Za Ka Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki da Wani a Watan Oktoba?
1. Waɗanne littattafai ne za a ba da a watan Oktoba?
1 Littattafan da za a ba da a watan Oktoba su ne mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Don mu iya koma ziyara, an ƙarfafa mu mu ba da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? kuma mu yi ƙoƙari mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wani. Yaya za mu iya yin hakan sa’ad da muka koma ziyara?
2. Yaya za mu iya yin amfani da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? don soma nazarin Littafi Mai Tsarki sa’ad da muka koma ziyara wurin wanda ya karɓi mujallu?
2 Yadda Za a Yi Amfani da Warƙar: Za mu iya ce: “Mujallun da na ba ka suna ƙarfafa mutane na kowanne al’adu da addinai su bincika Littafi Mai Tsarki. [Ka ba mai gidan warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?, sai ka nuna tambayoyin da suke gaban warƙar.] Ga wasu amsoshi masu gamsarwa da Littafi Mai Tsarki ya ba da ga tambayoyi masu muhimmanci. Ka taɓa yin ɗaya daga cikin waɗannan tambayoyin?” Bayan mai gidan ya ba da amsa, ku tattauna amsa ɗaya daga cikin tambayoyi da ya zaɓa da ke cikin warƙar, kuma ka karanta nassi ɗaya da aka yi ƙaulinsa. Sai ka bayyana cewa wannan misali ne na abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, sa’an nan ka ba shi littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Bayan hakan, za mu iya tattauna sakin layi na farko da ke babin da ya zaɓa daga cikin littafin. Za mu kuma iya buɗe inda aka tattauna abin da ke cikin warƙar a cikin Littafin. Ga wasu wuraren da za mu iya yin amfani da su:
● Allah yana kula da mu kuwa da gaske? (shafuffuka na 9-11, sakin layi na 6-10)
● Yaƙi da wahala za su taɓa ƙarewa kuwa? (shafi na 12, sakin layi na 12-13)
● Me ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu? (shafuffuka na 59-60, sakin layi na 7-8)
● Matattu suna da bege kuwa? (shafi na 71, sakin layi na 13-15)
● Ta yaya zan yi addu’a kuma Allah ya ji ni? (shafuffuka na 166-167, sakin layi na 5-8)
● Ta yaya zan iya samun farin ciki a rayuwa? (shafi na 9, sakin layi na 4-5)
3. Ta yaya za mu iya yin amfani da gabatarwa dabam dabam dangane da yanayin mai gida?
3 Idan yanayi bai ƙyale mu mu soma da kuma gwada yadda ake yin nazari da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ba a ziyara ta farko, za mu iya shirya mu koma mu ci gaba da tattaunawarmu. Kuma dangane da yadda mutumin yake son saƙon, za mu iya yanki shawarar tattauna tambaya fiye da ɗaya da ke cikin warƙar sau da yawa kafin mu gabatar da littafin. Bari mu yi amfani da wannan warƙar mai amfani a watan Oktoba don soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kuma mu taimaki masu zukatan kirki su “san gaskiya.”—Yoh. 8:31, 32.