Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Maris pp. 2-7
  • Ka Inganta Yadda Kake Koyarwa a Waꞌazi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Inganta Yadda Kake Koyarwa a Waꞌazi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MU NUNA MUN DAMU DA MUTANE
  • MU YI AMFANI DA LITTAFI MAI TSARKI
  • MU TAIMAKA MUSU SU SAN JEHOBAH
  • MU CI-GABA DA INGANTA YADDA MUKE KOYARWA
  • Ka Taimaka wa Ɗalibanka Su Zaɓi Bauta wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ku Yi Saurin Taimaka ma Waɗanda Suke da Zuciyar Kirki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Maris pp. 2-7

4-10 GA MAYU, 2026

WAƘA TA 53 Muna Shirin Fita Waꞌazi

Ka Inganta Yadda Kake Koyarwa a Waꞌazi

“Ka nace cikin waꞌazin Kalmar Allah . . . da iyakacin haƙuri da koyarwa.”—2 TIM. 4:2.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abubuwa uku da za su taimaka mana mu inganta yadda muke koyar da mutane a waꞌazi.

1. Mene ne muke bukatar mu yi, kuma me ya sa? (2 Timoti 4:2) (Ka kuma duba hoton.)

YESU ya gaya wa mabiyansa cewa: Ku je ku taimaka wa mutane “su zama almajiraina . . . , ku riƙa koyar da su su yi dukan abubuwan da na umurce ku.” (Mat. 28:​19, 20) Wannan abin da Yesu ya faɗa ya nuna cewa wajibi ne kowanne Kirista ya zama mai koyar da mutane. Gaskiyar ita ce, Jehobah ne yake jawo “dukan waɗanda suke marmarin samun rai na har abada,” kuma malaꞌiku suna taimaka mana mu haɗu da irinsu. (A. M. 13:48; Yoh. 6:44; R. Yar. 14:6) Duk da haka, muna bukatar mu san yadda za mu koyar da mutane game da Jehobah. Ka yi laꞌakari da misalin manzo Bulus da Barnaba. Littafi Mai Tsarki ya ce, yadda “suka yi magana” saꞌad da suke waꞌazi a majamiꞌar da ke Ikoniya, ya sa “Yahudawa da mutanen Girka da yawa suka ba da gaskiya.” (A. M. 14:1) Babu shakka, Bulus da Barnaba sun ƙware sosai wajen koyar da mutane. (Karanta 2 Timoti 4:2.) Kamar Bulus da Barnaba, dukan Kiristoci suna bukatar su ƙware wajen koyar da mutane.

Manzo Bulus yana koyar da mutane a majamiꞌa da ƙwazo. Barnaba kuma yana zaune kusa da shi yana kallon sa yana murmushi.

Za mu iya inganta yadda muke koyar da mutane idan muka yi laꞌakari da yadda Yesu da manzaninsa kamar su Bulus da Barnaba suka koyar da mutane (Ka duba sakin layi na 1)


2. Me ya sa wasu suke ganin kamar ba za su iya inganta yadda suke koyarwa ba?

2 Wasu za su iya ganin kamar ba za su iya inganta yadda suke koyarwa ba domin ba su yi makarantar boko sosai ba. Ko kuma suna ganin ba za su iya bayyana wa mutane abu yadda za su fahimta ba. Wasu ma a Littafi Mai Tsarki sun ga kamar ba za su iya yin aikin da aka ba su ba. (Fit. 4:10; Irm. 1:6) Wasu kuma suna ganin kamar ba za su iya inganta yadda suke koyarwa ba domin su gagara samun ɗalibai ko waɗanda za su saurare su da kyau a waꞌazi. Gaskiyar ita ce, ba kowa ne da muka haɗu da shi a waꞌazi zai so ya saurare mu ba. Kuma ba yadda muke koyarwa ne kawai yake sa mutane su saurare mu ko su ƙi ba. Kamar yadda aka ambata ɗazu, Jehobah da malaꞌikunsa suna taimaka wajen sa mu haɗu da mutanen kirki. Duk da haka, muna bukatar mu riƙa yin waꞌazi yadda mutane za su ji daɗinsa. A talifin nan, za mu ga abubuwa uku da za su taimaka mana mu inganta yadda muke koyar da mutane a waꞌazi.

MU NUNA MUN DAMU DA MUTANE

3. Me ya sa mutane da yawa suka saurari Yesu?

3 Littafi Mai Tsarki ya ce, Yesu “ya san abin da ke cikin zuciyar mutum.” (Yoh. 2:25) Hakan yana nufin cewa Yesu ya san yadda mutane suke tunani, da dalilin da ya sa suke yin abin da suke yi. Abubuwan da Yesu ya koyar sun ratsa zukatan mutane domin ya san abubuwan da suke bukata. Yesu ya san cewa mutanen suna bukatar ja-goranci da ƙarfafa. Me ya sa? Domin shugabannin addinansu sun sa su bi dokoki da alꞌadu da yawa. Kuma hakan ya sa rayuwa bai yi musu sauƙi ba. (Mat. 9:36; 23:4) Saboda haka, a Huɗuba a kan Dutse da Yesu ya yi, ya taimaka wa mutane ta wajen koya musu abubuwan da za su sa su ji daɗin rayuwa. Mutane da yawa sun ji daɗin sauraron Yesu domin ya yi magana a kan abubuwan da ke damunsu.

4. Ta yaya za mu nuna cewa mun damu da mutane? (Ka kuma duba hotunan.)

4 Za mu nuna cewa mun damu da mutane idan muka yi ƙoƙari mu fahimci abubuwan da suke damunsu. Duk wanda muka haɗu da shi a waꞌazi, yana fama da wata matsala da duniyar Shaiɗan ta jawo. Sanin hakan, zai sa mu so taimaka musu. Alal misali, akwai wani abin da ya faru kwanan nan a yankinku da ke tayar wa mutane da hankali? Shin, iyaye suna damuwa cewa wani abu marar kyau zai iya faruwa da yaransu a makaranta? Mutane suna fama da rashin aikin yi? Ka yi tunani a kan irin faman da mutane suke yi, kuma gashi ba su san alkawuran da Allah ya yi a Littafi Mai Tsarki ba.—2 Tim. 3:1; Isha. 65:​13, 14.

Hotuna: Wata ꞌyarꞌuwa tana tunani a kan yanayin mutanen yankinsu yayin da take shirin fita waꞌazi. Na 1. Wata mata ta riƙe yaronta yayin da wani mutum cike da fushi ya ɗaga hannu kamar zai naushe su. Na 2. Wata mata tana shan taba. Na 3. Likita yana gaya ma wata mata da ta tsufa wani abu marar daɗi game da lafiyarta.

Ka yi ƙoƙari ka fahimci yanayin mutanen da kake koyar da su, kuma ka nuna ka damu da su (Ka duba sakin layi na 4)


5. Ta yaya halin Yesu ya yi dabam da na Farisiyawa? (Matiyu 11:​28-30)

5 Yesu ya damu da masu sauraronsa, kuma sun ga hakan ta yadda yake bi da su. Halin Yesu ya yi dabam sosai da na Farisiyawa. Farisiyawan suna ganin sun fi sauran mutane kuma sukan wulaƙanta su! (Mat. 23:13; Yoh. 7:49) Amma Yesu ya daraja mutane kuma ya yi musu alheri. Shi “marar zafin rai ne, mai sauƙin kai,” kuma hakan ya sa ya iya koyar da mutane da kyau. (Karanta Matiyu 11:​28-30.) Mu ma muna bukatar mu riƙa daraja mutanen da muke yi musu waꞌazi, kuma mu yi musu alheri.

6. Ta yaya za mu daraja waɗanda ba sa son su ji saƙonmu ko masu tsananta mana?

6 Wasu mutane ba sa so su ji saƙonmu, wasu kuma suna tsananta mana. Yaya za mu bi da irin mutanen nan? Yesu ya ce idan mutane suka tsananta mana, kada mu rama. A maimakon haka ya ce, “ku yi alheri ga waɗanda suka tsane ku, ku yi ma waɗanda suke tsine muku fatan alheri. Ku yi adduꞌa domin waɗanda suke zagin ku.” (Luk. 6:​27, 28) Zai yi mana sauƙi mu yi wa mutanen da ba sa son su ji saƙonmu alheri idan muka yi tunani game da yanayinsu. Mai yiwuwa, akwai dalilin da ya sa suka ƙi saurarar mu. Gaskiyar ita ce, wasu suna so su hana mu yin waꞌazi ne kwata-kwata. Wasu kuma mai yiwuwa wata matsala ce take sa ba sa son su saurare mu. Wataƙila lokacin da muka same su, suna cikin wani irin yanayi kuma ransu a ɓace. Amma, ko da mene ne ya sa ba sa son su saurare mu, zai yi kyau mu bi shawarar nan: “Bari maganarku ta kasance da alheri da kuma daɗin ji, domin ku san irin amsar da ya yi kyau ku ba kowa.” (Kol. 4:6) Idan muka tausaya wa mutane, kuma muka yi ƙoƙari don mu fahimci yanayinsu, hakan zai sa mu koya musu abin da zai taimaka musu.

MU YI AMFANI DA LITTAFI MAI TSARKI

7. Mene ne Yesu ya yi amfani da shi wajen koyar da mutane? (Yohanna 7:​14-16)

7 Yesu bai koya wa mutane raꞌayinsa ba. Ya koya musu abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki, da yadda abubuwan za su taimaka musu. Kuma ya yi hakan a hanyar da za ta yi wa mutanen sauƙi su tuna da abin da ya faɗa. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa, mutane sun “yi mamakin yadda [Yesu] yake koyarwa, domin yana koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar marubuta ba.” (Mar. 1:22) Marubuta a lokacin suna koya wa mutane abubuwan da wasu sanannun malaman addinai suka faɗa. Amma Yesu ya koya wa mutane abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Ko da yake Yesu ya daɗe yana rayuwa a sama, kuma ya san abubuwa da yawa, bai yi ƙoƙarin burge mutane da abubuwan da ya sani ba, ko kuma ya sa su ga kamar ba su san kome ba. A maimakon haka, ya yi amfani da Kalmar Allah wajen nuna musu abin da Allah yake so su yi. (Karanta Yohanna 7:​14-16.) Wannan misali ne mai kyau Yesu ya kafa wa mabiyansa.

8. Ta yaya Bitrus ya yi koyi da Yesu?

8 Almajiran Yesu ma sun koya wa mutane abin da ke Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Bitrus ya yi amfani da Kalmar Allah saꞌad da yake koyar da mutane a ranar Fentakos na shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu. Duk da cewa Bitrus bai halarci wani sanannen makaranta a lokacinsu ba, yadda ya bayyana Kalmar Allah da kuma annabce-annabce game da Yesu ya ratsa zuciyar masu sauraronsa. (A. M. 2:​14-37) Hakan ya sa “waɗanda suka yarda da maganar Bitrus da dukan zuciyarsu, an yi musu baftisma. A ranar sun sami ƙarin mutane wajen dubu uku.”—A. M. 2:41.

9. Me ya sa ya dace mu yi amfani da Kalmar Allah saꞌad da muke koyarwa?

9 Babu abin da ya kai Kalmar Allah ratsa zukatan mutane. (Ibran. 4:12) Saboda haka, wajibi ne mu yi amfani da Kalmar Allah saꞌad da muke koyar da mutane. Muna bukatar mu koya wa mutane Kalmar Allah ba raꞌayinmu ba. (2 Tim. 4:2) Karin Magana 2:6 ta ce: “Yahweh yana ba da hikima, sani da ganewa ma, daga bakinsa suke fitowa.” Don haka, idan muna koyarwa daga Littafi Mai Tsarki, muna ba wa mutane dama ne su saurari abin da Jehobah ya ce. (Mal. 2:7) Muna son mutane su san cewa shawarwarin da ke Littafi Mai Tsarki sun fi kowace irin shawarar ꞌyanꞌadam. Abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki daga wurin Mahaliccinmu ne. Suna sa mu farin ciki, kuma suna taimaka mana mu san yadda za mu faranta masa rai.—2 Tim. 3:​16, 17.

10. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibinmu ya san cewa abin da yake koya daga Littafi Mai Tsarki ne?

10 Saꞌad da kake shirin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibinka, ka yi tunani a kan nassosin da za su taimaka masa ya gane abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Ka taimaka masa ya san cewa ko da yake hotuna da bidiyoyi suna taimaka mana mu ƙara fahimtar nazarin da muke yi, mun fi mai da hankali a kan abin da ke Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, saꞌad da kuke nazarin Littafi Mai Tsarki, ka karanta ayoyin da za su taimaka wa ɗalibinka ya fahimci muhimman darussan. Idan kuka kalli hotuna ko bidiyoyi, ka taimaka wa ɗalibinka ya fahimci muhimman darussan da suke koyarwa. Hakan ba ya nufin cewa dole ne ku karanta dukan nassosin da ke darasin ko kuma ka yi maganganu da yawa. A maimakon haka, a duk lokacin da kuka karanta wani nassi, ka ba wa ɗalibinka dama ya yi tunani kuma ya fahimci abin da wurin yake faɗa. Idan da bukata za ku iya sake karanta nassin don ya fahimci batun da kyau. Ta hakan, ba abin da ke cikin littafin, ko hoton ko kuma bidiyon ne kawai muke koya wa ɗalibin ba, amma muna koya masa abin da ke Littafi Mai Tsarki.—1 Kor. 2:13.

11-12. (a) Ta yaya za mu nuna cewa muna haƙuri da ɗalibanmu? (Ayyukan Manzanni 17:​1-4) (Ka kuma duba hoton.) (b) Ta yaya za mu taimaka wa mutanen da ba su san Littafi Mai Tsarki kwata-kwata ba?

11 Idan akwai wani batu da ya yi wa ɗalibinka wuyar fahimta, zai yi kyau ka tuna cewa kana bukatar ka koyar da Kalmar Allah “da iyakacin haƙuri.” Yadda mutane dabam-dabam suke fahimtar abu ba ɗaya ba ne. Wasu abubuwan da muke ganin suna da sauƙin fahimta za su iya yi wa ɗalibanmu wuya, kuma zai iya ɗaukan lokaci kafin su gane. Ka tuna cewa, Yahudawa da ke Tasalonika ba su fahimci abin da Bulus yake koyarwa nan da nan ba. Bulus ya yi ta bayyana musu abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki kafin nan wasu suka gane abin da yake koyarwa.—Karanta Ayyukan Manzanni 17:​1-4.

12 Wata hanya kuma da za mu nuna cewa muna haƙuri da ɗalibanmu ita ce da wajen yi musu tambayoyi, da kuma ba su isasshen lokaci don su bayyana raꞌayinsu. Mu saurare su da kyau don mu fahimci dalilin da ya sa suke irin tunanin da suke yi. Saꞌan nan mu karanta kuma mu tattauna wani nassi da zai taimaka musu su fahimci raꞌayin Jehobah game da batun. Wani abu kuma shi ne: Wasu mutane ba su da Littafi Mai Tsarki kuma ba su san abin da ke ciki kwata-kwata ba. Zai yi kyau mu nuna musu Littafi Mai Tsarki. Za mu iya nuna musu sashen nan, “Ka Soma Karanta Littafi Mai Tsarki,” da ke cikin littafin, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Za mu iya karanta nassi ɗaya ko biyu da ke ƙarƙashin “Abin da Zai Taimaka Mana a Rayuwa” don mu nuna musu yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka musu su riƙa yin farin ciki. A taƙaice, idan mun nuna wa ɗalibanmu yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka musu a rayuwa, hakan zai ratsa zuciyarsu.

ꞌYarꞌuwar da aka nuna ɗazu tana nazari da matar da ke shan taba da aka nuna ɗazu. ꞌYarꞌuwar tana saurarawa da kyau yayin da matar take gaya mata yadda take ji.

Wanda ya ƙware a koyarwa yana saurarawa da kyau, kuma ba ya yawan magana (Ka duba sakin layi na 11-12)


MU TAIMAKA MUSU SU SAN JEHOBAH

13. Mene ne burinmu saꞌad da muke nazari da ɗalibanmu? Ka ba da misali.

13 Burinmu shi ne mu taimaka wa ɗalibanmu su san Jehobah kuma su kusace shi. (Yak. 4:8) Za mu iya kwatanta hakan da mai haska wa wani wuta don ya ga abin da yake nema a cikin duhu. Mutumin da ke riƙe da wutar ba zai haska wa kansa wutar ba. A maimakon haka, zai haska wutar a wurin da ake neman abin. Haka ma, saꞌad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane, muna so su mai da hankali a kan abin da suke koya game da Jehobah maimakon a kanmu.

14. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibanmu su yi abin da Allah yake so?

14 Saꞌad da muke nazari da ɗalibanmu, mu taimaka musu su so yin abin da Jehobah yake so. (K. Mag. 27:11) Ba wai kawai muna koya wa ɗalibanmu abubuwan da za su bi ko su guje wa don su zama Shaidun Jehobah ba. A maimakon haka, muna so mu taimaka musu su yi canje-canje don su faranta wa Jehobah rai ne. Alal misali, a ce wani ɗalibinmu yana ƙoƙarin daina wani hali marar kyau, za mu iya yi masa tambayoyin nan: “Me ya sa Jehobah ya tsani wannan halin? Me ya sa Jehobah yake so ka daina wani abin da kake jin daɗinsa? Ta yaya umurnan da Jehobah yake ba mu suke nuna cewa yana ƙaunar ka?” Idan mun taimaka wa ɗalibanmu su riƙa tunani game da Jehobah da kuma halayensa, za su ga cewa Jehobah Uba ne mai ƙauna. Kuma hakan zai taimaka musu su so su yi abubuwan da yake so.

MU CI-GABA DA INGANTA YADDA MUKE KOYARWA

15. Waɗanne abubuwa ne muke bukatar mu yi don mu inganta yadda muke koyarwa?

15 Za mu iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu san abubuwan da muke bukatar mu yi don mu inganta yadda muke koyar da mutane. (1 Yoh. 5:14) Bayan mun yi adduꞌa, zai dace mu bi shawarwarin da ake ba mu a taron ikilisiya game da yadda za mu iya koyar da mutane da kyau. Za mu iya zuwa wurin ɗalibanmu tare da ꞌyanꞌuwan da suka iya koyarwa da kyau, kuma mu ce su gaya mana inda muke bukatar gyara. Ƙari ga haka, mu yi tunani a kan abubuwan da ɗalibanmu suka sani, da waɗanda ba su sani ba. Kuma mu yi tunani a kan yadda za su ji game da batun da muke so mu tattauna da su. Yayin da muke nazarin, mu taimaka wa ɗalibanmu su ga yadda abubuwan da suke koya za su amfane su, da kuma alkawura masu kyau da Jehobah ya yi mana. Yin waɗannan abubuwan zai taimaka wa ɗalibanmu su kusaci Jehobah kuma su yi farin ciki a rayuwa.—Zab. 1:​1-3.

16. Me ya sa yake da kyau mu ci-gaba da inganta yadda muke koyarwa?

16 Ɗaya daga cikin abubuwan da suke sa mu matukar farin ciki a yau shi ne koya wa mutane game da Jehobah. A sabuwar duniya, mutane da yawa za su bukaci su koya game da Jehobah. Saboda haka, mu ci-gaba da nuna cewa mun damu da mutane, mu riƙa amfani da Kalmar Allah saꞌad da muke koyar da su, kuma mu taimaka musu su san kuma su kusaci Jehobah. Yin hakan zai taimaka mana mu inganta yadda muke koyar da mutane a waꞌazi.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya za mu nuna cewa mun damu da mutane?

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki saꞌad da muke koyar da mutane?

  • Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibanmu su san Jehobah sosai?

WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba