Ku Yi Amfani da Sabuwar Warƙar da Aka Wallafa don Dandalinmu
Jigon wannan warƙar shi ne A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi? An yi tambayoyi uku a bayan warƙar. Idan kuka sami damar tattaunawa da wani, ku nuna masa warƙar kuma ku ce ya zaɓi tambayar da ya fi so, sa’an nan ya duba sashen KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > AN AMSA TAMBAYOYIN LITTAFI MAI TSARKI a Yanar gizo don ya sami amsar. A wannan sashen, zai sami amsoshin tambayoyi kamar haka: Mene ne Mulkin Allah? Kuma mene ne Mulkin Allah zai yi?
Ku riƙe wannan warƙar a jiki koyaushe don ku taimaki mutane su san koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan yadda rayuwarmu za ta zama a cikin Mulkin Allah.