Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 11/1 pp. 19-24
  • “Kuna Al’amura Na Dacewa Wurin Al’ummai”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Kuna Al’amura Na Dacewa Wurin Al’ummai”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Iyalan Kiristoci
  • ’Yan’uwanci na Kiristoci
  • Sha’ani da Duniya
  • ‘Ku Riƙe Halaye na Kirki’
  • Miƙa Kai na Kirista
  • Bayin Allah
  • Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ku Daraja Matsayinku Na “Baƙi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • A Ina Ƙaunarka Ta Tsaya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 11/1 pp. 19-24

“Kuna Al’amura Na Dacewa Wurin Al’ummai”

“Ku girmama dukan mutane. Ku ƙaunaci ’yan’uwanci.” —1 BITRUS 2:17.

1, 2. (a) Wane kalami ne marubucin jarida ya yi game da Shaidun Jehovah? (b) Me ya sa Shaidun Jehovah suke ƙoƙarin su riƙe mizanan ɗabi’a masu kyau?

SHEKARU da yawa da suka gabata, marubucin jarida a Amarillo, Texas, U.S.A., ya ziyarci coci dabam dabam a yankin kuma ya ba da rahoton abin da ya gani. Wani rukuni ya burge shi. Ya ce: “Shekara uku, ina halartar taron Shaidun Jehovah na shekara shekara a Filin Taro na Amarillo. Sa’ad da na yi tarayya da su, ban taɓa ganin wanda ya kunna sigari ba, ko kuma wanda ya buɗe kwalabar giya ba, ko kuma wanda yake batsa. Su mutane mafi tsabta ne, mafi ɗabi’a, masu ado da kyau, taron mutane mai kyau ne da na taɓa gani.” Irin wannan kalami game da Shaidun Jehovah sau da yawa an buga su. Me ya sa mutane da ba sa cikin imani ɗaya suke yawan yaba wa Shaidun?

2 Dalilin shi ne, ana yaba wa mutanen Allah domin halayensu ne masu kyau. Ko da yake mizanan ɗabi’a suna lalacewa, wajibi ne ga Shaidun Jehovah su kasance da mizanan ɗabi’a masu kyau, kuma ɓangaren bautarsu ne. Sun sani cewa ayyukansu zai shafi Jehovah da kuma ’yan’uwansu Kiristoci kuma halayensu yana yaba wa gaskiyar da suke yin wa’azinta. (Yohanna 15:8; Titus 2:7, 8) Bari mu ga yadda za mu riƙe halayenmu masu kyau ta haka mu ci gaba da riƙe suna mai kyau na Jehovah da Shaidunsa da kuma yadda muke amfanar kanmu ta wajen yin haka.

Iyalan Kiristoci

3. Daga menene ake bukatar a kāre iyalan Kiristoci?

3 Mu yi la’akari da halayenmu cikin iyali. Wani littafi Die Neuen Inquisitoren: Religionsfreiheit und Glaubensneid (Sabon Matambayi: ’Yancin Addini da kuma Hassadar Addini), wanda Gerhard Besier da Erwin K. Scheuch suka rubuta, ya ce: “Ga [Shaidun Jehovah], iyali aba ce da musamman ya kamata a kāre ta.” Wannan furcin gaskiya ne, kuma a yau da akwai abubuwa da yawa da ake bukatar a kāre iyali daga gare su. Da akwai yara “marasa-bin iyaye” da kuma manya “marasa-ƙauna irin ta taɓi’a” ko kuma “marasa-kamewa.” (2 Timothawus 3:2, 3) Iyali ta zama filin faɗa tsakanin ma’aurata, iyaye suna zaluntar ko kuma suna ƙyale ’ya’yansu, kuma yara suna tawaye, suna saka kai cikin shan miyagun ƙwayoyi da lalata, ko kuma su gudu daga gida. Dukan wannan domin rinjaya mai halakarwa na ‘ruhun duniya’ ne. (Afisawa 2:1, 2) Muna bukatar mu kāre iyalanmu daga wannan ruhun. Ta yaya? Ta wajen bin gargaɗin Jehovah da kuma ja-gorarsa ga waɗanda suke cikin iyali.

4. Wane hakki ne kowa a cikin iyali yake da shi ga juna?

4 Ma’aurata Kiristoci sun fahimci cewa suna da hakki na motsin zuci, da na ruhaniya, da wajibin jikinsu ga junansu. (1 Korinthiyawa 7:3-5; Afisawa 5:21-23; 1 Bitrus 3:7) Iyaye Kiristoci suna da hakki mai nauyi na ’ya’yansu. (Misalai 22:6; 2 Korinthiyawa 12:14; Afisawa 6:4) Kuma sa’ad da yara a gidajen Kiristoci suka yi girma, suna koyon cewa su ma suna da hakki. (Misalai 1:8, 9; 23:22; Afisawa 6:1; 1 Timothawus 5:3, 4, 8) Cika hakkin iyali yana bukatar ƙoƙari, naciya, da kuma halin ƙauna da kuma sadaukar da kai. Saboda haka, iyakar yadda kowa a iyali ya cika hakki da Allah ya ba shi, iyakar yadda za a albarkace su da kuma ikilisiya ke nan. Mafi muhimmanci ma, suna daraja Wanda ya kafa iyali, Jehovah Allah.—Farawa 1:27, 28; Afisawa 3:15.

’Yan’uwanci na Kiristoci

5. Waɗanne albarka muke samu daga yin tarayya da ’yan’uwanmu Kiristoci?

5 Mu Kiristoci, mu ma muna da hakki ga ’yan’uwa a ikilisiya, musamman, ga waɗanda suka taru suka kasance “ ’yan’uwanku da ke cikin duniya.” (1 Bitrus 5:9) Dangantakarmu da ikilisiya tana da muhimmanci ga lafiyarmu ta ruhaniya. Sa’ad da muke taro da ’yan’uwa Kiristoci, muna more cuɗanyarsu mai ƙarfafawa haɗe da abinci mai gina jiki na ruhaniya daga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Matta 24:45-47) Idan muna da matsaloli, za mu iya zuwa wajen ’yan’uwanmu domin shawara mai kyau da take bisa mizanan Nassosi. (Misalai 17:17; Mai-Wa’azi 4:9; Yaƙub 5:13-18) Sa’ad da muke da bukata ’yan’uwanmu ba sa guje mana. Hakika albarka ce a kasance cikin ƙungiyar Allah!

6. Ta yaya Bulus ya nuna cewa muna da hakki ga wasu Kiristoci?

6 Duk da haka, ba mu kasance cikin ikilisiya domin kawai muna so a ba mu ba; mun kasance ne domin mu ma mu bayar. Hakika, Yesu ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayukan Manzanni 20:35) Manzo Bulus ya nanata halin bayarwa sa’ad da ya ce: “Bari mu riƙe shaidar begenmu da ƙarfi kada ta yi rawa; gama shi mai-aminci ne wanda ya yi alkawari: bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗadda juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.”—Ibraniyawa 10:23-25.

7, 8. Ta yaya za mu nuna halin bayarwa a cikin ikilisiya da kuma ga Kiristoci waɗanda suke wasu ƙasashe?

7 A cikin ikilisiya, muna ‘furta begenmu’ sa’ad da muka yi kalami lokacin da ake gabatar da taro ko kuma muka saka hannu cikin tsarin ayyuka a wasu hanyoyi. Waɗannan gudummawa babu shakka suna ƙarfafa ’yan’uwanmu. Muna kuma ƙarfafa su ta wajen taɗinmu kafin taro ya soma da kuma bayan an gama taro. Wannan lokaci ne da za mu iya mu ƙarfafa raunannu, kuma lallashi masu rauni a zuci, kuma mu yi wa marasa lafiya jaje. (1 Tassalunikawa 5:14) Tun da Kiristoci masu karimanci ne a irin wannan bayarwa, kuma abin da ya sa ke nan mutane da yawa da suka halarci taronsu na farko, ƙauna da suka lura tsakaninmu ta burge su.—Zabura 37:21; Yohanna 15:12; 1 Korinthiyawa 14:25.

8 Duk da haka, ƙaunarmu ba ta tsaya ga ikilisiyarmu ba kawai. Ta ƙunshi dukan ’yan’uwantaka ta duniya. Abin da ya sa ke nan, alal misali, muke da akwatuna na Kuɗin Gina Majami’ar Mulki a yawancin Majami’un Mulki. Wataƙila Majami’ar Mulki tamu tana da kyau, amma mun sani cewa ’yan’uwanmu Kiristoci dubbai a wasu ƙasashe ba su da wurare masu kyau da za su taru. Sa’ad da muka ba da kyauta don Kuɗin Gina Majami’ar Mulki, muna nuna ƙaunarmu ga mutanen ko idan ba mu san su ba ma da kanmu.

9. Domin wannan dalili ne Shaidun Jehovah suke ƙaunar juna?

9 Me ya sa Shaidun Jehovah suke ƙaunar juna? Domin Yesu ya umurce su su yi haka. (Yohanna 15:17) Kuma ƙaunar da suke da ita ga juna tabbaci ne na cewa ruhun Allah yana aiki cikin kowannensu da kuma rukuninsu. Ƙauna “ ’yar Ruhu” ne. (Galatiyawa 5:22, 23) Sa’ad da Shaidun Jehovah suke nazarin Littafi Mai Tsarki, suke halartar taron Kirista, kuma suke addu’a babu fasawa ga Allah, ƙauna ta zama da sauƙi a gare su ko da yake suna rayuwa cikin duniyar da ‘ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi.’—Matta 24:12.

Sha’ani da Duniya

10. Wane hakki muke da shi ga wannan duniya?

10 Da Bulus ya ambaci “shaida zuwa ceto” ya tuna mana wani hakkinmu. Wannan shaidar ta ƙunshi yin wa’azin bishara ga waɗanda har yanzu ba su zama ’yan’uwanmu Kiristoci ba tukuna. (Matta 24:14; 28:19, 20; Romawa 10:9, 10, 13-15) Irin wannan wa’azin wani aikin bayarwa ne. Domin mu saka hannu, zai ɗauki ɗan lokaci, kuzari, shiri, horo, da kuma yin amfani da dukiyarmu. Duk da haka, Bulus ya sake rubutawa: “Ni mabarci ne ga Helenawa duk da Baibayi, ga masu-hikima duk da marasa-hikima. Domin wannan fa, gwargwadon ƙarfina, a shirye ni ke in yi wa’azin bishara a gareku waɗanda ke cikin Roma kuma.” (Romawa 1:14, 15) Kamar Bulus, ba za mu kasance marowata ba wajen biyan “bashinmu.”

11. Wane mizanai biyu ne na Nassosi suke ja-gorar dangantakarmu da duniya, amma duk da wannan menene muka fahimta?

11 Muna da wani hakki ne ga waɗanda ba ’yan’uwanmu ba masu bi? Ƙwarai kuwa. Babu shakka, mun fahimci cewa “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Mun sani cewa Yesu ya ce almajiransa: “Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” Duk da haka, muna raye cikin duniya, muna neman abinci a cikin ta, kuma ana yi mana wasu ayyuka a cikinta. (Yohanna 17:11, 15, 16) Saboda haka, muna da hakki ga duniya. Menene waɗannan? Manzo Bitrus ya amsa wannan tambayar. Lokacin da ake goshin halaka Urushalima, ya rubuta wasiƙa zuwa ga Kiristoci a Asiya Ƙarama, kuma wannan abin da ya rubuta cikin wasiƙa ya taimaka mana mu daidaita a dangantakarmu da duniya.

12. A wace hanya ce Kiristoci ‘baƙi ne, bare ne,’ saboda haka, menene ya kamata su guje wa?

12 Da farko Bitrus ya ce: “Ƙaunatattu, ina roƙonku misalin saukakku, baƙi masu-tafiya kuma, ku hanu daga sha’awoyi na jiki, waɗanda ke yaƙi da rai.” (1 Bitrus 2:11) Kiristoci na gaskiya, a hanya ta ruhaniya, ‘baƙi ne, bare ne’ domin ainihin dalilin rayuwarsu, begen rai madawwami ne—waɗanda ruhu ya shafe su a samaniya kuma “waɗansu tumaki” a aljanna a duniya ta nan gaba. (Yohanna 10:16; Filibbiyawa 3:20, 21; Ibraniyawa 11:13; Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14-17) To, menene sha’awoyi na jiki? Waɗannan sun haɗa da abubuwa kamar su sha’awar zama mai arziki, sha’awar zama sananne, sha’awar lalata, da kuma sha’awoyi da aka kwatanta da “kishi” da “kwaɗayi.”—Kolossiyawa 3:5; 1 Timothawus 6:4, 9; 1 Yohanna 2:15, 16.

13. Ta yaya ne sha’awoyi na jiki suke “yaƙi da [‘ranmu’]”?

13 Irin waɗannan sha’awoyin babu shakka suna “yaƙi da rai.” Suna yi wa dangantakarmu da Allah zagon ƙasa kuma ta haka suna saka begenmu na Kirista (‘ranmu’) cikin haɗari. Alal misali, idan muna sha’awar lalata, ta yaya za mu ba da “jikunanmu hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah”? Idan muka fāɗa cikin tarkon son abin duniya, ta yaya muke “fara biɗan mulkinsa”? (Romawa 12:1, 2; Matta 6:33; 1 Timothawus 6:17-19) Hanya mai kyau shi ne mu bi misalin Musa, mu juya wa sha’awar duniya baya, kuma mu saka hidimar Jehovah farko a rayuwarmu. (Matta 6:19, 20; Ibraniyawa 11:24-26) Wannan abu ne mai muhimmanci na samun daidaitacciyar dangantaka da duniya.

‘Ku Riƙe Halaye na Kirki’

14. Me ya sa mu Kiristoci muke ƙoƙarin mu riƙe hali mai kyau?

14 Wani umurni mai muhimmanci an same shi cikin kalmomin Bitrus na gaba: “Kuna al’amura na dacewa wurin Al’ummai; domin, yayinda su ke kushenku kamar ma’aikatan mugunta, ta wurin nagargarun ayyukanku da su ke dubawa su ɗaukaka Allah cikin ranar ziyara.” (1 Bitrus 2:12) Mu Kiristoci muna ƙoƙarin mu kasance abin koyi. A makarantu muna ƙoƙari sosai. A wajen aikinmu, muna aiki kuma muna da gaskiya—har idan magidantan aikinmu sun kasance ba su da sauƙin hali. A gidaje da suka rabu ta wurin addini, maigida ko uwargida mai bi suna ƙoƙari na musamman domin su bi mizanan Kirista. Ba shi da sauƙi, amma mun sani cewa halinmu abin koyi yana faranta wa Jehovah rai kuma sau da yawa yana da sakamako mai kyau ga waɗanda ba Shaidu ba ne.—1 Bitrus 2:18-20; 3:1.

15. Ta yaya muka sani cewa mizani mai kyau na halin Shaidun Jehovah an san da shi a dukan duniya?

15 Nasarar yawancin Shaidun Jehovah wajen mizanai masu kyau ta bayyana a kalami game da su da aka buga a cikin shekaru da suka gabata. Alal misali, II Tempo na Italiya ya ba da rahoto: “Mutane da abokan aikinsu Shaidun Jehovah ne sun ce ma’aikata ne masu gaskiya, suna da tabbaci game da imaninsu har da sun shagala cikinsa; duk da haka, sun wajibci a daraja su domin ɗabi’arsu.” Herald na Boenos Aires, Argentina, ya ce: “Cikin shekaru da yawa, Shaidun Jehovah sun tabbatar da cewa su ma’aikata ne masu aiki tuƙuru, masu ƙwazo, masu tsoron Allah.” Manazarci na Rasha Sergei Ivanenko ya ce: “A dukan duniya an san da Shaidun Jehovah cewa mutane ne masu bin doka kuma musamman ma halinsu wajen biyan haraji.” Manajar wani fili a Zimbabwe da Shaidun Jehovah suke yin amfani da shi domin taronsu na gunduma ta ce: “Na ga wasu Shaidun Jehovah suna shara kuma suna wanke bayan gida. Sun bar filin da tsabta fiye da yadda yake a dā. Matasanku suna da ɗabi’a. Da ma a ce dukan duniya ta cika da Shaidun Jehovah.”

Miƙa Kai na Kirista

16. Mecece dangantakarmu da masu sarauta, kuma me ya sa?

16 Bitrus ma ya yi magana game da dangantakarmu da masu sarauta. Ya ce: “Ku yi biyayya ga kowanne hukunci na mutane sabili da Ubangiji: ko ga sarki, watau na birbishin duka ne; ko kuwa ga masu mulki, watau aikakkunsa ne domin ramawa bisa masu-aika mugunta, da yabo ga masu-aika nagarta. Gama hakanan nufin Allah ya ke, bisa ga aikin kirki ku kwaɓe jahilcin mutane marasa-hikima.” (1 Bitrus 2:13-15) Muna godiya domin amfani da muke samu daga gwamnatoci, kuma kalmomin Bitrus sun yi mana ja-gora, muna bin dokokinsu kuma muna biyan harajinmu. Ko da yake mun sani Allah ya ba su daman su hukunta masu taka doka, ainihin dalilin da ya sa za mu miƙa kai ga masu iko domin “Ubangiji ne.” Nufin Allah ne. Bugu da ƙari, ba ma fatan mu saɓa wa sunan Jehovah ta wajen yi mana horo domin mun taka doka.—Romawa 13:1, 4-7; Titus 3:1; 1 Bitrus 3:17.

17. Sa’ad da “mutane marasa-hikima” suka yi hamayya da mu, game da me za mu kasance da tabbaci?

17 Abin baƙin ciki, wasu “mutane marasa-hikima” a gwamnati suna tsananta mana ko kuma suna hamayya da mu a wasu hanyoyi—ta wajen yaɗa jita-jitar ƙarya game da mu. Duk da haka, a lokaci na Jehovah, ana fallasa ƙaryarsu, kuma an ƙwaɓe ‘maganganunsu na jahilci’ da kyau. Tarihin halayenmu na Kirista suna magana da kansu. Abin da ya sa kenan ma’aikatan gwamnati masu gaskiya suke yaba mana cewa mu masu aikata nagarta ne.—Romawa 13:3; Titus 2:7, 8.

Bayin Allah

18. Mu Kiristoci, a waɗanne hanyoyi ne za mu iya guje yin ƙeta da ’yancinmu?

18 Bitrus ya yi gargaɗi: “Kamar ’yantattu, ba kuwa za ku mori ’yancinku misalin mayafin ƙeta ba, amma kamar bayin Allah ne.” (1 Bitrus 2:16; Galatiyawa 5:13) A yau, iliminmu na gaskiyar Littafi Mai Tsarki ya ’yantar da mu daga koyarwar addinan ƙarya. (Yohanna 8:32) Bugu da ƙari, muna da ’yancin zaɓe, kuma za mu iya zaɓan abin da muke so. Duk da haka, ba ma ƙeta da ’yancinmu. Sa’ad da muke zaɓan waɗanda za mu yi tarayya da su, tufafinmu, ado, da kuma nishaɗi—har ma da abinci da abin sha—muna tuna cewa Kiristoci na gaskiya bayin Allah ne, ba masu faranta wa kansu rai ba. Mun zaɓi mu bauta wa Jehovah maimakon mu zama bayin namu sha’awoyi ko kuma hanyoyin duniya.—Galatiyawa 5:24; 2 Timothawus 2:22; Titus 2:11, 12.

19-21. (a) Yaya muke ɗaukan waɗanda suke da iko a duniya? (b) Ta yaya wasu suka nuna ƙauna ga dukan “ ’yan’uwanci na dukan duniya”? (c) Menene hakkinmu mafi muhimmanci?

19 Bitrus ya ci gaba da cewa: “Ku girmama dukan mutane. Ku ƙaunaci ’yan’uwanci. Ku yi tsoron Allah. Ku girmama sarki.” (1 Bitrus 2:17) Tun da Jehovah ya ƙyale mutane a matsayi na iko, muna ba wa waɗannan mutane daraja da ta cancanta. Muna ma yin addu’a dominsu, saboda su ƙyale mu mu biɗi hidimarmu cikin salama da kuma ibada. (1 Timothawus 2:1-4) Har ila kuma muna ƙaunar “ ’yan’uwanci na dukan duniya.” Muna yin ayyuka domin amfanin ’yan’uwanmu Kiristoci ba domin mu wahalar da su ba.

20 Alal misali, sa’ad da aka wargaza wata ƙasar Afirka domin yaƙi tsakanin ƙabilai, halin Kirista na Shaidun Jehovah ya bayyana. Jaridar Reformierte Presse ta Switzerland ta ba da rahoto: “A shekara ta 1995, ’Yancin Afirka . . . suna tabbatar da saka hannu na dukan coci [a yaƙin] Shaidun Jehovah ne kawai ba su saka hannu ba.” Sa’ad da labaran wannan bala’in ya isa kunne duniya, Shaidun Jehovah a Turai babu ɓata lokaci suka aika da abinci da magunguna ga ’yan’uwansu a wannan ƙasar. (Galatiyawa 6:10) Sun bi kalmomin Misalai 3:27: “Kada ka hana alheri ga waɗanda ya wajibce su, lokacin da yana cikin ikon hannunka da za ka aika.”

21 Har ila, akwai hakki mafi muhimmanci fiye da daraja da za mu ba wa masu iko har ma fiye da ƙauna da za mu nuna wa ’yan’uwanmu. Menene wannan? Bitrus ya ce: “Ji tsoron Allah.” Muna da hakki ga Jehovah fiye da yadda muke da shi ga kowanne mutum. Ta yaya wannan ya kasance gaskiya? Kuma ta yaya za mu daidaita wannan hakki ga Allah da hakkin da muke da shi ga masu iko? Waɗannan tambayoyin za a amsa su a talifi na gaba.

Ka Tuna?

• Waɗanne hakki ne Kiristoci suke da shi cikin iyali?

• Ta yaya za mu nuna halin bayarwa a cikin ikilisiya?

• Wane hakki muke da shi ga masu sarauta?

• Waɗanne amfani ne suke zuwa daga riƙe mizananmu na ɗabi’a?

[Hoto a shafi na 19]

Ta yaya iyalan Kirista za su kasance tushen farin ciki mai yawa?

[Hotuna a shafi na 20]

Me ya sa Shaidun Jehovah suke ƙaunar juna?

[Hotuna a shafi na 20]

Za mu iya nuna wa ’yan’uwanmu ƙauna ko ma ba mu san su ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba