Ka Kasance da Muradin Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki
1. Menene cika umurnin Yesu da ke Matta 28:19, 20 ya ƙunsa?
1 Yesu ya umurce mu mu ‘almajirtar da dukan al’ummai . . . , muna koya musu.’ (Mat. 28:19, 20) Saboda haka, muna son mu kasance da muradin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a kowane lokaci, ba kawai mako guda da aka keɓe don gabatar da nazarin Littafi Mai Tsarki ba. Shawarwarin da ke gaba za su iya taimakawa.
2. Ga wa za mu iya gabatar da nazarin Littafi Mai Tsarki?
2 Ka Gabatar da Shi: Yayin da muke gabatar da nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, za mu samu ƙarin zarafin soma nazari. (M. Wa. 11:6) Ka taɓa gwada gabatar da nazari a farkon ziyara? Wata ikilisiya a Amirka ta yi hakan a cikin wata ɗaya cir. Sun yi farin cikin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane arba’in da biyu! Kada ka yi tsammanin cewa masu marmari da ka ziyarta sun san cewa kana gabatar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ka sake komawa ziyara, zai dace ka gabatar da nazari. Babu wani laifi idan ba su amince ba. Za ka iya ci gaba da tattaunawa da su. Ka tambayi maƙwabta, danginka, abokan aiki, da abokan makaranta ko za su so ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuwa? Kana kuma iya tambayar ɗalibanka na Littafi Mai Tsarki ko suna da abokai ko ’yan’uwa da za su so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su.
3. Wane kayan aiki mai kyau na soma nazari ne muke da shi, kuma a wane lokaci ne za mu iya yin amfani da shi?
3 Kayan Aiki da Zai Taimaka: Wani abu mai tamani da za a iya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ita ce warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? Za ka iya ba masu gida ko da sun karɓi wasu littattafai ko a’a. Ana iya yin amfani da ita sa’ad da ake wa’azi a wuraren sana’a, a kan hanya, sa’ad da ake aika wasiƙu, da kuma sa’ad da aka koma ziyara. Za a kuma iya barinta a gidan da babu kowa. Zai dace ka ɗauki warƙar sa’ad da ka shiga motar haya, sa’ad da ka tafi yin sayayya a kasuwa, da kuma sa’ad da kake wurin aiki. Shafin ƙarshe na warƙar ya ɗan bayyana shirye-shiryenmu na yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
4. Ta yaya za mu iya yin amfani da warƙar nan Za Ka so ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin? don soma nazari?
4 Bayan ka miƙa wa wani warƙar, kana iya nuna masa tambayoyin da ke farkon shafin kuma ka tambaye shi, “Wannene ka fi so a cikin tambayoyin nan?” Sai ku tattauna amsar tare daga cikin warƙar, kuma ka karanta ko ka ɗan bayyana shafin ƙarshe na warƙar, wanda ya bayyana shirinmu na yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Bayan haka sai ka nuna masa inda ƙarin bayani game da wannan batun yake a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa, ka ba shi littafin, kuma ka yi shirin komawa don ci gaba da tattaunawar.
5. Me ya sa ya kamata mu kasance da muradin soma nazarin Littafi Mai Tsarki?
5 Har ila akwai waɗanda suke marmarin sanin ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa a yankinmu. Ta wajen kasancewa da muradin soma nazarin Littafi Mai Tsarki, za mu sami ƙarin zarafi na shaida farin cikin taimaka wa wasu su sami hanyar zuwa rai.—Mat. 7:13, 14.