Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Maris pp. 8-13
  • Ka Dogara ga Jehobah Mai Iko Duka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Dogara ga Jehobah Mai Iko Duka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SHAIƊAN YA SHIGO INDA SUKE
  • JEHOBAH NE MAI IKO DUKA
  • JEHOBAH YA SA AYUBA YA DAINA SHAN WAHALA
  • JEHOBAH YANA ƘAUNAR BAYINSA MASU AMINCI
  • KA DOGARA GA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARKA
  • Littafin Ayuba Zai Iya Taimaka Mana a Lokacin da Muke Shan Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ta Yaya Za Ka Iya Zama Aminin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Maris pp. 8-13

11-17 GA MAYU, 2026

WAƘA TA 7 Jehobah Ne Ƙarfinmu

Ka Dogara ga Jehobah Mai Iko Duka

Jehobah ne “Mafi Ɗaukaka a dukan duniya.”—ZAB. 83:18.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga dalilin da ya sa za mu ci-gaba da kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana idan muka fuskanci matsaloli yanzu, ko kuma a nan gaba.

1. Waɗanne munanan abubuwa ne suka faru a rayuwar Ayuba?

MUNANAN abubuwa sun faru a rayuwar Ayuba. Ya rasa yaransa da dukiyoyinsa, kuma ya kamu da wata cuta mai tsanani. Ban da haka ma, mutane da yawa sun daina daraja shi. Ƙari ga haka, abubuwan da abokansa uku suka faɗa sun ƙara sa shi sanyin gwiwa. Matarsa ma ta damu sosai har ta ce masa ya zagi Allah ya mutu. (Ayu. 2:9; 15:​4, 5; 19:​1-3) Matsalolin nan za su iya sa Ayuba ya daina dogara ga Jehobah. Kuma ya ga kamar Jehobah ba ya kāre masu ƙauna da kuma bauta masa.

2-3. Yaya za mu iya ji idan muna fuskantar matsaloli, kuma mene ne za mu iya koya daga littafin Ayuba?

2 A wasu lokuta, mu ma muna fuskantar matsalolin da za su iya sa mu daina dogara ga Jehobah. Muna rayuwa a kwanakin ƙarshe da ake ‘shan wahala sosai.’ (2 Tim. 3:1) Idan muna fama da matsaloli da yawa, za mu iya yin baƙin ciki sosai har mu ga kamar tamu ta ƙare. Wasu ma za su iya ganin kamar Jehobah ba ya ƙaunarsu kuma ba ya so ya taimaka musu.

3 Idan haka ne kake ji, kada ka karaya. Da shigewar lokaci, Ayuba ya gano cewa Jehobah ba ya watsi da masu bauta masa da aminci. Mu ma za mu iya dogara ga Jehobah, kuma mu kasance da tabbaci cewa zai taimaka mana kuma ya albarkace mu. Talifin nan zai taimaka mana mu ga yadda za mu iya yin hakan. Za mu ga yadda littafin Ayuba ya nuna mana cewa, za mu iya dogara ga Jehobah domin shi ne Mafi Ɗaukaka. Za mu kuma ga cewa Jehobah yana da iko ya sa abubuwa su kasance daidai yadda yake so. Kuma zai taimaka mana mu iya riƙe amincinmu.

SHAIƊAN YA SHIGO INDA SUKE

4. Mene ne ya faru saꞌad da Jehobah da malaꞌiku suka taru a sama?

4 Wata rana, malaꞌiku sun taru a gaban Jehobah a sama. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shaiɗan ma ya zo tare da su.” (Ayu. 1:6) Wannan shi ne karo na farko da aka kira babban magabcin Jehobah da sunan nan, “Shaiɗan.” A wannan lokacin, Shaiɗan ba ya cikin malaꞌikun Allah masu aminci. Ya riga ya zama magabcin Jehobah da na malaꞌiku da kuma na ꞌyanꞌadam masu aminci. A Farawa 3:15 Jehobah ya nuna cewa Shaiɗan ba ya cikin iyalinsa na sama. Saboda haka, Shaiɗan ba ya cikin “macen,” wato iyalin Jehobah na sama da aka ce wani daga zuriyarta zai murƙushe kan Shaiɗan.

5. Mene ne abin da ya faru a taron ya nuna game da Shaiɗan da kuma Jehobah?

5 Jehobah ya sa a rubuta abin da ya faru a taron a cikin Littafi Mai Tsarki. Abubuwan da Shaiɗan ya faɗa sun nuna cewa shi mugu ne da kuma maƙaryaci. (Ayu. 1:9; ka kuma duba Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 12:10.) Abin da ya faru a taron ya kuma nuna mana cewa duk da cewa Jehobah Mai Iko Duka ne, yana amfani da ikonsa a hanyar da ta dace. Ƙari ga haka, a matsayinsa na Mai Iko Duka, Jehobah yana sa iyaka a kan abin da wasu za su iya yi, da abin da ba za su iya yi ba.

JEHOBAH NE MAI IKO DUKA

6. Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi ne Mai Iko Duka a taron da aka yi a sama? (Ayuba 1:​7, 8)

6 Karanta Ayuba 1:​7, 8. A taron, Jehobah ya nuna cewa shi ne yake da ikon faɗan abin da zai faru. Jehobah ya tambayi Shaiɗan cewa: “Ka lura da bawana Ayuba?” Jehobah ya riga ya san cewa Shaiɗan yana so ya jarrabci Ayuba. Bari mu ga yadda Jehobah ya yi amfani da ikonsa wajen taimaka wa Ayuba.

7. Bisa ga Ayuba 1:​10, 11, mene ne Shaiɗan ya ce game da mutanen da suke bauta wa Jehobah?

7 Karanta Ayuba 1:​10, 11. Jehobah ne Mafi Ɗaukaka a sama da duniya. Kuma yana da ikon yin duk abin da yake so ya yi. (Irm. 32:17; Dan. 4:35) Duk da haka, Shaiɗan ya ce Jehobah ba ya amfani da ikonsa a hanyar da ta dace. Kuma ya ce Jehobah yana ba wa ꞌyanꞌadam abubuwa masu kyau ne don su bauta masa kamar yadda ya yi wa Ayuba. Abin da Shaiɗan yake nufi shi ne, mutanen da suke bauta wa Jehobah suna yin hakan ne don abubuwan da za su samu daga wurin Jehobah. Mene ne Jehobah ya yi?

8-9. Mene ne Jehobah ya gaya wa Shaiɗan, kuma me ya sa? (Ayuba 1:12) (Ka kuma duba hoton.)

8 Karanta Ayuba 1:12. Jehobah ya bar Shaiɗan ya jarabci Ayuba, don a ga ko abin da Shaiɗan ya faɗa gaskiya ne ko aꞌa. Amma Jehobah ya kafa masa iyaka. Jehobah ya gaya wa Shaiɗan cewa: “Kada ka miƙa hannu ka taɓa [Ayuba]!” Dukan malaꞌikun da ke wurin sun ji dokar nan da Jehobah ya ba Shaiɗan. Kuma dole ne Shaiɗan ya bi dokar nan, domin bai da iko ya yi wa Ayuba fiye da abin da Jehobah ya faɗa. A yau ma, Shaiɗan ba zai iya yi fiye da abin da Jehobah ya ƙyale shi ya yi ba. Jehobah ya yi amfani da ikonsa wajen kāre Ayuba, kuma ya nuna cewa shi Allah ne mai ƙauna da adalci.

9 Duk da cewa Shaiɗan ya hallaka dukan abubuwan da Ayuba yake da su, Ayuba ya ci-gaba da bauta wa Allah da aminci. (Ayu. 1:22) Amma Shaiɗan yana ganin har ila akwai abin da zai iya yi don ya hana Ayuba bauta wa Jehobah.

Shaiɗan yana yi wa Jehobah magana da reni a gaban sauran malaꞌiku.

Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya faɗi abin da ke zuciyarsa a gaban kowa a sama (Ka duba sakin layi na 8-9)


10. Me ya sa Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya sake jarrabtar Ayuba? (Ayuba 2:​2-6)

10 Karanta Ayuba 2:​2-6. A wannan karon, Shaiɗan ya so ya yi wani mugun abu don ya hana Ayuba bauta wa Jehobah. Shaiɗan ya ce idan Ayuba ya ga cewa zai mutu, zai tsani Jehobah kuma ya daina bauta masa. Don a ga cewa abin da Shaiɗan ya faɗa ƙarya ne, Jehobah ya ƙyale shi ya jarrabci Ayuba. A wannan karon kuma, Jehobah ya sake gaya wa Shaiɗan cewa: “Amma fa ka bar ransa!” Shaiɗan bai isa ya kashe Ayuba ba, domin Jehobah ya kafa masa iyaka. Jehobah ya sake nuna cewa shi ne Mai Iko Duka, kuma Shaiɗan ba zai iya yi wa Ayuba fiye da abin da Jehobah ya ƙyale shi ya yi ba.

JEHOBAH YA SA AYUBA YA DAINA SHAN WAHALA

11. Ta yaya Jehobah ya albarkaci Ayuba bayan da ya sa Ayuba ya daina shan wahala? (Ayuba 42:​10-13)

11 Karanta Ayuba 42:​10-13. Da Ayuba ya nuna cewa zai ci-gaba da riƙe amincinsa ko da mene ne ya faru, Jehobah ya sa Shaiɗan ya daina jarrabtar sa. Ta hakan ne Jehobah ya sa Ayuba ya daina shan wahala. Hakan ya kuma nuna mana cewa Shaiɗan ba zai iya hana Jehobah kāre Ayuba da kuma yi masa albarka ba.

12. Ka ba da misalin da ya nuna yadda Jehobah ya ceci wasu bayinsa da suka dogara gare shi.

12 Jehobah ya yi amfani da ikonsa wajen taimaka wa bayinsa da yawa a wannan kwananki na ƙarshe. Alal misali, a 1945 sojoji sun tilasta wa Shaidun Jehobah 230 su yi dogon tafiya mai haɗarin gaske daga wani kurkukun da ke Jamus zuwa wani teku don su kashe su. Amma ba ko ɗayansu da ya mutu. ꞌYanꞌuwan sun rubuta cewa: “Jehobah ya cece su kamar yadda ya ceci Ibraniyawa guda uku da aka jefa a cikin wuta, kuma ko warin hayaƙi ba a ji a jikinsu ba.” Duk da cewa ꞌyanꞌuwan nan sun sha wuya sosai, bangaskiyarsu ta daɗa ƙarfi. Jehobah ya ba su ƙarfin jimrewa. Sun kuma ji kamar Daniyel lokacin da Jehobah ya cece shi daga bakin zakuna. Daga lokacin, sun ƙudura niyyar bauta wa Jehobah har abada, kuma hakan babban gata ne a gare su.—Ka duba Daniyel 3:27; 6:22.

13. Wane tabbaci ne muke da shi game da matsalolinmu? (Ka kuma duba hotunan.)

13 A wasu lokuta, za mu iya fama da matsaloli sosai. (1 Bit. 5:​8-10) Matsalolin za su iya sa mu yi sanyin gwiwa sosai, har mu ji kamar babu mafita. A irin wannan yanayin, labarin Ayuba zai taimaka mana. Zai dace mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana da ikon sa mu daina shan wahala. Kuma zai yi hakan, ko yanzu ko a sabuwar duniya. Jehobah ya riga ya zaɓi lokacin da zai kawo ƙarshen wannan zamanin. Kuma babu abin da zai hana shi yin hakan a daidai lokacin!

Hotuna: Bayin Jehobah suna fama da matsaloli da dama. Na 1. Wani ɗanꞌuwa yana taꞌazantar da wani ɗanꞌuwan da ya tsufa kuma matarsa ta mutu. Su biyun suna tsaye kusa da wani kabari a maƙabarta. Na 2. Wani mutum da matarsa sun zauna kusa da ꞌyarsu da ke kwance a gadon asibiti suna baƙin ciki. Na 3. Wani ɗanꞌuwa da ke kurkuku yana tona rami a cikin zafin rana, kuma wani soja da bindiga yana gadin sa.

Jehobah zai kawo ƙarshe dukan matsalolin bayinsa masu aminci (Ka duba sakin layi na 13)


JEHOBAH YANA ƘAUNAR BAYINSA MASU AMINCI

14-15. Mene ne Jehobah yake so ya yi wa bayinsa masu aminci, kuma me ya sa? (Ayuba 14:15) (Ka kuma duba hoton.)

14 Karanta Ayuba 14:15. Ubanmu na sama yana da dangantaka ta kud da kud da bayinsa masu aminci. Yana ƙaunar su sosai kuma zai ta da su idan suka mutu. Babu shakka, dukanmu za mu yi farin ciki saꞌad da aka ta da matattu a sabuwar duniya.—Isha. 65:17.

15 Duk da cewa Jehobah ya sa Ayuba ya daina shan wahala, Ayuba ya ci-gaba da rayuwa a wannan muguwar duniyar. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ya albarkaci Ayuba sosai. Ya warkar da shi, kuma ya sami abubuwan da suka fi waɗanda yake da su a dā. Waɗannan albarkun soma taɓi ne na abubuwan da Jehobah zai yi masa a nan gaba. Jehobah ya nuna cewa yana son bayinsa masu aminci su yi farin ciki kuma su ji daɗin rayuwa. Jehobah zai sa dukan masu aminci su yi rayuwa har abada a aljanna a duniya. (R. Yar. 21:​3, 4) A matsayinsa na Mai Iko Duka, yana marmarin yin hakan. Sanin cewa Jehobah zai cika alkawarin da ya yi zai taimaka mana mu jimre saꞌad da muke fama da matsaloli!

Ayuba da matarsa a gidansu suna marabtar abokansu da suka zo gai da su. Ayuba yana cikin koshin lafiya kuma ya sa kaya mai kyau.

Bayan da Ayuba ya sha wahala, Jehobah ya albarkace shi da matarsa (Ka duba sakin layi na 14-15)


16. Wane dalili kuma zai iya sa mu dogara ga Jehobah?

16 Ko da yake Jehobah ya albarkaci Ayuba da tsawon rai, daga baya ya mutu. Amma Jehobah zai iya ta da shi daga mutuwa domin shi ne Maɗaukaki Mai Iko Duka. (M. Sha. 32:39) Saboda haka, babu wanda zai iya hana Jehobah ta da bayinsa masu aminci a daidai lokacin da ya shirya.—Rom. 8:​38, 39.

KA DOGARA GA JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARKA

17. Ta yaya muka san cewa Shaiɗan ba zai iya hallaka bayin Jehobah ba?

17 Labarin Ayuba ya nuna mana cewa za mu iya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu. Muna godiya ga Jehobah don bai bar Shaiɗan ya hallaka bayinsa ba! A yau, yadda mutane wajen miliyan tara suke bauta wa Jehobah da aminci na nuna cewa Jehobah ne Maɗaukaki, Mai Iko Duka. Masu mulki da shugabannin addinai da yawa sun yi ƙoƙari su hana bayin Jehobah bauta masa da kuma yin waꞌazi. Amma ba su yi nasara ba, domin Jehobah yana taimaka mana. (Isha. 54:17) Kuma ba abin da zai hana mu gaya wa mutane gaskiya game da Jehobah, da kuma cewa Shaiɗan maƙaryaci ne da ke kakkashe mutane. Ko da za mu mutu, zai dace mu tuna cewa Jehobah zai ta da dukan waɗanda suka riƙe amincinsu.—Hos. 13:14.

18. Me ya sa ba za mu ji tsoron abin da zai faru a nan gaba ba?

18 Idan mun yi tunani a kan labarin Ayuba, hakan zai iya sa mu kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai taimaka mana ko da mene ne ya faru a nan gaba. A lokacin ƙunci mai girma, Shaiɗan da mutanensa za su kai wa bayin Jehobah hari. Domin za su ga kamar bayin Jehobah ba su da wanda zai taimaka musu. Amma kamar yadda Jehobah ya yi amfani da ikonsa don ya taimaka wa Ayuba, ba zai bar Shaiɗan ya hallaka bayinsa ba. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai kawo ƙarshen dukan matsalolin da Shaiɗan ya jawo. Za a jefa Shaiɗan da aljannunsa cikin rami mai zurfi na shekara 1,000. (Luk. 8:31; R. Yar. 20:​1-3) A ƙarshe, Jehobah zai hallaka Shaiɗan da masu goyon bayansa kamar yadda Jehobah ya faɗa tun farko.—Far. 3:15; Rom. 16:20; R. Yar. 20:10.

19. Waɗanne albarku ne Jehobah zai yi ma waɗanda suke dogara gare shi? (Ka kuma duba hoton.)

19 Muna marmarin ganin lokacin da duniya za ta zama Aljanna. A lokacin, za mu zama marasa zunubi, kuma mu yi farin ciki na gaske. Rayuwa za ta yi kyau sosai. Jehobah ya ce: “Ga shi, yanzu zan yi dukan kome sabo!” (R. Yar. 21:5) Mene ne hakan yake nufi? A lokacin, Shaiɗan da aljannunsa ba za su sake sa mutane su yi zunubi ko mugunta ba. Kuma za mu yi farin ciki sosai! Babu wata matsala da za ta sake hana mu yin barci da dare. Waɗanda suka tsira daga yaƙin Armageddon za su ga abubuwan ban mamaki da yawa. Masu rashin lafiya, za su warke. Ƙari ga haka, za a soma ta da waɗanda suka mutu. A lokacin, za mu ji daɗin rayuwa kamar yadda Jehobah ya shirya tun da farko!

ꞌYanꞌuwan da aka nuna ɗazu suna jin daɗi a cikin aljanna. Ɗanꞌuwan da ya tsufa yanzu ya zama saurayi, kuma yana takawa da matarsa. Iyayen suna tafiya tare da ꞌyarsu kuma tana cikin ƙoshin lafiya. Ɗanꞌuwan da aka sa a kurkuku yana zaune a ƙarƙashin wani bishiya kusa da ɗan ƙaramin zaki yana karanta Littafi Mai Tsarki.

Jehobah zai albarkaci bayinsa masu aminci da suka jimre matsaloli a dā (Ka duba sakin layi na 19)


20. Mene ne ka ƙudura niyyar yi?

20 A waɗannan kwanakin ƙarshen, za mu yi fama da matsaloli. Kuma muna bukatar ƙarfin zuciya don mu riƙe amincinmu ga Jehobah. Zai dace mu ƙudura niyyar cewa za mu dogara ga Jehobah Mai Iko Duka kuma mu yi masa biyayya. Bari mu ci-gaba da nuna cewa muna ƙaunar Ubanmu Jehobah. Da kuma nuna cewa dukan abubuwan da Shaiɗan ya faɗa game da Jehobah da kuma bayinsa ƙarya ne. Muna da tabbaci cewa idan muka riƙe amincinmu ga Jehobah, Allah Mai Iko Duka, za mu yi rayuwa mai maꞌana a nan gaba. Domin Jehobah yana marmarin yi wa dukan bayinsa masu aminci albarka!

TA YAYA LABARIN AYUBA YA NUNA CEWA . . .

  • Jehobah ne Mai Iko Duka?

  • Jehobah yana marmarin yi wa bayinsa masu aminci albarka?

  • za mu iya dogara ga Jehobah Mai Iko Duka da dukan zuciyarmu?

WAƘA TA 153 Ka Ba Ni Karfin Hali

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba