Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 12/15 pp. 19-23
  • Ku Daraja Matsayinku Na “Baƙi”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Daraja Matsayinku Na “Baƙi”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “DUKAN TALIKAI SUNA NISHI”
  • ME AKE BUKATA DAGA KIRISTOCI NA GASKIYA?
  • HALI MAI KYAU
  • MU RIƘA YIN BIYAYYA GA HUKUMA
  • MU ƘAUNACI ’YAN’UWA
  • “Baƙi” A Cikin Muguwar Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • “Kuna Al’amura Na Dacewa Wurin Al’ummai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • “Baƙi” Suna Bauta Wa Jehobah Tare
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 12/15 pp. 19-23

Ku Daraja Matsayinku Na “Baƙi”

“Ina roƙonku misalin saukakku, baƙi masu-tafiya kuma, ku hanu daga sha’awoyi na jiki.”—1 BIT. 2:11.

MECE CE AMSARKA?

Me ya sa za mu kira shafaffu baƙi?

Me ya sa za mu ce “waɗansu tumaki” ma baƙi ne?

Mene ne kake jira a nan gaba?

1, 2. Su waye ne Bitrus ya kira “zaɓaɓu,” kuma me ya sa ya ce da su “baƙi masu-tafiya”?

BAYAN kusan shekara 30 da Yesu ya koma sama, manzo Bitrus ya rubuta wasiƙa zuwa ga rukunin da ya kira “zaɓaɓu waɗanda ke saukakku suna warwatse cikin Buntus, da Galatiya, da Kaffadokiya da Asiya, da Butiniya.” (1 Bit. 1:1) Ta yin amfani da kalmar nan “zaɓaɓu,” Bitrus yana maganar waɗanda aka shafa da ruhu mai tsarki kuma aka ‘sake haifarsu zuwa bege mai-rai’ don su yi sarauta da Kristi a sama. (Karanta 1 Bitrus 1:3, 4.) Me ya sa daga baya ya kira waɗannan zaɓaɓun “saukakku, baƙi masu-tafiya”? (1 Bit. 2:11) Me ya sa wannan zai kasance da muhimmanci a gare mu, tun da yake Shaidu kalilan ne a dukan duniya suke da begen zuwa sama?

2 Ya dace da aka kira shafaffu na ƙarni na farko “baƙi masu-tafiya,” domin kamar shafaffu da suke raye a yau, ba za su kasance a duniya har abada ba. Manzo Bulus wanda yake cikin “ƙaramin garke” ya bayyana cewa shafaffu mazaunan sama ne. Ya ce: “Namu yangaranci cikin sama yake; daga can kuwa muna sauraron Mai-ceto, Ubangiji Yesu Kristi.” (Luk 12:32; Filib. 3:20) Hakan yana nufin cewa sa’ad da shafaffu suka rasu, za su bar duniya da Shaiɗan ke mulkinta kuma su koma sama inda ba za su ƙara mutuwa ba. (Karanta Filibiyawa 1:21-23.) Saboda haka, su “baƙi, masu-tafiya” ne tun da yake za su rayu a duniya na ɗan lokaci kawai.

3. Wace tambaya ce ya kamata mu yi game da “waɗansu tumaki”?

3 Amma, “waɗansu tumaki” kuma fa? (Yoh. 10:16) Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa suna da begen zama mazaunan duniya har abada. Amma, me ya sa za a ce suna kamar baƙi a duniya?

“DUKAN TALIKAI SUNA NISHI”

4. Mene ne ya gagari shugabannan duniya?

4 Dukanmu za mu ci gaba da shan wahala domin Jehobah ya ƙyale wannan mugun zamani ya wanzu, don tawayen da Shaiɗan ya yi. Romawa 8:22 ta ce: “Mun sani dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.” Shugabannan duniya da masanan kimiyya da kuma masu aikin ceton al’umma ba su iya kawar da wahala da ’yan Adam suke sha ba.

5. Wane mataki ne mutane da yawa suka ɗauka tun shekara ta 1914, kuma me ya sa?

5 Tun shekara ta 1914, mutane da yawa sun zama talakawan Yesu Kristi wanda Allah ya naɗa Sarki. Ba sa son su zama ’yan duniyar Shaiɗan, kuma sun ƙi su goyi bayanta. Maimakon haka, suna amfani da rayuwarsu da kuma dukiyarsu su goyi bayan Mulkin Allah.—Rom. 14:7, 8.

6. Me ya sa za a kira Shaidun Jehobah baƙi?

6 Shaidun Jehobah ’yan ƙasa ne masu bin doka a sama da ƙasashe 200, duk da haka su baƙi ne a duk inda suke da zama. Ba sa saka hannu a cikin siyasa da zanga-zanga da kuma rikici na ƙasar. A yanzu ma, suna ɗaukan kansu ’yan sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta. Suna farin ciki cewa su baƙi ne a wannan muguwar duniya da ta kusan shuɗewa.

7. Ta yaya bayin Allah za su zama ’yan ƙasa na dindindin, kuma a ina?

7 Nan ba da daɗewa ba, Yesu Kristi zai halaka duniyar Shaiɗan. Gwamnatinsa za ta kawar da zunubi da kuma wahala. Za ta halaka duk wanda ya yi tawaye da sarautar Jehobah. Waɗanda suka kasance da aminci ga Allah za su zama mazaunan Aljanna a duniya har abada. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 21:1-5.) A lokacin, za a ’yantar da talikai daga dukan abin da ke jawo wahala “zuwa cikin ’yancin darajar ’ya’yan Allah.”—Rom. 8:21.

ME AKE BUKATA DAGA KIRISTOCI NA GASKIYA?

8, 9. Mene ne Bitrus yake nufi da mu “hanu daga sha’awoyi na jiki”?

8 Bitrus ya bayyana abin da ake son Kiristoci su yi, sa’ad da ya ce: “Ƙaunatattu, ina roƙonku misalin saukakku, baƙi masu-tafiya kuma, ku hanu daga sha’awoyi na jiki, waɗanda ke yaƙi da rai.” (1 Bit. 2:11) Ya fara ba shafaffu Kiristoci ne wannan shawarar, amma ya kamata waɗansu tumaki na Yesu su bi ta.

9 Ya dace mu gamsar da wasu sha’awoyinmu, muddin mun yi hakan yadda Mahalicci ya ce mu yi. Yin hakan yana sa mu ji daɗin rayuwa. Alal misali, muna son cin abinci mai ɗanɗano da kuma abin sha mai daɗi, kuma mu more cuɗanya da abokan kirki. Ba laifi ba ne mata da miji su gamsar da sha’awar yin jima’i tsakaninsu. (1 Kor. 7:3-5) Amma, Bitrus yana magana game da “sha’awoyi na jiki” ne “waɗanda ke yaƙi da rai.” Wannan yana nufin sha’awoyi na jiki da ba su dace ba. Wasu juyi na Littafi Mai Tsarki sun fassara shi “kwaɗayi na jiki,” (King James Version) ko kuma “sha’awoyi na zunubi” (New International Version). Jehobah ya gaya mana yadda yake son mu yi rayuwa da kuma gamsar da sha’awoyinmu. Bai kamata mu bar sha’awoyi na jiki su ɓata dangantakarmu da Allah ba.

10. A waɗanne hanyoyi ne Shaiɗan yake jaraba Kiristoci don su goyi bayansa?

10 Shaiɗan ba ya son Kiristoci su daraja matsayinsu na “baƙi masu-tafiya” a wannan zamanin. Yana son mu riƙa son abin duniya da yin lalata da zama sanannu da yin ƙoƙari mu kasance kan gaba a kome da muke yi da kuma ƙishin ƙasa. Amma, ya kamata mu fahimci cewa dukan waɗannan sha’awoyi tarkunan Shaiɗan ne. Idan muka ƙudura niyyar mu ƙi waɗannan sha’awoyi, muna nuna sarai cewa ba ruwan mu da muguwar duniya ta Shaiɗan. Muna nuna cewa mu baƙi ne a duniya. Burinmu shi ne mu zama mazauna na dindindin a sabuwar duniya ta Allah. Kuma muna iya ƙoƙarinmu don mu cim ma wannan burin.

HALI MAI KYAU

11, 12. Ta yaya wasu suke ɗaukan baƙi, kuma yaya wasu suke ɗaukan Shaidun Jehobah?

11 Bitrus ya ci gaba da bayyana abin da ake bukatar Kiristoci “baƙi masu-tafiya” su yi. Ya ce a aya ta 12: “Kuna al’amura na dacewa wurin al’ummai; domin, yayinda suke kushenku kamar ma’aikatan mugunta, ta wurin nagargarun ayyukanku da su ke dubawa su ɗaukaka Allah cikin ranar ziyara.” A wasu lokatai, ana kushe baƙi da suke zama a wata ƙasa. Me ya sa? Domin sun fita dabam kuma wasu mutane suna ɗaukansu mugaye. Yadda suke magana da halinsu da adonsu da kuma siffarsu suna iya yin dabam da na ’yan ƙasar. Amma suna iya sa ’yan ƙasar su ga cewa su mutanen kirki ne idan suna da halaye masu kyau.

12 Hakazalika, Kiristoci na gaskiya suna iya yin dabam da maƙwabtansu a yadda suke taɗi ko kuma nishaɗi. Sau da yawa mutane sukan gane su domin adonsu. Saboda haka, wasu mutane suna iya ‘kushen’ Shaidun Jehobah. Amma, wasu suna iya yabonsu domin halinsu na kirki.

13, 14. Ta yaya hikima ta “barata bisa ga ayyukanta”? Ka ba da misali.

13 Halinmu mai kyau zai iya sa wasu su ga cewa ba su da dalilin su ‘kushe’ mu. Mutane sun kushe Yesu, mutumin da ya kasance da aminci sosai ga Allah. Wasu sun kira shi “mutum mai-zarin ci, mai-zarin sha, masoyin masu-karɓan haraji da masu-zunubi!” Amma, ta halinsa mai kyau, Yesu ya nuna cewa shi mutumin kirki ne. Ya ce: “Hikima kuwa ta barata bisa ga ayyukanta.” (Mat. 11:19) Hakan yake a yau. Alal misali, wasu mutane da ke zama kusa da Bethel da ke garin Selters a ƙasar Jamus, suna mamakin irin rayuwa da waɗanda suke hidima a Bethel suke yi. Amma, magajin garin ya yaba wa waɗanda suke hidima a Bethel, ya ce: “Shaidu da suke hidima a wajen suna da nasu salon rayuwa, amma ba sa damun mutane da suke zama a yankin.”

14 An zargi Shaidun Jehobah da suke zama a birnin Moscow da ke ƙasar Rasha, cewa suna munanan abubuwa. Wasu sun ce Shaidun Jehobah suna raba iyalai da ƙarfafa mutane su kashe kansu kuma ba sa son yin jinya sa’ad da suke rashin lafiya. A watan Yuni na 2010, Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam da ke wani birni a ƙasar Faransa ya hukunta cewa bai dace ba da birnin Moscow ya hana Shaidun Jehobah yin bauta, kuma ba su da ikon hana su yin taro. Kotun ya ce kotuna da ke Rasha ba su ba da tabbacin da ya nuna cewa Shaidun suna da munanan halaye ba. Ya ce a wannan batun, waɗannan kotuna sun yi amfani da dokokin birnin Moscow a hanyar da ba ta dace ba.

MU RIƘA YIN BIYAYYA GA HUKUMA

15. Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce Kiristoci na gaskiya a faɗin duniya suke bi?

15 Shaidun Jehobah a faɗin duniya suna yin wani abu da Bitrus ya ce Kiristoci su riƙa yi. Ya ce: “Ku yi biyayya ga kowanne hukunci na mutane sabili da Ubangiji: ko ga sarki, watau na birbishin duka ne; ko kuwa ga masu-mulki.” (1 Bit. 2:13, 14) Ko da yake babu ruwan Kiristoci na gaskiya da wannan muguwar duniya, amma suna yin biyayya ga masu mulki a duk lokacin da dokokinsu ba su saɓa da na Allah ba.—Karanta Romawa 13:1, 5-7.

16, 17. (a) Me ya nuna cewa ba ma son mu yi tawaye da gwamnati? (b) Mene ne wasu shugabannan gwamnati suka amince da shi?

16 Shaidun Jehobah suna rayuwa a matsayin “baƙi masu-tafiya” a wannan zamanin, amma ba sa hakan domin su yi wa gwamnati tawaye ko kuma su zargi wasu mutane. Sun fahimci cewa wasu suna da nasu ra’ayi game da wanda zai yi sarauta ko kuma yadda za a magance matsalolin ’yan Adam. Shaidun Jehobah ba sa sha’anin siyasa ko da yake wasu addinai suna yin hakan. Ba sa ƙoƙarin sa shugabannai su canja yadda suke mulki. Ba sa yin tawaye da gwamnati ko kuma su sa wasu mutane su yi hakan.

17 Bitrus ya ce a “girmama sarki,” shi ya sa Kiristoci suke daraja da kuma ɗaukaka masu mulki ta wajen yi musu biyayya. (1 Bit. 2:17) A wasu lokatai, masu mulki sun yarda cewa ba su da dalilin yi wa Shaidun Jehobah kallon mugaye. Alal misali, wani wanda a dā ministan majalisar gudanarwa a wata jiha da ke Jamus, kuma daga baya ya zama ɗan majalisa na ƙasar ya ce: “Shaidun Jehobah sun nuna halin kirki sa’ad da aka saka su cikin sansani da kurkuku. Shaidun ba su canja imaninsu ba duk da cewa an tsananta musu, kuma sun kasance da kirki ga waɗanda suke fursuna tare.” Ya ce ƙasar Jamus tana bukatar ta nuna waɗannan halaye, musamman yanzu da wasu mutane ba sa nuna halin kirki ga baƙi ko waɗanda imaninsu da ra’ayoyinsu na siyasa ya bambanta.

MU ƘAUNACI ’YAN’UWA

18. (a) Me ya sa ya dace mu ƙaunace dukan ’yan’uwanmu? (b) Mene ne wasu da ba Shaidu ba ne suka ce game da Shaidun Jehobah?

18 Manzo Bitrus ya ce: “Ku ƙaunaci ’yan’uwanci. Ku ji tsoron Allah.” (1 Bit. 2:17) Shaidun Jehobah suna jin tsoron Allah, wato, tsoron ɓata masa rai. Kuma hakan yana ƙarfafa su su yi nufinsa. Suna farin cikin bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwansu a duk faɗin duniya. Yana da wuya mutane a duniyar yau su ƙaunaci wasu, amma Shaidun Jehobah suna ‘ƙaunar dukan ’yan’uwansu.’ Shi ya sa a wasu lokatai, waɗanda ba Shaidu ba suke mamakin yadda muke ƙaunar juna. Alal misali, wata mai aikin kai mutane zagaya da take aiki da wani kamfani a Amirka ta yi mamaki ƙwarai sa’ad da ta ga yadda Shaidun Jehobah suke ƙaunar juna a taron ƙasashe da aka yi a ƙasar Jamus, a shekara ta 2009. Shaidun da ke Jamus sun ƙaunaci ’yan’uwansu daga wasu ƙasashe kuma sun taimaka musu sosai a lokacin ziyararsu. Ma’aikaciyar ta ce ba ta taɓa ganin mutane kamar Shaidun Jehobah ba. Ka taɓa jin mutane suna furta irin waɗannan kalmomin game da Shaidun Jehobah a taron gundumar da ka taɓa halarta?

19. Mene ne ya kamata mu ƙudura niyyar yi, kuma me ya sa?

19 Kamar yadda muka tattauna, Shaidun Jehobah sun nuna a hanyoyi da yawa cewa su “baƙi masu-tafiya” ne a duniyar Shaiɗan. Suna farin cikin yin hakan kuma sun ƙudura niyya su ci gaba. Suna da ƙwaƙƙwarar dalilai na kasancewa da bege cewa nan ba da daɗewa ba, za su zama mazauna na dindindin a sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta. Kana ɗokin shiga wannan sabuwar duniya kuwa?

[Hoto a shafi na 20]

Ba ma goyon bayan duniyar Shaiɗan

[Hoto a shafi na 20]

Muna mara wa sabuwar duniya ta Allah baya

[Hoto a shafi na 22]

Koyarwar Littafi Mai Tsarki ta sa wannan iyali ’yan ƙasar Rasha ta kasance da haɗin kai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba