Tsarin Ayyuka na Makon 29 ga Agusta
MAKON 29 GA AGUSTA
Waƙa ta 33 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl shafi na 47 zuwa 51 (minti 25)
□ Makarantar Hidima Ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Zabura 110-118 (minti 10)
Bitar Makarantar Hidima Ta Allah (minti 20)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 128
Minti 10: Sanarwa. Ka yi amfani da gabatarwa da ke shafi na 8 don gwada yadda za a iya soma nazari a Asabar ta fari na watan Satumba, kuma ka ƙarfafa kowa ya saka hannu. Ta hanyar jawabi, ka tattauna “Ku Ba Da Tsohuwar Mujalla ko Wata Ƙasida da ta Dace da Mai Gidan.”
Minti 15: Suna da Ƙwazo Ko da Yake Sun Tsufa. Tattaunawa da aka ɗauko daga 2011 Yearbook, shafi na 61, sakin layi na 1-2; shafi na 67, sakin layi na 1; da shafi na 135, sakin layi na 2, zuwa shafi na 136, sakin layi na 1. Ko kuma Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 1998, shafi na 32 da 15 ga Disamba, 2010, shafi na 25. Ka gayyaci masu sauraro su faɗi darussan da suka koya.
Minti 10: Ku Yi Shirin Gabatar da Mujallu a Watan Satumba. Tattaunawa. Ka yi amfani da minti ɗaya ko biyu don yin bitar abin da ke cikin mujallun. Sai ka zaɓi talifofi biyu ko uku, kuma ka gayyaci masu sauraro su faɗi tambayoyi da nassosi da za a iya amfani da su don gabatarwar. Ka gwada yadda za a iya gabatar da kowacce fitowa.
Waƙa ta 122 da Addu’a