Sabuwar Hanya Mai Ban Sha’awa na Yin Wa’azi ga Jama’a
1. Me aka ƙarfafa ikilisiyoyin da suke da wuraren da jama’a suke yawan wucewa a yankinsu su yi?
1 An ƙarfafa ikilisiyoyin da suke da wuraren da jama’a suke yawan wucewa a yankinsu su soma yin wa’azi ga jama’a ta wajen amfani da tebura ko amalanke ɗauke da littattafai. Idan sun yi amfani da amalanke, mai shela ɗaya zai iya tsaya ko zauna kusa da amalanken. Amma idan teburi ne, masu shela biyu su zauna ko tsaya kusa da shi. Masu shela da suke wannan hidimar su nuna fara’a. Idan wani ya ga abin da ya jawo hankalinsa a jikin littattafan, mai shela guda zai iya soma tattaunawa da shi, kuma zai iya ce: “Ka san abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a kan wannan batun?” Ban da waɗanda suke wurin teburin, mai shela ɗaya ko biyu za su iya tsayawa kusa da wurin suna tattaunawa da mutane.
2. Ku faɗi labarin da ya nuna muhimmancin yin wa’azi ga jama’a ta wajen yin amfani da amalanke ko teburi.
2 Wannan sabuwar hanyar wa’azi ta sa an soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa. Wata ’yar kwaleji ta so ta yi rubutu a kan Shaidun Jehobah amma ta kasa samun Majami’ar Mulki. Bayan mako guda, ta gano wurin da aka ajiye teburi ɗauke da littattafai a makarantarsu. Sai aka soma nazari da ita, kuma a yanzu haka, ta riga ta yi baftisma kuma tana ɗaya daga cikin waɗanda suke yin wa’azi ta wannan hanyar.
3. Yaya wasu masu shela suke ji game da wannan hanyar yin wa’azi ga jama’a?
3 Wata ’yar’uwa da ta ji daɗin yin wa’azi ta wannan hanyar ta ce: “Wasu suna tsayawa a wurin da aka ajiye littattafan don su karɓi sababbin mujallu. Wasu kuma ba su taɓa jin labarin Shaidun Jehobah ba. Lallai wannan hanyar tana sa a yi wa mutane dabam-dabam wa’azi.” Wata ’yar’uwa kuma ta ce: “Hakika, wannan sabuwar hanya mai ban sha’awa ce ta yin wa’azi domin mutane ne suke zuwa wurinka kuma ko da ba sa son saƙonmu, suna so su san abin da muke yi a wurin.”
4. Me ya sa ba zai dace mu riƙa canja wuraren da muke ajiye littattafai da kuma ranakun da muke ajiye su ba?
4 Kada a canja wuraren da ake ajiye waɗannan littattafan ko kuma ranakun da ake ajiye su. A sakamakon haka, mutane za su saba da ganin teburin ko amalanken kuma za su kasance da gaba gaɗin zuwa wurin don su yi tambaya ko kuma su karɓi littattafai. Ikilisiyarku ta soma wa’azi ga jama’a kuwa? Idan ta riga ta soma, kowannenku zai iya goyon bayan wannan sabuwar hanya mai ban sha’awa na yin ‘shelar Mulkin Allah.’—Luk. 9:60.