Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 11/15 p. 21
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 11/15 p. 21

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Shin zai yiwu a san daidai sa’ar da aka rataye Yesu Kristi?

An yi wannan tambayar ne saboda ɗan saɓanin da aka samu tsakanin labarin da Markus marubucin Linjila ya rubuta da wanda manzo Yohanna ya rubuta game da rasuwar Yesu. Markus ya ce: “Sa’a ta uku ke nan, sai [sojoji suka] rataye shi.” (Mar. 15:25, NW) Yohanna ya ce, “a wajen sa’a shidda ne” sa’ad da Bilatus ya miƙa Yesu ga Yahudawa domin su rataye shi. (Yoh. 19:14-16) Masu bayyana Littafi Mai Tsarki sun ba da bayani dabam-dabam game da wannan saɓanin. Amma dai, babu isashen bayanai na Nassi da za su bayyana bambancin da ke tsakanin waɗannan labarai biyu. Duk da haka, yin la’akari da yadda mutane suke ɗaukan lokaci a dā zai iya kasance da amfani.

A ƙarni na farko A.Z., Yahudawa suna raba rana zuwa sa’o’i 12, kuma suna soma ƙirgawa daga fitowar rana. (Yoh. 11:9) Saboda haka, “Sa’a ta uku” tana somawa daga ƙarfe takwas zuwa ƙarfe tara na safiya kuma “sa’a shidda” tana ƙarewa da rana. Hakika, rana tana fitowa kuma tana faɗuwa a lokaci dabam-dabam a shekara. Saboda haka, tsawon rana yana samun bambanci bisa ga yanayi. Bugu da ƙari, ana sanin lokaci ta kallon inda rana take. Da haka, ana kimanta lokaci ne. Galibi, Nassosin Hellenanci na Kirista yana amfani da sa’a ta uku da ta shida da ta tara sa’ad da yake bayyana wani abu, sau da yawa a kusan lokacin. (Mat. 20:3, 5; A. M. 10:3, 9, 30) An furta wasu takamammun bayanai kamar “sa’a ta bakwai,” don lokacin tana da muhimmanci domin labarin da ake faɗa.—Yoh. 4:52.

Abin da Linjila ta faɗa game da sa’a ta ƙarshe na rayuwar Yesu a duniya duk ɗaya ne. Duka huɗun sun nuna cewa firistoci da dattawan sun yi taro bayan faɗuwar rana kuma sun sa aka kai Yesu wurin Gwamnan ƙasar Roma, wato, Bilatus Ba-Bunti. (Mat. 27:1; Mar. 15:1; Luk 22:66; Yoh. 18:28) Matta da Markus da Luka duk sun ba da rahoto cewa daga sa’a ta shida, sa’ad da Yesu yake kan gungumen, kuma duhu ta rufe dukan ƙasar “har sa’a ta tara.”—Mat. 27:45, 46; Mar. 15:33, 34; Luk 23:44.

Wani abin da zai iya nuna lokacin da aka rataye Yesu shi ne: Ana yawan haɗa lokacin da ake dūkan mutum a matsayin rataye shi. Kuma a wasu lokatai, dūkan yana yin tsanani sosai har mutumin yana iya mutuwa. Babu shakka na Yesu ma ya yi tsanani sosai har wani mutum ya taya Yesu ɗaukan gungumen azaban. (Luk 23:26; Yoh. 19:17) Idan dūkan mutum yana cikin tsarin rataya, babu shakka, wasu sa’o’i sun wuce kafin a rataye Yesu a kan gungumen. Saboda haka, kowanne mutum zai iya faɗa lokaci dabam-dabam da aka rataye Yesu, dangane da abubuwan da suka auku da suka shaida kafin a rataye shi.

Manzo Yohanna ya rubuta labarinsa ƙarnuka da yawa bayan sauran marubutan Linjila sun kammala rubutunsu. Saboda haka, ya samu damar karanta labarun da suka rubuta. A gaskiya, Yohanna ya rubuta lokacin da ya bambanta da wanda Markus ya rubuta. Amma dai, hakan ya nuna cewa Yohanna bai je ya kofa abin da Markus ya rubuta kawai ba. Allah ne ya hure Yohanna da Markus. Ko da yake babu isassun bayanai na Nassosi da suka bayyana bambancin da ke waɗannan ayoyin, amma za mu iya dogara ga labarin da ke Linjila.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba