Ka Yi Amfani da Lokacinka a Hanya Mafi Inganci Sa’ad da Kake Wa’azi
Daga watan Satumba na 2013 zuwa Agusta na 2014, Shaidun Jehobah sun yi awa 1,945,487,604 suna wa’azi, kuma hakan ya nuna cewa muna shirye mu ci gaba da yi wa Jehobah hidima da ƙwazo. (Zab. 110:3; 1 Kor. 15:58) Tun da yake “lokacin da aka ƙayyade ya ƙure,” shin zai yiwu mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi amfani da lokacinmu wajen yi wa mutane da yawa wa’azi?—1 Kor. 7:29, LMT.
Yin amfani da lokacinmu a hanya mafi inganci a wa’azi yana bukatar yin amfani da dabaru dabam-dabam. Idan kana yawan yin awa ɗaya ko fiye da hakan a wani fanni na wa’azi ba tare da yin magana da wani ba, zai dace ka yi gyara ga tsarinka don ka iya samun mutane da yawa ka tattauna da su. A wurare dabam-dabam, yanayi yakan bambanta. Amma shawarwarin da ke gaba za su taimaka maka ka yi amfani da lokacinka a hanya mafi inganci don kada ka riƙa “naushin” iska.—1 Kor. 9:26.
Yin Wa’azi Gida-gida: Masu shela sun yi shekaru da yawa suna wa’azi gida-gida da safe, bayan haka, sai su koma ziyara. Amma da yake mutane da yawa suna aiki da safe, zai fi dacewa mu jira sai da rana ko yamma a lokacin da suka dawo gida kuma suka huta kafin mu fita wa’azi gida-gida. Za mu iya yin wa’azi a kan titi ko kuma a wuraren kasuwanci da safe ko da rana.
Yin Wa’azi ga Jama’a: A ajiye tebura ko amalanke a wuraren da mutane ke yawan wucewa a yankin ikilisiyar. (Ka duba Hidimarmu ta Mulki ta Yuli 2013, shafi na 5.) Idan mutane sun rage bin inda ake ajiye tebura ko amalanke, Kwamitin Hidima na Ikilisiya ɗin zai iya yanke shawarar canja wurin da ake ajiye teburan da amalanken zuwa inda mutane suke yawan wucewa.
Koma Ziyara da Nazarin Littafi Mai Tsarki: Shin zai yiwu ka koma ziyara a lokacin da ba a yawan samun mutane a wasu fannonin wa’azi ba? Alal misali, idan ana samun mutane sosai sa’ad da ake wa’azi gida-gida a ranar Asabar da safe, za ka iya shirya ka yi nazari da ɗalibanka da rana ko da yamma. Idan mu da wanda muke wa’azi tare muna komawa ziyara, za mu iya shirya mu ziyarce ɗalibanmu da suke unguwa ɗaya. Hakan zai sa mu sami mutane da yawa.
Gaskiya ne cewa muna jin daɗin ba da rahoton awoyi a duk lokacin da muka fita wa’azi, amma za mu fi yin farin ciki idan muka sami sakamako mai kyau. Idan ka ga cewa yin wani fanni na wa’azi a wani lokaci ba zai kawo sakamako mai kyau ba, sai ka canja zuwa wani fanni dabam. Ka yi addu’a ga Jehobah “Ubangijin girbi” don ya ja-gorance ka ka yi amfani da lokacinka a hanya mafi inganci sa’ad da kake wa’azi.—Mat. 9:38.