“Na Naƙasa Yanzu Amma Ba Har Abada Ba!”
Sara van der Monde ce ta ba da labarin
Mutane suna yawan gaya mini, “Sara, murmushinki yana da ban sha’awa. Me ya sa kike farin ciki kullum?” Sai na gaya musu cewa ina da bege na musamman. A taƙaice, “Na naƙasa yanzu, amma ba har abada ba!”
A N HAIFE ni a shekara ta 1974 a birnin Paris, a ƙasar Faransa. Mahaifiyata ta samu matsala sosai sa’ad da za ta haife ni, kuma daga baya likitoci suka ce ina da ciwon ƙwaƙwalwa. Na kuma samu ciwon farfaɗiya kuma ina yin ciwo a kai a kai.
Sa’ad da nake ’yar shekara biyu, iyali ta ta ƙaura zuwa birnin Melbourne, a ƙasar Ostereliya. Shekaru biyu bayan hakan, Mahaifi na ya gudu ya bar ni da mahaifiyata. Wannan ne lokaci na farko da na taɓa kusantar Allah. Mahaifiyata Mashaidiyar Jehobah ce, kuma tana kai ni taron Kirista a kai a kai, inda na koya cewa Allah yana ƙaunata kuma yana kula da ni. Sanin wannan da kuma ƙaunar da Mahaifiyata take mini sun taimaka mini na ji cewa ina da kāriya duk da cewa yanayinmu ya canja.
Mahaifiyata ta kuma koya mini yadda ake addu’a ga Jehobah. A gaske, yin addu’a ya fi yin magana sauƙi a gare ni. Sa’ad da nake addu’a, ba na bukatar furta kalamin, amma ina “jinsu” dalla-dalla a cikin zuciyata. Kuma domin kalmomi na suna da wuyar fahimta, ina samun ƙarfafa don sanin cewa Jehobah yana fahimtar kome, ko na furta su a cikin zuciyata ko da gargada.—Zab. 65:2.
Jimrewa da Matsaloli
Sa’ad da nake ’yar shekara biyar, ciwon ƙwaƙwalwata ta yi tsanani sosai har ina bukatar yin amfani da na’ura don yin tafiya. Kuma ina yin tafiya da kyar! Sa’ad da nake ’yar shekara sha ɗaya, ban iya tafiya kuma ba. Daga baya, ban iya hawa da kuma sauƙa daga gado ba sai da taimakon wani na’ura mai amfani da lantarki da ke ɗaga ni ya ɗaura a kan keken guragu ta, sai kuma na tuƙa ta.
A gaskiya, a wasu lokatai, ciwo ta tana sa ni baƙin ciki sosai. Amma sai na tuna da abin da iyalinmu ta ƙudurta: “Kada ka damu da abubuwan da ba za ka iya yi ba. Amma ka mai da hankali ga abubuwan da za ka iya yi.” Hakan ya taimaka mini na iya hawan doki da kwalekwale da kuma tuƙa mota a wurin da babu motoci sosai! Ina gwada fasaha ta ta yin zane-zane da ɗinki da zanen gado da yin tangaran.
Domin na naƙasa sosai, wasu sun yi shakka ko zan iya tsai da shawara na bauta wa Allah. Sa’ad da nake ’yar shekara sha takwas, malamata ta gaya mini cewa na “gudu” daga gida don kada mahaifiyata ta rinjaye ni da addininta. Ta ma ce za ta samo mini masauƙi. Amma, na gaya mata cewa ba zan taɓa rabuwa da imani ta ba kuma zan bar gida sa’ad da na tabbata cewa zan iya kula da kaina.
Ba da daɗewa ba bayan wannan aukuwar, na yi baftisma a matsayin Mashaidiyar Jehobah. Shekaru biyu bayan hakan, na ƙaura zuwa wani ƙaramin gida. Na yi farin ciki a wannan gidan sosai, domin na samu taimako da ’yancin da nake bukata.
Tayin da Ban Yi Tsammani Ba
Na fuskanci gwaje-gwaje da yawa ga imani na a cikin shekaru da yawa da suka shige. Amma, na yi mamaki sosai sa’ad da abokin makarantarmu wanda shi ma ya naƙasa, ya gaya mini cewa yana son ya aure ni. Da farko, na yi farin ciki. Domin ina ɗokin samun miji, yadda sauran ’yan mata ma suke yi. Amma duk da haka, da yake wanda ya naƙasa ne kamar ni ne yake son ya aure ni ba tabbaci ba ne cewa za mu yi farin ciki. Bugu da ƙari, shi ba Mashaidi ba ne. Imaninmu da ayyukanmu da maƙasudinmu sun bambanta sosai. Don haka, ta yaya za mu iya kasancewa tare? Na kuma ƙuduri aniyar yin biyayya ga umurnin da Allah ya ba mu cewa mu yi aure cikin Ubangiji kaɗai. (1 Kor. 7:39) Saboda haka, na gaya masa cewa ba zai yiwu ba.
Har yau, na san cewa na tsai da shawara mai kyau. Kuma na tabbata cewa zan yi farin ciki a sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta. (Zab. 145:16; 2 Bit. 3:13) Amma kafin wannan lokacin, na ƙudurta cewa zan ci gaba da kasance da aminci ga Jehobah kuma na yi wadar zuci don yanayin da na tsinci kaina yanzu.
Ina ɗokin ganin ranar da zan yi tsalle daga keken guragu na kuma na yi gudu kamar guguwa. A lokacin zan faɗa da babbar murya, “A dā na naƙasa, amma yanzu ina da cikakkiyar lafiya na har abada!”