Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 7/13 pp. 4-6
  • Sababbin Hanyoyi na Yin Wa’azi a Inda Akwai Jama’a

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sababbin Hanyoyi na Yin Wa’azi a Inda Akwai Jama’a
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Sabuwar Hanya Mai Ban Sha’awa na Yin Wa’azi ga Jama’a
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Wa’azi a Kan Titi Mai Ba da Amfani
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ka Yi Amfani da Lokacinka a Hanya Mafi Inganci Sa’ad da Kake Wa’azi
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Yadda Za A Yi Wa’azi ta Wajen Yin Amfani da Tebura da Amalanke
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 7/13 pp. 4-6

Sababbin Hanyoyi na Yin Wa’azi a Inda Akwai Jama’a

1. Wane misali ne Kiristoci na farko suka kafa mana?

1 Kiristoci na ƙarni na farko sun yi wa’azi gida-gida da kuma duk inda suka sami jama’a. (A. M. 20:20) Alal misali, sun shiga cikin haikali don sun san cewa za su sami mutane da yawa a wurin. (A. M. 5:42) Sa’ad da manzo Bulus yake Atina, ya yi wa mutane wa’azi a kasuwa kullum. (A. M. 17:17) A yau, hanya ta musamman da muke yaɗa bishara ita ce wa’azi gida-gida. Amma, ban da yin wa’azi gida-gida, mukan yi wa’azi a tashoshi da wuraren kasuwanci da inda jama’a suke yawan bi da kuma wasu wurare da za a sami mutane. Ko da yake ana ƙarfafa kowane mai shela ya yi wa’azi a duk inda jama’a suke, wasu masu shela za su sami damar saka hannu a yin wa’azi a inda jama’a suke ta bin sababbin hanyoyi biyu nan.

2. Wane sabon tsari ne aka gwada a watan Nuwamba 2011?

2 Tsari na Musamman a Manyan Birane na Yin Wa’azi a Inda Jama’a Suke: A 2013 Yearbook, shafuffuka na 16 da 17, an ba da rahoto cewa an gwada wani sabon tsari na yin wa’azi a inda akwai jama’a a cikin New York City a watan Nuwamba, 2011. An saka littattafai masu kyan gani sosai a cikin amalanke da kuma tebura a wuraren da mutane da yawa suke wucewa. Kowace rana dubban mutane suna wucewa a wurin, waɗannan sun haɗa da mutanen da suke zama a manyan gidajen da ba a yarda Shaidun Jehobah su shiga da kuma mutanen da ba sa yawan zama a gida. Mutane da yawa sosai sun karɓi littattafanmu. A wani wata guda a kwanan nan, an ba wa mutane mujallu 3,797 da kuma littattafai 7,986. Mutane da yawa da suke wucewa sun ce a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Tun da yake dalilin da ya sa aka kafa wannan tsari saboda soma nazari da mutane ne, ana miƙa duk adireshin da mutanen suka bayar ga ikilisiyoyi da ke kusa da su nan da nan, don masu shela su kai musu ziyara a gidajensu.

3. Ta yaya za a faɗaɗa wannan tsarin wa’azi?

3 Tun da wannan tsarin ya yi nasara sosai, ana yunƙurin soma shi a wasu manyan birane da dama a faɗin duniya, inda akwai mutane da yawa sosai. Ofishin reshe da ke ƙasar ne zai zaɓi biranen da za a iya soma irin wannan wa’azin a wurin. Yawancin lokaci, waɗannan birane suna da tashoshin motoci da dama ko ofisoshi da yawa ko kuma manyan gidaje da ɗimbin jama’a suke zama a ciki. Bayan haka, Ofishin reshe da ke ƙasar zai aika saƙo ga ikilisiyar da aka ba ta damar yin wannan hidimar kuma ya ba da ja-gora a kan yadda za su yi hakan. Ana cika amfani da majagaba na kullum da na musamman, amma a wasu wurare, ana iya amfani da majagaba na ɗan lokaci.

4. Ta yaya ake yin wannan wa’azi a inda jama’a suke a manyan birane?

4 Yadda Ake Irin Wannan Wa’azin: Waɗanda suke saka hannu a wannan hanya ta musamman na yin wa’azi a inda jama’a suke a manyan birane sukan jira sai mutum ya zo ya same su a inda suke tsaye da littattafai a kan tebura ko amalanke. Idan wani ya zo kusa, sai su gaya masa ya ɗauki duk wani littafin da yake so. Idan yana da wasu tambayoyi, majagaban za su ba da amsa daga Littafi Mai Tsarki. Ba za su ambaci tsarin da ake bi na yin gudummawa ba idan ya ɗauki littafi. Amma idan ya tambaye su yadda ake samun kuɗin da ake aikinmu da shi, za su iya gaya masa cewa zai iya aika gudummawarsa zuwa ga adireshin da aka rubuta a cikin littafin. Idan da hali, za su iya tambayarsa: “Za ka so Shaidun Jehobah su ziyarce ka a gidanka?” ko kuma “Shin ka san cewa ana iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai a gidanka kyauta idan ka karɓi wannan littafin?”

5. Ta yaya wasu ma’aurata suka sami albarka daga bin wannan sabon tsari na yin wa’azi?

5 Saka hannu a wannan sabon tsarin yana da albarka sosai. Wasu ma’aurata sun rubuta cewa: “A duk lokacin da muke tsaye a gaban teburanmu kuma muna ganin dubban mutane suna wucewa a kullum, hakan yana tuna mana babban aikin wa’azi da muke yi a faɗin duniya. Ganin ɗimbin mutanen nan da kuma yin tunani a kan yadda Jehobah yake kula da kowannensu yana ƙarfafa mu mu saka yin wa’azi farko a rayuwarmu. Muna ji kamar Jehobah yana bincika zukatan mutane da suke wucewa a gaban teburan don ya gan waɗanda suka cancanci su ji bishara. Hakan yana sa mu ji kamar muna tare da abokan aikinmu, wato, mala’iku.”

6. (a) Wane sabon tsari na yin wa’azi a inda akwai jama’a ne ake shiryawa a ikilisiyoyi da yawa, kuma ta yaya ya bambanta da tsari na musamman na yin wa’azi a manyan birane? (b) Ta yaya ikilisiyoyi za su nuna haɗin kai sa’ad da suke wa’azi a inda jama’a suke?

6 Tsarin da Ake Bi a Ikilisiya na Yin Wa’azi a Inda Jama’a Suke: Ban da wannan tsari na musamman na yin wa’azi a inda jama’a suke a manyan birane, akwai wani sabon tsari da rukunin dattawa da yawa suke bi a yankunansu. Da wannan sabon tsarin, masu shela suna saka littattafai a kan tebura ko amalanke kuma su tsaya a inda jama’a suke yawan wucewa a yankin ikilisiyarsu. Wannan tsarin ya bambanta da tsarin yin wa’azi na musamman a manyan birane, inda ofishin reshe yana zaɓan ’yan’uwa daga ikilisiyoyi da yawa don su yi wa’azi tare a inda jama’a suke yawan wucewa.—Duba akwatin nan, “Haɗin Kai Yana da Muhimmanci.”

7. Ta yaya dattawa za su shirya a yi wa’azi a inda jama’a suke a yankinsu, idan hakan zai yiwu?

7 Dattawa za su bincika ko akwai inda mutane da yawa suke yawan wucewa a yankinsu don su san ko zai yiwu a shirya irin wannan wa’azi. Wuraren da za a iya saka littattafai a kan tebura ko amalanke su ne, tashoshi da wuraren da jama’a suke taro, tituna da ɗimbin mutane suke wucewa, wuraren da akwai manyan shaguna, harabobin kwaleji ko jami’a, tashoshin jirgin sama da na ƙasa da kuma wuraren da ake bukukuwan cika shekara. Kasancewa da teburi a wuri ɗaya a ranaku da kuma lokaci ɗaya yana da amfani. An lura cewa saka tebura a inda akwai manyan shaguna da yawa ya fi dacewa, maimakon zama a gaban babban shago guda inda mutane sun cika mai da hankali ga abin da ya kawo su shagon ne kawai. Amma a wasu wurare kamar gefen hanyoyi da mutane da yawa suke wucewa sosai, zai dace a yi amfani da ƙaramin amalanke. Dattawa za su iya sauko da bayanai da aka saka a dandalinmu a kan yadda za a shirya hotunan Hasumiyar Tsaro da Awake! da kuma Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da za a saka a jikin amalanken ko teburan. An shirya waɗannan bayanan ne musamman don irin wannan tsarin wa’azi a inda jama’a suke yawan taruwa. Waɗanda aka zaɓa su yi irin wannan wa’azin za su bi tsari na musamman da aka shirya don yin wa’azi a manyan birane a inda jama’a suke kuma ya kamata su bi umurnin da mai kula da hidima ya ba su da kyau. Idan suka karɓi adireshin wani da ke son saƙon Littafi Mai Tsarki amma ba ya zama a yankin, su cika fom ɗin Please Follow Up (S-43) ba tare da ɓata lokaci ba kuma su miƙa wa sakataren ikilisiyarsu.

8. Idan ikilisiyarku ba ta da wani tsari na yin wa’azi a inda akwai jama’a, ta yaya za ku iya yin wa’azi a inda akwai jama’a a yankinku?

8 Yin Wa’azi a Duk Inda Akwai Jama’a: Wasu ikilisiyoyi ba su da wurare da jama’a suke wucewa sosai a yankunansu kuma saboda haka, ba za su iya yin amfani da tebura ko amalanke don yin wa’azi ba. Duk da haka, ana ƙarfafa masu shela a waɗannan ikilisiyoyin su bincika ko zai yiwu su riƙa yin wa’azi a duk inda akwai jama’a. Za ku iya yin wa’azi a kasuwa ko inda aka jera shaguna, ko wani babban shagon da mutane da yawa suke zuwa ko tasha ko kuma inda mutane suke taro. Za ku iya yin hakan kuma sa’ad da ake yin wani biki ko wasu abubuwa makamantan haka a yankinku.

9. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga yin wa’azi a duk inda muka sami mutane?

9 Nufin Jehobah ne cewa “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) Shi ya sa muna ƙoƙarin yi wa mutane da yawa wa’azi game da Mulkin Allah kafin ƙarshen ya zo. (Mat. 24:14) A wurare da yawa, samun mutane a gida yana da wuya. Amma za mu iya samunsu sa’ad da suke cikin jama’a. Ta yin wa’azi a inda jama’a suke ne kawai wataƙila wasu za su sami damar jin bishara. Saboda haka, bari mu ba da kanmu sosai ga yin wa’azi a duk inda muka sami mutane.—2 Tim. 4:5.

[Akwati a shafi na 5]

Haɗin Kai Yana da Muhimmanci

A wasu lokatai, masu shela daga ikilisiyoyin da ke kusa da juna suna wa’azi a inda akwai jama’a a kan titi ɗaya ko a tashar mota ɗaya ko kuma a wurin kasuwanci ɗaya. ’Yan’uwa daga wata ikilisiya dabam sun taɓa zuwa tasha ɗaya da wurin kasuwanci ɗaya da kuma asibiti ɗaya don yin wa’azi kuma suka ba da mujallu a wurin bayan ikilisiya da ke da yankin ta riga ta yi wa’azi a wurin. Hakan ya ɓata wa mutane masu kasuwancin da waɗanda ke tashar da kuma asibitin rai, ko da masu shelan ba su zo a lokaci ɗaya ba. Saboda da haka, a duk lokacin da kuke so ku yi wa’azi ga jama’a, ku yi hakan a yankin da aka ba ikilisiyarku kawai.

Idan masu shela suna so su yi wa’azi ga jama’a a yankin wata ikilisiya da ke kusa, ya kamata su gaya wa mai kula da hidima na ikilisiyarsu. Da haka, zai tattauna da mai kula da hidima na waccan ikilisiyar don ya nemi izini kafin masu shela da ke ikilisiyarsa su yi hakan. Idan ikilisiyoyi da ke wani yare suna wa’azi a yanki ɗaya da wata ikilisiya, zai dace masu kula da hidima na waɗannan ikilisiyoyin sun riƙa tuntuɓar juna don kada a ɓata ran mutanen da ke zama a unguwar saboda yawan wa’azi da ake yi a wurin. Da haɗin kai, za a iya yin abubuwa a “hankali bisa ga ƙa’ida kuma.”—1 Kor. 14:40.

[Hoto a shafi na 6]

[Hoto a shafi na 6]

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba