Tsarin Ayyuka na Makon 28 ga Yuni
MAKON 28 GA YUNI
Waƙa ta 62
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
bh rataye shafuffuka na 204-206
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sarakuna 3-6
Bitar Makarantar Hidima Ta Allah
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 90
Minti 5: Sanarwa.
Minti 15: Ka Yi Shirin Gabatar da Mujallu a Watan Yuli. Tattaunawa da masu sauraro. Ka ɗauki minti ɗaya ko biyu ka yi bitar abin da ke ciki mujallun. Sai ka zaɓi talifofi biyu ko uku, kuma ka gayyaci masu sauraro su faɗi tambayoyi da nassosi da za a iya yin amfani da su wajen gabatarwan. Ka gwada yadda za a gabatar da kowanne talifin. Ka kammala da wani gwaji da ya nuna yadda za a iya soma nazarin Littafi Mai Tsarki sa’ad da aka koma ziyara.—Duba km-E 8/07 shafi na 3.
Minti 15: An Koyar da Shi Tun Yana Yaro. Tattaunawa da masu sauraro. Timotawus ƙwararren mai wa’azi ne kuma mai ƙwazo. (Filib. 2:20-22) Hakan ya faru ne, a wani galibi, saboda koyarwa ta ruhaniya da ya samu daga mahaifiyarsa da kakarsa tun yana ɗan ƙarami. (2 Tim. 1:5; 3:15) Shawarwarin da ke gaba da aka ɗauko daga Nassosi za su taimaka wa iyaye su koyar da yaransu su zama ƙwararrun masu wa’azin bishara. (1) Ku riƙa fita hidima da yaronka tun yana ƙarami, ku koya masa ya saka hannu bisa ga shekarunsa da iyawarsa. (Mis. 22:6) (2) Ku kafa misali mai kyau ta wajen mai da hidima ta zama abin farko. (Filib. 1:9, 10) (3) Ku cusa musu ƙauna da kuma muhimmancin aikin wa’azi a lokacin da kuke yin Bauta Ta Iyali da sauran lokatai. (K. Sha 6:6, 7) (4) Ku kasance da ra’ayin da ya dace game da hidima a hali da kalamanku. (Filib. 3:8; 4:8; 1 Tim. 1:12) (5) Ku riƙa fita hidima a kai a kai a matsayin iyali, kuna sa hidima ta zama jininku. (A. M. 5:41, 42) (6) Ku yi tarayya da waɗanda suke da ƙwazo a hidima. (Mis. 13:20) Ka gayyaci masu sauraro su yi furci a kan ainihin abin da iyayensu suka yi don su taimaka musu su more hidima kuma su ƙware.
Waƙa ta 88