Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Agusta p. 31
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Makamantan Littattafai
  • Mulkin Allah Ya Halaka Maƙiyansa
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Me Muka Sani Game da Yadda Jehobah Zai Shariꞌanta Mutane a Nan Gaba?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Armageddon Albishiri Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Ku Kasance da Aminci a Lokacin Kunci Mai Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Agusta p. 31

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

A wane lokaci ne za mu daina yin waꞌazi?

Yesu ya ce: “Wannan labari mai daɗi na Mulki, za a yi waꞌazin sa a dukan duniya domin ya zama shaida ga dukan alꞌummai, saꞌan nan ƙarshe zai zo.” (Mat. 24:14) Kalmar Helenanci da aka fassara zuwa “ƙarshe” a wannan ayar, da kuma ayoyi 6 da 13, ita ce teʹlos. Tana nufin lokacin da za a kawo ƙarshen duniyar Shaiɗan a Armageddon. (R. Yar 16:​14, 16) Saboda haka, za mu ci-gaba da yin waꞌazi har zuwa lokacin da ake dab da soma yaƙin Armageddon. Wannan bayanin ya canja yadda muka fahimci batun nan a dā.

A dā, mun ce za mu daina yin waꞌazi saꞌad da aka halaka Babila Babba kuma aka soma ƙunci mai girma. (R. Yar. 17:​3, 5, 15, 16) Mun ɗauka cewa, idan aka soma ƙunci mai girma Jehobah ba zai ba mutane dama su amince da waꞌazin da muke yi ba. (Isha. 61:2) Ƙari ga haka, mun ɗauka cewa mutane da za su tsira a lokacin ƙunci mai girma, su ne waɗanda suke bauta wa Jehobah da aminci kafin lokacin. Mun ce suna kama da Yahudawan da suka tsira lokacin da aka halaka Urushalima a shekara ta 607 K.H.Y. An sa musu alamar nuna cewa za su tsira, domin sun bauta wa Jehobah da aminci kuma sun tsane mugunta. (Ezek. 5:11; 9:4) Amma hakan bai jitu da abin da Yesu ya faɗa a Matiyu 24:14 ba. Ayar ta nuna cewa za a ba mutane dama su amince da waꞌazinmu har zuwa lokacin da ake dab da soma yaƙin Armageddon.

Wannan ƙarin haske da muka samu a kan Matiyu 24:14 ya sa muna bukatar mu gyara bayanin da muka yi a dā game da manyan ƙanƙara da ke Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 16:21. Binciken da mu ka yi sun nuna cewa ayoyi biyun nan suna da alaƙa. Me ya sa muka ce hakan? Abin da ya taimaka mana mu ga hakan shi ne abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da yadda mutane za su ƙi ko su yarda da waꞌazinmu. Bulus ya ce waꞌazinmu na kamar da “ƙanshi mai ba da rai,” ga waɗanda za su sami ceto. Amma ga maƙiyan Allah, “warin mutuwa ne.” (2 Kor. 2:​15, 16) Ba sa son waꞌazin Mulkin domin yana nuna cewa duniyar nan da suke ƙauna muguwa ce. Shaiɗan ne yake mulkin ta, kuma ba da daɗewa ba za a halaka ta.—Yoh. 7:7; 1 Yoh. 2:17; 5:19.

Wani abu kuma shi ne, manyan ƙanƙara da aka ambata a Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 16:21 suna da nauyi sosai. Saboda haka, mai yiwuwa a lokacin ƙunci mai girma, waꞌazinmu zai daɗa zama dalla-dalla, kuma mutane da yawa za su sami damar jin waꞌazin fiye da yadda yake a yanzu, hakan zai sa mutane da yawa su san game da Jehobah. (Ezek. 39:7) A wannan lokacin bayan an halaka Babila Babba, shin za a sami waɗanda za su so saƙonmu kamar yadda ake son turare mai ƙanshi? Ba mamaki za a samu. Mai yiwuwa za su tuna ko su ji cewa, Shaidun Jehobah sun yi shekaru da yawa suna waꞌazi cewa za a halaka Babila Babba, ga shi kuma suna ganin hakan da idanunsu.

Hakan yana kama da abin da ya faru a dā a ƙasar Masar, bayan annoba goma da suka yi fama da su. Saꞌad da Jehobah ya “hukunta dukan allolin Masar,” “mutane masu yawa” waɗanda su ba Israꞌilawa ba ne, sun bi Israꞌilawa. (Fit. 12:​12, 37, 38) Mai yiwuwa sun bi Israꞌilawan ne domin sun ga cewa duk abin da Musa ya faɗa game da annoba goman sun faru kamar yadda ya faɗa.

Saboda haka, duk wanda ya soma bauta wa Jehobah bayan an halaka Babila Babba, zai sami damar goyon bayan shafaffu da suka rage a duniya a lokacin. (Mat. 25:​34-36, 40) Amma wannan damar za ta zo ƙarshe ba da daɗewa ba kafin a soma yaƙin Armageddon, lokacin da sauran shafaffun da suka rage a duniya za su sami ladansu a sama.

Wannan ƙarin hasken ya nuna yawan ƙauna da jinƙan Jehobah. A gaskiya, “ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.”—2 Bit. 3:9.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba