Yadda Za A Yi Wa’azi ta Wajen Yin Amfani da Tebura da Amalanke
Ana taimaka wa mutane masu tawali’u su san gaskiya ta wajen yin wa’azi ta hanyar tebura ko amalanke. (Yoh. 6:44) Saboda haka, an ƙarfafa dattawa su kafa tsarin yin wa’azi ga jama’a a yankin ikilisiyarsu, inda mutane suke yawan wucewa. Ba a bukatar a nemi izini daga wurin hukumomi kafin a ajiye tebura ko amalanke tun da ba a barinsu a wurin har washegari. Su waye ne suka cancanci su yi irin wannan wa’azi? Masu shelan da suka manyanta da suke ado da kyau kuma sun ƙware a yin magana. Ga wasu abubuwa da ya kamata masu shela su yi da kuma waɗanda bai kamata su yi ba don su yi nasara.