwanaki tara, Orlin ya yi nazari da Svetomir sau takwas. Svetomir ya ce: “Kwanaki biyu kafin in sadu da kai, na yi addu’a ga Allah ya taimake ni in san shi. Na yi alkawari cewa idan ya taimake ni, zan keɓe masa rayuwata.” Bayan da Orlin ya koma Italiya, ’yan’uwa da ke yankin sun ci gaba da nazari da Svetomir, kuma ya mai da gaskiya tasa.
Waɗanda Suka Yi Sadaukarwa Suna Samun Albarka Mai Yawa
Yaya waɗanda suka yi amfani da lokacin hutunsu kuma suka biya kuɗin kansu zuwa wata ƙasa don su yi wa’azin bishara suka ji? Wani dattijo da ke hidima a Spain ya rubuta: “Kamfen ɗin ya sa ’yan’uwa ’yan ƙasar Bulgeriya da ke Spain su kusaci juna. Ya shafi ’yan’uwa da suka sa hannu a wa’azin sosai.” Mata da miji daga Italiya sun rubuta: “Wannan shi ne wata mafi kyau a rayuwarmu!” Sun daɗa cewa: “Kamfen ɗin ya canja rayuwarmu! Yanzu mu mutane ne dabam.” Wannan ma’aurata sun soma tunani sosai game da ƙaura na dindindin zuwa Bulgeriya don su yi hidima inda ake da bukata mai girma. Carina majagaba ce na kullum da ba ta yi aure ba daga Spain da ta tallafa wa kamfen ɗin a Silistra. Bayan hakan ta bar aikin da take yi a Spain kuma ta ƙaura zuwa Bulgeriya don ta tallafa wa sabuwar ikilisiyar da ke wannan birni. Ta tara isashen kuɗi don ta zauna a Bulgeriya shekara guda. Carina ta ce game da shawararta: “Na yi farin ciki sosai da Jehobah ya ƙyale ni in yi hidima a Bulgeriya, kuma ina begen cewa zan kasance a nan na dogon lokaci. Yanzu ina gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki guda biyar, kuma uku a cikinsu suna halartan taro.”
Wata ’yar’uwa ’yar Italiya tana son ta sa hannu a kamfen ɗin, amma da yake ta soma sabon aiki, ba ta da kwanakin hutu. Duk da haka, ta ce a ba ta hutu na wata guda ba tare da biyan ta ba kuma tana shirye ta bar aikin idan ba a yarda ba. Ta yi mamaki da shugaban wurin aikinta ya ce: “To, amma da sharaɗi guda: Za ki aika mini katin gaisuwa daga Bulgeriya.” Babu shakka ’yar’uwar ta ga cewa Jehobah ya amsa addu’o’inta.
Stanislava, wata ’yar’uwa matashiya daga birnin Varna na Bulgeriya, tana aikin gwamnati na cikakken lokaci kuma tana karɓan albashi mai tsoka, ta ɗauki hutu don ta sa hannu a kamfen ɗin a Silistra. Ta zubar da hawaye na farin ciki, sa’ad da ta ga farin cikin majagaba da yawa da suka zo daga wurare masu nisa don su yi wa’azi a ƙasarsu. Ta soma tunani game da abin da take yi da rayuwarta, tana aikin neman kuɗi. Sa’ad da ta koma gida bayan makonni biyu, ta daina aiki kuma ta zama majagaba na kullum. Yanzu tana farin ciki sosai, tana tuna da Mahaliccinta a kwanakin ƙuruciyarta.—M. Wa. 12:1.
Albarka ne mutum ya kasance da ƙwazo a hidimar Jehobah. Abin da ya fi kyau da za ka yi shi ne ka ba da lokacinka da kuzarinka ga yin aiki mafi muhimmanci na koyarwa da wa’azin bishara. Akwai hanyoyi ne da za ka ƙara faɗaɗa wannan hidima mai ceton rai? Wataƙila akwai wurare a ƙasarku da ake da bukata mai girma. Za ka iya ƙaura zuwa irin wannan wurin? Ko kuma, kana iya yin tunanin koyon wani yare don ka taimaka wa mutane a ƙasarku da suke son su san koyarwar Littafi Mai Tsarki. Kowane gyara da ka yi don ka faɗaɗa hidimarka, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace ka sosai.—Mis. 10:22.
[Akwati/Hoton da ke shafi na 32]
Rana da Ba Za a Taɓa Mantawa Ba
Mutane da yawa da suka zo daga wasu ƙasashen Turai don su tallafa wa wannan kamfen na musamman a Bulgeriya sun yi shiri su halarci Taron Gunduma na “Ku Yi Tsaro” da aka yi a Sofia. Abin ƙarfafa ne ga ’yan’uwa maza da mata da ke wurin su sadu da baƙi masu yawa daga ƙasashe dabam-dabam. Mutane 2,039 da suka halarta sun yi farin ciki sosai sa’ad da Ɗan’uwa Geoffrey Jackson na Hukumar Mulki ya fito da cikakken New World Translation of the Holy Scriptures a yaren Bulgeriya. Dukan waɗanda suka halarta a ranar Jumma’ar sun nuna godiyarsu ta wurin yin tafi sosai na dogon lokaci. Har mutane da yawa suka zubar da hawaye na farin ciki. Wannan fassara mai kyau da yare mai sauƙin fahimta za ta taimaka wa mutanen Bulgeriya masu zuciyar kirki su san Jehobah.
[Taswira da ke shafi na 30, 31]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
BULGERIYA
SOFIA
Sandanski
Silistra
Kazanlak
[Hotuna da ke shafi na 31]
An ba da shaida na musamman a waɗannan makonni bakwai