Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 7/15 p. 1
  • Ku Mai da Hankali ga Almajirtar da Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Mai da Hankali ga Almajirtar da Mutane
  • Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance da Muradin Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Ka Taimaka wa Mutane Su Zama Almajiran Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ka Rika Koyar da Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Ku Je Ku Sa Mutane Su Zama Almajiraina
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2015
km 7/15 p. 1

Ku Mai da Hankali ga Almajirtar da Mutane

1. Mene ne muke bukata mu yi don mutane su tsira?

1 Rahoton shekara ta 2014 ya nuna ƙwazon da bayin Allah suke yi da kuma ƙudurinsu na yin wa’azin Mulki. (Mat. 24:14) Yin wa’azi gida-gida da rarraba warƙoƙi da takardun gayyata da kuma hanyoyi dabam-dabam na yin wa’azi ga jama’a yana ba mutane da yawa damar jin saƙonmu fiye da dā. Duk da haka, idan muna son mutane su tsira, ya kamata mu taimaka musu su zama almajiran Yesu ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su.—1 Tim. 2:4.

2. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu riƙa neman waɗanda za mu yi nazari da su?

2 Ku Riƙa Neman Zarafin Yin Nazari da Mutane: Idan wani ya nuna cewa yana son saƙonmu, zai dace ku karɓi adireshinsa don ku ziyarci shi nan da nan kuma ku soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Yaushe rabonka da yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wani a haɗuwarku ta farko? Yaushe rabonka da gwada yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutanen da kake ba su mujallunmu a kai a kai? Shin kun taɓa nuna wa abokan aikinku da abokan makarantarku da maƙwabtanku da danginku da kuma wasu bidiyoyin nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? da Yaya Ake Gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki? Sa’ad da kake wa’azi da amalanke ko teburi, shin kana gaya wa waɗanda suke ɗaukan littattafanmu cewa za a iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su kyauta?

3. Mene ne muke bukata mu yi idan muna so mu koyar da Kalmar Allah da kyau?

3 Taimako Daga Wurin Jehobah da Kuma Yesu: Sa’ad da Yesu ya umurci mabiyansa su yi wa’azi, ya fara da furucin nan “ku je,” kuma hakan ya nuna cewa muna bukatar mu ɗauki mataki kuma mu yi ƙwazo. Yesu bai bar mu haka ba, amma ya yi alkawari cewa zai kasance tare da mu. (Mat. 28:19, 20, Littafi Mai Tsarki) Ƙari ga haka, Jehobah ya ba mu ruhunsa mai tsarki da kayan aiki da kuma horarwa da muke bukata don mu koyar da mutane. (Zak. 4:6; 2 Kor. 4:7) Saboda haka, za mu iya roƙon Allah ya sa mu kasance da marmari da kuma ikon saka hannu a wannan aiki mai muhimmanci.—Filib. 2:13.

4. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali wajen almajirtar da mutane?

4 Yin wa’azi yana sa mu yi farin ciki. Amma, za mu yi farin ciki sosai sa’ad da muka taimaka wa wani ya san Allah kuma ya soma bin hanyar da “ta nufa wajen rai.” (Mat. 7:14; 1 Tas. 2:19, 20) Mafi muhimmanci, idan muka mai da hankali wajen almajirtar da mutane, za mu faranta wa Jehobah rai domin “ba ya so kowa ya halaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.”—2 Bit. 3:9, LMT.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba