Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 8/11 p. 6
  • Ku Yi Amfani da Ita a Kowane Lokaci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Amfani da Ita a Kowane Lokaci
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Ku Yi Amfani da Sabuwar Warƙar da Aka Wallafa don Dandalinmu
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Za Ka Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki da Wani a Watan Oktoba?
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 8/11 p. 6

Ku Yi Amfani da Ita a Kowane Lokaci

1. A waɗanne hanyoyi ne warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? za ta taimaka mana?

1 An wallafa warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? don ya yi mana sauƙi mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma kayan aiki ne mai kyau da zai taimaka wajen yaɗa irin gaskiya. (M. Wa. 11:6) Ga wasu shawarwarin da za su taimaka mana mu yi amfani da ita yadda ya dace.

2. Ta yaya za mu yi amfani da warƙar don soma tattaunawa?

2 Don Soma Tattaunawa: Za ku iya ba mai gida warƙar, sai ku nuna tambayoyi shida da ke gaban, kuma ku yi tambaya: “Wace cikin waɗannan tambayoyin ne ka taɓa yin tunani a kai?” Bayan ya ba da amsa, ku yi amfani da amsoshin Nassi da ke cikin warƙar don amsa tambaya guda da mai gidan ya yi kuma ku karanta nassi guda da aka ambata. Ka karanta ko kuma taƙaita shafi na baya, kuma ka ba da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ko ma bai karɓi littafin ba, amma ya karɓi warƙar kuma hakan zai sa gaskiya ta yi jijiya a cikin zuciyarsa.—Mat. 13:23.

3. Mene ne za ka iya yi, idan mai gida yana aiki?

3 Idan Mai Gidan Yana Aiki: Za ka iya cewa: “Tun da wannan lokacin bai dace ba, bari in ba ka wannan warƙar. Ta lissafa takamammun tambayoyi shida da yawancinmu muka taɓa yi kuma ta ba da amsa kai tsaye daga Littafi Mai Tsarki. Idan mun sake haɗuwa, zan so na san ra’ayinka.”

4. Mene ne za mu iya cewa sa’ad da muke ba da warƙar a kan titi?

4 Sa’ad da Kuke Yin Wa’azi a Kan Titi: Za ka iya ce: “Barka dai. Ka taɓa yin ɗaya cikin waɗannan tambayoyin kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan ya ba da amsa mai gamsarwa daga Littafi Mai Tsarki.” Idan mutumin ba ya sauri, za ka iya tattauna amsa guda daga warƙar kuma za ka iya ba da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

5. Ta yaya za mu iya yin amfani da warƙar nan a wasu lokatai idan babu kowa a gida?

5 Waɗanda ba Sa Gida: A wasu yankuna, masu shela suna yawan ajiye mujallu a ƙofar waɗanda ba sa gida. Idan hakan kuke yi a ikilisiyarku, zai dace ku riƙa ajiye warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? Sa’ad da ka koma ziyara za ka iya cewa: “Ranar da muka fara zuwa nan, ba mu tarar da kai a gida ba, shi ya sa muka ajiye wannan warƙar a ƙofarka. Wace cikin waɗannan tambayoyi ne za ka so a amsa maka?”

6. Me ya sa warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? kayan aiki ne mai kyau na yin wa’azi?

6 Warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? ta bayyana gaskiya a hanya mai sauƙi da kuma kai tsaye. Ya shafi mutane daga addini da kuma al’adu dabam-dabam. Yana da sauƙin gabatarwa, kuma ƙananan yara da kuma sababbin masu shela za su iya ba da ita. Kana amfani da ita a kowane yanayi kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba