Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 11/15 pp. 16-20
  • “Baƙi” A Cikin Muguwar Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Baƙi” A Cikin Muguwar Duniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sun Yi Rayuwa a Matsayin “Baƙi”
  • Gargaɗi ga Isra’ilawa
  • “Ba na Duniya Ba Ne”
  • Ba Sa Cika Moriyar Duniya
  • Ka Guji Sa Alhini na Rayuwa Ya Nauyaya Ka
  • ‘Duniya Tana Wucewa’
  • Ku Daraja Matsayinku Na “Baƙi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • “Kuna Al’amura Na Dacewa Wurin Al’ummai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Kada Ka Yi Kasala A Aikin Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 11/15 pp. 16-20

“Baƙi” A Cikin Muguwar Duniya

“Cikin bangaskiya, . . . suka shaida haka nan su baƙi ne, alhazai ne cikin duniya.”—IBRAN. 11:13.

1. Mene ne Yesu ya ce game da matsayin mabiyansa a duniya?

YESU ya ce game da almajiransa: “Suna cikin duniya.” Amma ya bayyana: “Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yoh. 17:11, 14) Da hakan, Yesu ya bayyana matsayin mabiyinsa na gaske a wannan “zamani” da Shaiɗan yake mulki. (2 Kor. 4:4) Ko da yake suna zama a wannan muguwar duniya, amma su ba na duniya ba ne. Yanayinsu a wannan zamanin zai zama na “baƙi masu-tafiya.”—1 Bit. 2:11.

Sun Yi Rayuwa a Matsayin “Baƙi”

2, 3. Me ya sa za a iya ce Anuhu da Nuhu da Ibrahim da kuma Saratu sun yi rayuwa a matsayin ‘baƙi da alhazai cikin duniya’?

2 Tun daga zamanin dā, bayin Jehobah amintattu sun kasance dabam daga mutanen da ke muguwar zamanin da suke ciki. Kafin Rigyawar, Anuhu da Nuhu sun yi “tafiya tare da Allah.” (Far. 5:22-24; 6:9) Dukansu biyu masu wa’azin hukuncin Jehobah da gaba gaɗi a kan wannan muguwar duniya na Shaiɗan ne. (Karanta 2 Bitrus 2:5; Yahuda 14, 15.) Domin sun yi tafiya da Allah a muguwar duniya, Anuhu “mai-game Allah ne sarai” kuma Nuhu “marar-aibi ne cikin tsararakinsa.”—Ibran. 11:5; Far. 6:9.

3 Ibrahim da Saratu sun yi biyayya ga Allah kuma suka bar rayuwa ta jin daɗi a birnin Ur na Kaldiyawa kuma sun kasance a shirye su zauna a wata ƙasa ba tare da samun gidan kansu ba. (Far. 11:27, 28; 12:1) Manzo Bulus ya rubuta: “Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa’anda aka kira shi, ya yi biyayya shi tafi zuwa wani wurin da zai karɓe shi gādo; ya kuwa fita, bai san inda za shi ba. Ta wurin bangaskiya ya baƙunta cikin ƙasar alkawari, sai ka ce ba tasa ba ce, yana zaune cikin tenti, tare da Ishaƙu da Yakubu, magāda tare da shi na alkawarin.” (Ibran. 11:8, 9) Bulus ya faɗa game da irin waɗannan bayin Jehobah masu aminci cewa: “Dukan waɗannan suka mutu cikin bangaskiya, ba su rigaya sun amshi alkawarai ba, amma daga nesa suka tsinkaye su, suka yi masu maraba, suka shaida haka nan su baƙi ne, alhazai ne cikin duniya.”—Ibran. 11:13.

Gargaɗi ga Isra’ilawa

4. Wane gargaɗi ne aka ba Isra’ilawa kafin su zama mazauna a ƙasarsu?

4 Zuriyar Ibrahim, wato, Isra’ilawa sun yi yawa kuma daga baya aka mai da su al’umma mai tsarin dokoki da kuma ƙasa. (Far. 48:4; K. Sha 6:1) Bai kamata Isra’ilawa su manta cewa Jehobah ne ainihin Mai ƙasar da suke ciki ba. (Lev. 25:23) Suna kama da masu haya da suke bukatar su yi biyayya ga abin da Mai ƙasar yake so. Ƙari ga hakan, an bukace su su tuna cewa “mutum ba da abinci kaɗai ya ke rayuwa ba,” an bukace su kada su ƙyale ni’ima na abubuwan mallaka su sa su manta da Jehobah. (K. Sha 8:1-3) Jehobah ya ba Is’ra’ilawa wannan gargaɗin kafin su zama mazauna a ƙasarsu: “Za ya zama kuma, sa’anda Ubangiji Allahnka ya kawo ka cikin ƙasa wadda ya rantse ma ubanninka, Ibrahim, da Ishaƙu, da Yaƙub, za ya ba ka; manyan birane masu-kyau, waɗanda ba kai ka gina ba, da gidaje cikakku da kowane abu mai-kyau, waɗanda ba kai ne ka cika su ba, rijiyoyi haƙaƙu waɗanda ba kai ne ka haƙa ba, gonakin anab da itatuwan zaitun, waɗanda ba kai ne ka dasa ba, za ka kuwa ci ka ƙoshi; sa’annan ka yi hankali kada ka manta da Ubangiji.”—K. Sha 6:10-12.

5. Me ya sa Jehobah ya ƙi da Isra’ilawa, kuma ga wace sabuwar al’umma ce ya nuna wa tagomashinsa?

5 Ba su bi wannan gargaɗin ba. A zamanin Nehemiya, rukunin Lawiyawa sun faɗi abin da ya faru da Isra’ilawa da kunya sa’ad da suka zama mazauna a Ƙasar Alkawari. Bayan da Isra’ilawa suka zauna a gidaje masu kyau kuma suna da abinci da ruwan anab a yalwace “suka ci fa, suka ƙoshi, suka yi ƙiba.” Sun yi tawaye da Allah, kuma suka kashe annabawan da ya aika su gargaɗe su. Don haka, Jehobah ya ƙyale magabtansu su mallake su. (Karanta Nehemiya 9:25-27; Hos. 13:6-9) Daga baya sa’ad da Romawa suka mallake su, Yahudawa marasa bangaskiya suka kashe Almasihun da aka yi musu alkawarinsa! Jehobah ya ƙi da su kuma ya nuna wa sabuwar al’umma, wato, Isra’ila ta ruhaniya tagomashinsa.—Mat. 21:43; A. M. 7:51, 52; Gal. 6:16.

“Ba na Duniya Ba Ne”

6, 7. (a) Yaya za ka bayyana abin da Yesu ya ce game da matsayin mabiyansa game da duniya? (b) Me ya sa Kiristoci na gaskiya ba za su zama na duniyar Shaiɗan ba?

6 Kamar yadda aka nuna a farkon wannan talifin, Yesu Kristi, Shugaban ikilisiyar Kirista, ya nuna sarai cewa mabiyansa za su kasance dabam da duniya, wato, mugun tsarin abubuwa na Shaiɗan. Gab da mutuwarsa, Yesu ya gaya wa almajiransa: “Da na duniya ne ku, da duniya ta yi ƙaunar nata; amma domin ku ba na duniya ba ne, amma ni na zaɓe ku daga cikin duniya, saboda wannan duniya tana ƙinku.”—Yoh. 15:19.

7 Bayan ɗan lokaci, Kiristoci da yawa sun kasance a wuraren da Romawa suke sarauta. Kiristoci suna bukata su ci gaba da ware kansu daga duniya. A duk inda suke da zama, za su kasance dabam da tsarin Shaiɗan. Shekara talatin bayan mutuwar Kristi, manzo Bitrus ya rubuta wa Kiristoci da suke da zama a duk ɓangarorin Roma: “Ƙaunatattu, ina roƙonku misalin saukakku, baƙi masu-tafiya kuma, ku hanu daga sha’awoyi na jiki, waɗanda ke yaƙi da rai; kuna al’amura na dacewa wurin al’ummai.”—1 Bit. 1:1; 2:11, 12.

8. Ta yaya wani ɗan tarihi ya kwatanta dangantakar Kiristoci na farko da duniya?

8 Sa’ad da wani ɗan tarihi Kenneth Scott Latourette yake nuna cewa Kiristoci na farko sun yi rayuwa a matsayin ‘baƙi da alhazai cikin duniya’ ya rubuta: “A ƙarni na farko, an tsananta wa Kiristoci sosai, kuma hakan ya faru sau da yawa. Domin sun ƙi su saka hannu cikin bukukuwa na addinan ƙarya sai aka yi masu zargi cewa ba su gaskata da Allah ba. An kira su masu ƙin ’yan Adam domin ba sa bin mutane da ke tare da su wajen yin nishaɗi da kuma bukukuwan da ake bautar ƙarya da lalata.”

Ba Sa Cika Moriyar Duniya

9. A matsayin Kiristoci na gaskiya, ta yaya muke ba da tabbaci cewa ba mu “ƙi jinin ’yan Adam ba”?

9 Mene ne yanayin a yau? Muna bin halin Kiristoci na farko game da ‘muguwar duniya ta yanzu.’ (Gal. 1:4) Saboda haka, mutane da yawa ba su fahimce mu ba kuma wasu sun tsane mu. Amma, ba mu “ƙi jinin ’yan Adam ba.” Domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu ’yan Adam, muna bi gida gida, muna iya ƙoƙarinmu domin mu yi wa kowanne mutum ‘bishara ta mulkin Allah.’ (Mat. 22:39; 24:14) Muna yin hakan domin muna da tabbaci cewa Mulkin Jehobah a ƙarƙashin Kristi ba da daɗewa ba zai kawo ƙarshen sarauta na ’yan Adam ajizai, zai sake shi da sabon yanayi.—Dan. 2:44; 2 Bit. 3:13.

10, 11. (a) Yaya ya kamata mu more duniya? (b) A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci masu tsaro ba sa cika moran duniya?

10 Domin ƙarshen zamanin nan ya kusa, a matsayin bayin Jehobah mun fahimci cewa wannan ba lokacin yin rayuwa ta jin daɗi a wannan duniya da take taɓarɓarewa ba ne. Muna biyayya ga kalamin manzo Bulus: “Abin da na ke faɗi ke nan, ’yan’uwa, an gajertar da kwanaki, domin nan gaba . . . masu-saye kuma, kamar su ba masu-abu ba ne, waɗanda su ke moron duniya, kamar ba su cika moriyatata ba; gama ƙa’idar duniyan nan tana shuɗewa.” (1 Kor. 7:29-31) Amma yaya Kiristoci na zamani suke moran duniya? Suna yin hakan ta wajen yin amfani da fasaha na zamani da kuma hanyar sadarwa don yaɗa koyarwa na Littafi Mai Tsarki a dukan duniya a cikin harsuna da yawa. Suna ɗan amfani da duniya don biyan bukatunsu. Suna sayan kaya da kuma yin amfani da hidimomi da suka dace da ke cikin duniya. Hakan yana nufin cewa ba kuɗi da abubuwan da muke da su da kuma aikinmu ba ne suka fi muhimmanci a rayuwarmu ba.—Karanta 1 Timotawus 6:9, 10.

11 Wata hanya da Kiristoci masu yin tsaro suke nuna cewa ba sa cika moran duniya ita ce ta wajen ƙin sa biɗan ilimi a jami’a ta kasance abu mafi muhimmanci a gare su. Mutane da yawa a wannan duniya suna ganin cewa dole ne mutum ya je jami’a don ya samu aiki mai kyau da kuma kuɗi sosai. Amma mu Kiristoci muna zama a matsayin baƙi kuma muna biɗan maƙasudai dabam da nasu. Muna guje wa ‘biɗan manyan abubuwa.’ (Rom. 12:16; Irm. 45:5) Tun da yake mu mabiyan Yesu ne, muna bin gargaɗinsa: “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan ƙyashi: gama ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.” (Luk 12:15) Saboda haka, ya kamata Kiristoci matasa su tuna cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne su bauta wa Jehobah. Ya kamata su je makarantar da za ta taimaka musu su iya kula da kansu domin su samu zarafin bauta wa Jehobah ‘da dukan zuciyarsu da ransu da ƙarfinsu da azancinsu.’ (Luk 10:27) Ta wajen yin hakan, suna iya zama ‘mawadata ga Allah.’—Luk 12:21; karanta Matta 6:19-21.

Ka Guji Sa Alhini na Rayuwa Ya Nauyaya Ka

12, 13. Ta yaya bin kalamin Yesu da ke rubuce a Matta 6:31-33 ya bambanta mu da mutanen duniya?

12 Bayin Jehobah sun yi dabam da mutanen duniya a halinsu game da abin duniya. Game da wannan batun, Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, Me za mu ci? ko kuwa, Me za mu sha? ko kuwa, Da minene za mu yi sutura? Gama waɗannan abubuwa duka al’ummai suna ta biɗa; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abubuwa duka. Amma ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.” (Mat. 6:31-33) Daga abubuwa da suka fuskanta, ’yan’uwanmu da yawa sun ga cewa Ubanmu na samaniya yana biyan bukatunsu.

13 “Ibada tare da wadar zuci riba ce mai-girma.” (1 Tim. 6:6) Amma ra’ayin mutane a duniya ta yau dabam ne. Alal misali, sa’ad da matasa suka yi aure, da yawa cikinsu suna son su samu kome nan da nan. Suna son gida da kayan ɗaki da mota mai kyau da sababbin na’urorin ɗaki da suke amfani da lantarki. Amma, Kiristoci da suke zama a matsayin baƙi suna sa sha’awoyinsu su kasance daidai wa daida kuma su zama wanda zai yiwu a cim ma. Hakika, abin yabawa ne cewa mutane da yawa sun bar wasu jin daɗi na duniya domin su ba da ƙarin lokaci da kuzari a hidimar Jehobah a matsayin masu shelar Mulki da ƙwazo. Wasu suna hidima a matsayin majagaba da kuma a Bethel da aikin masu ziyara ko kuma masu wa’azi a ƙasashen waje. Dukanmu muna godiya sosai don hidima da ’yan’uwanmu masu bi suke yi ga Jehobah da dukan zuciyarsu!

14. Wane darassi ne za mu iya koya daga almarar Yesu na mai shuki?

14 A cikin almararsa na mai shuki, Yesu ya ce “ɗawainiyar duniya, da ruɗin dukiya” suna iya shaƙe kalmar Allah a zuciyarmu kuma ya sa mu zama marasa amfani. (Mat. 13:22) Kasancewa masu wadar zuci a matsayin baƙi a wannan duniya zai taimaka mana mu guji faɗawa cikin wannan tarko. Maimakon haka, zai taimaka mana mu sa idonmu “sarai” ga Mulkin Allah da kuma sa al’amuransa su kasance farko a rayuwarmu.—Mat. 6:22.

‘Duniya Tana Wucewa’

15. Wane kalamin manzo Yohanna ne yake nuna ra’ayi da kuma halin Kiristoci na gaskiya game da wannan duniya?

15 Wani dalili mai muhimmanci da ya sa Kiristoci na gaskiya suke rayuwa a matsayin ‘baƙi da kuma alhazai’ shi ne don sun gaskata cewa ba da daɗewa ba duniyar Shaiɗan za ta zo ƙarshenta. (1 Bit. 2:11; 2 Bit. 3:7) Muna nuna cewa mun gaskata wannan ta yadda muke rayuwa da sha’awoyinmu da kuma maƙasudinmu. Manzo Yohanna ya gargaɗi ’yan’uwansa kada su yi ƙaunar duniya ko kuma abubuwa da ke cikin duniya domin “duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”—1 Yoh. 2:15-17.

16. Ta yaya za mu nuna cewa an ware mu a matsayin mutanen da suke dabam?

16 An gaya wa Isra’ilawa cewa idan sun yi biyayya ga Jehobah, za su zama ‘keɓaɓiyar taska a gare shi daga cikin dukan al’umman duniya.’ (Fit. 19:5) Sa’ad da suke da aminci, Isra’ila ta yi dabam daga sauran al’ummai a yadda suke bauta da kuma hanyar rayuwarsu. Haka nan ma a yau, Jehobah ya ware wa kansa mutane da suke dabam da duniyar Shaiɗan. An umurce mu: “Mu rayu da hankali da adalci da ibada cikin wannan zamani na yanzu, yayinda muna ƙin rashin ibada da sha’awoyi na duniya; muna sauraron begen nan mai-albarka da bayanuwar darajar Allahnmu mai-girma Mai-cetonmu kuma Yesu Kristi: wanda ya bada kansa dominmu, domin shi fanshe mu daga dukan zunubi, shi tsarkake wa kansa jama’a su zama abin mulkinsa, masu-himman nagargarun ayyuka.” (Tit. 2:11-14) Wannan “jama’a” sun ƙunshi shafaffu Kiristoci da “waɗansu tumaki” na Yesu masu yawa waɗanda suka taimaka da kuma tallafa masa.—Yoh. 10:16.

17. Me ya sa shafaffu da abokansu ba su taɓa yin da na sani ba don sun yi rayuwa a matsayin baƙi a wannan muguwar duniyar?

17 “Begen nan mai-albarka” na shafaffu shi ne su yi sarauta tare da Kristi a sama. (R. Yoh. 5:10) Sa’ad da begen waɗansu tumaki na rai madawwami a duniya ya cika, ba za su ƙara zama baƙi a wannan muguwar duniya kuma ba. Za su samu gidaje masu kyau da abinci da kuma abin sha a yalwace. (Zab. 37:10, 11; Isha. 25:6; 65:21, 22) Ba za su kasance kamar Isra’ilawa ba da suka manta da Jehobah, amma, za su ci gaba da tuna cewa dukan waɗannan daga wurin Jehobah ne, “Allah na dukan duniya.” (Isa. 54:5) Shafaffu da waɗansu tumaki ba za su yi da na sani ba don sun zama baƙi a wannan muguwar duniya.

Yaya Za Ka Amsa?

• A wace hanya ce mutane masu aminci na dā suka yi rayuwa a matsayin baƙi?

• Yaya Kiristoci na farko suka aikata game da wannan duniyar?

• Ta yaya Kiristoci na gaskiya ba sa cika moran duniya?

• Me ya sa ba za mu taɓa yin nadamar cewa mun yin rayuwa a matsayin baƙi a wannan muguwar duniya ba?

[Hoto a shafi na 18]

Kiristoci na zamanin dā sun guji saka hannu a nishaɗin mugunta da lalata

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba