TALIFIN NAZARI NA 27
WAƘA TA 79 Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci
Ka Taimaka wa Ɗalibanka Su Zaɓi Bauta wa Jehobah
“Ku tsaya sosai cikin bangaskiyarku . . . kuma da ƙarfi.”—1 KOR. 16:13.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga yadda za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su kasance da bangaskiya kuma su iya yin canje-canje har su soma bauta wa Jehobah.
1-2. (a) Me ya sa wasu ɗalibai suke jinkirin bauta wa Jehobah? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?
AKWAI wasu abubuwan da suka sa ka jinkirin zama Mashaidin Jehobah? Ƙila ka ji tsoro cewa, iyalinka, ko abokanka ko waɗanda kuke aiki tare, za su yi fushi da kai idan ka zama Mashaidin Jehobah. Ko kuma ka ga kamar ba za ka iya yin duk abin da Jehobah ya ce ka yi ba. Idan ka taɓa jin hakan, babu shakka za ka san yadda wasu ɗalibai suke ji, da dalilin da ya sa yakan zama musu da wuya su zama Shaidun Jehobah.
2 Yesu ya san cewa irin abubuwan nan za su iya hana mutum bauta wa Jehobah. (Mat. 13:20-22) Duk da haka, ya ci gaba da taimaka ma waɗanda suka yi jinkirin zama mabiyansa. Kuma ya koya wa almajiransa yadda za su taimaka ma irin waɗannan ta wajen (1) taimaka musu su gane abin da ke hana su samun ci gaba, (2) taimaka musu su ƙara ƙaunar Jehobah, (3) taimaka musu su sa bautar Jehobah farko a rayuwarsu, da kuma (4) taimaka musu su san yadda za su shawo kan kalubale. Saꞌad da muke nazari da ɗalibanmu da littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, ta yaya za mu bi shawarwarin nan da Yesu ya ba wa almajiransa?
KA TAIMAKA WA ƊALIBINKA YA GANE ABIN DA YAKE HANA SHI SAMUN CI GABA
3. Mene ne wataƙila ya hana Nikodimus zama mabiyin Yesu?
3 Nikodimus wani shugaban Yahudawa ne, amma ya yi masa wuya ya zama mabiyin Yesu. Wata shida bayan da Yesu ya soma waꞌazi ne, Nikodimus ya gane cewa shi ne Almasihu. (Yoh. 3:1, 2) Amma Nikodimus ya zaɓi ya yi wa Yesu magana da dare domin yana “tsoron shugabannin Yahudawa.” (Yoh. 7:13; 12:42) Wataƙila yana ganin zai rasa matsayinsa da kuma dukiyarsa idan ya zama mabiyin Yesu.a
4. Ta yaya Yesu ya taimaka wa Nikodimus ya san abin da Allah yake bukata daga wurinsa?
4 Nikodimus ya san Dokar Musa da kyau, amma yana bukatar taimako don ya san abin da Jehobah yake so ya yi. Ta yaya Yesu ya taimaka masa? Yesu ya ba wa Nikodimus lokacinsa. Yana a shirye ya kasance da shi a duk lokacin da za su iya yin hakan, ko da da dare ne. Kuma Yesu ya gaya wa Nikodimus abin da yake bukatar ya yi don ya zama almajirinsa ba ɓoye-ɓoye. Ya ce masa ya tuba daga zunubansa, ya yi baftisma kuma ya ba da gaskiya ga Ɗan Allah.—Yoh. 3:5, 14-21.
5. Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibinka ya san abin da yake hana shi bauta wa Jehobah?
5 Ko da ɗalibinka ya san abubuwa da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki, zai yi kyau ka taimaka masa ya gane abubuwan da suke hana shi samun ci gaba. Mai yiwuwa aikin da yake yi yana ɗaukan lokacinsa sosai, ko iyalinsa ba sa so ya zama Mashaidin Jehobah. Saboda haka, ka ba wa ɗalibinka lokacinka, kamar yadda Yesu ya yi. Kai da ɗalibinka za ku iya zuwa wani wurin da za ku iya zama ku yi hira. Yin hakan zai iya sa ya gaya maka wasu abubuwa game da rayuwarsa, kuma zai taimaka maka ka san wasu matsalolin da yake fuskanta. Ka ƙarfafa ɗalibinka ya yi gyare-gyaren da yake bukata, ba don ya sa ka farin ciki ba, amma don ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah.
6. Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibinka ya sami ƙarfin gwiwar yin abin da yake koya? (1 Korintiyawa 16:13)
6 Idan ɗalibinka yana da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa ya riƙa yin abin da ya dace, hakan zai ba shi ƙarfin gwiwar yin abin da yake koya. (Karanta 1 Korintiyawa 16:13.) Aikin da muke yi yana kama da na malamin makaranta. A lokacin da kake makaranta, wane malami ne ka fi so? Mai yiwuwa ka fi son malamin da yake haƙuri da kai, kuma yana taimaka maka ka san cewa za ka iya cim ma abubuwan da kake so ka yi. Haka ma, malamin Littafi Mai Tsarki da ya ƙware, ba ya koya wa ɗalibinsa abin da Allah yake bukata daga wurinsa kawai. Amma yana tabbatar wa ɗalibin cewa Jehobah zai taimaka masa ya yi canje-canjen da yake so ya yi a rayuwarsa. Ta yaya za ka zama irin malamin nan?
KA TAIMAKA WA ƊALIBINKA YA ƘARA ƘAUNAR JEHOBAH
7. Ta yaya Yesu ya taimaka wa masu sauraron sa su ƙara ƙaunar Jehobah?
7 Yesu ya san cewa idan mutum yana ƙaunar Allah, zai so ya yi abin da yake koya. A yawancin lokuta, yana koya wa almajiransa abin da zai taimaka musu su ƙara ƙaunar Ubansa na sama. Alal misali, ya ce Jehobah na kama da uba da ke ba wa yaransa abubuwa masu kyau. (Mat. 7:9-11) Mai yiwuwa, wasu daga cikin masu sauraron sa ba su da irin wannan uban. Ka yi tunanin yadda za su ji saꞌad da Yesu ya ba da misalin wani uba da ya nuna wa ɗansa jinƙai duk da cewa ya yi munanan abubuwa. Wannan misalin da Yesu ya bayar ya taimaka wa mutane su ga cewa Jehobah yana ƙaunar su kuma yana so ya taimaka musu.—Luk. 15:20-24.
8. Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibinka ya ƙara ƙaunar Jehobah?
8 Kai ma za ka iya taimaka wa ɗalibinka ya ƙara ƙaunar Jehobah, ta wajen gaya masa game da halayen Jehobah masu kyau a kai a kai. A duk lokacin da kuke nazari, ka taimaka masa ya ga yadda abin da yake koya ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunar sa. Saꞌad da kuke tattaunawa game da fansa, ka taimaka wa ɗalibinka ya gane cewa Jehobah ya ba da fansar ne domin yana ƙaunar sa. (Rom. 5:8; 1 Yoh. 4:10) Idan ɗalibi ya fahimci irin ƙaunar da Jehobah yake masa, hakan zai taimaka masa ya ƙara ƙaunar Jehobah sosai.—Gal. 2:20.
9. Mene ne ya taimaka ma wani mutum mai suna Michael ya yi canje-canje a rayuwarsa?
9 Ka yi laꞌakari da labarin Michael daga Indonisiya. An koya masa gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, amma bai yi baftisma ba. Da ya kai shekara 18, ya je ƙasar waje don ya yi aikin tuki. Daga baya sai ya dawo gida ya yi aure, amma sai ya bar iyalinsa ya koma ƙasar waje. Ana nan, sai matarsa da ꞌyarsa suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma sun sami ci gaba. Bayan da mahaifiyarsa ta mutu, sai Michael ya yanke shawarar dawowa gida ya kula da mahaifinsa. A nan ne ya amince a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Saꞌad da suka iso sashen “Ka Yi Bincike Sosai” a darasi na 27 na littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Abin da ke wurin ya ratsa zuciyar Michael. Da ya yi tunani a kan yadda Jehobah ya ji saꞌad da ya ga Ɗansa yana shan wahala a duniya, sai Michael ya fashe da kuka. Wurin ya sa ya fahimci irin ƙaunar da Jehobah da kuma Yesu suke masa. Hakan ya sa ya ƙara nuna godiya, kuma ya yi canje-canje a rayuwarsa har ya yi baftisma.
KA TAIMAKA WA ƊALIBINKA YA SA BAUTAR JEHOBAH FARKO A RAYUWARSA
10. Ta yaya Yesu ya taimaka wa almajiransa su san abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsu? (Luka 5:5-11) (Ka kuma duba hoton.)
10 Wasu mutane da Yesu ya yi musu waꞌazi sun gane a tāke cewa shi ne Almasihu. Amma sun bukaci taimako don su sa yin waꞌazi ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarsu. Kafin Yesu ya gaya wa Bitrus da Andarawus su soma bin sa na cikakken lokaci, sun riga sun amince da shi da kuma koyarwarsa. (Mat. 4:18, 19) Su da Yakub da Yohanna suna aikin kamun kifi, kuma da alama suna samun ci gaba a aikin. (Mar. 1:16-20) A lokacin da Bitrus da Andarawus “suka bar kayansu na kama kifi,” ba mamaki sun shirya yadda iyalansu za su riƙa samun abin biyan bukata yayin da suke bin Yesu. Me ya sa suka bar aikin da suke yi don su sa aikin waꞌazi a kan gaba? Yesu ya yi wani abin ban mamaki da ya nuna musu cewa Jehobah zai iya tanadar musu da abin da suke bukata a kowane lokaci.—Karanta Luka 5:5-11.
Me za mu iya koya daga yadda Yesu ya taimaka wa almajiransa su yi canje-canje don su iya sa yin waꞌazi farko a rayuwarsu? (Ka duba sakin layi na 10)b
11. Ta yaya za ka yi amfani da labarinka ka taimaka wa ɗalibinka ya ƙarfafa bangaskiyarsa?
11 Ba za mu iya yin abubuwan ban mamaki kamar yadda Yesu ya yi ba, amma za mu iya gaya wa mutane game da yadda Jehobah yake taimaka ma waɗanda suka sa bautarsa a kan gaba a rayuwarsu. Alal misali, ka tuna yadda Jehobah ya taimaka maka saꞌad da ka soma halartan taro? Mai yiwuwa ka sami maigidanka a wurin aiki, kuma ka bayyana masa cewa za ka daina yin aiki bayan an tashi don ka iya halartan taro. Yayin da kake gaya wa ɗalibinka abubuwan da ka fuskanta, ka bayyana masa yadda ganin taimakon Jehobah ya ƙarfafa ka saꞌad da ka sa bautarsa a kan gaba.
12. (a) Idan za ka je yin nazari da ɗalibinka, me ya sa zai dace ka je da ꞌyanꞌuwa dabam-dabam? (b) Ta yaya za ka yi amfani da bidiyoyinmu da kyau wajen koyar da ɗalibinka? Ka ba da misali.
12 Ɗalibinka zai amfana idan wasu ꞌyanꞌuwa suka gaya masa yadda suka yi wasu canje-canje don su sa bautar Jehobah farko a rayuwarsu. Saboda haka, idan za ka je ka yi nazari da ɗalibinka, ka je da ꞌyanꞌuwa dabam-dabam. Ka gaya musu su bayyana yadda suka soma bauta wa Jehobah da kuma canje-canjen da suka yi don su sa bautar Jehobah farko a rayuwarsu. Ƙari ga haka, kai da ɗalibinka ku yi ƙoƙari ku kalli bidiyoyin da ke sashen “Ka Yi Bincike Sosai” da kuma “Ka Bincika” na littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Alal misali, saꞌad da kuke tattauna darasi na 37, kuma kuka kalli bidiyon Jehobah Zai Biya Bukatunmu, ku tattauna game da bidiyon kuma ka taimaka wa ɗalibinka ya fahimci cewa Jehobah zai taimaka masa idan ya sa bautarsa a kan gaba.
TA YAYA ZA KA TAIMAKA WA ƊALIBINKA YA SHAWO KAN KALUBALE
13. Ta yaya Yesu ya shirya mabiyansa don tsanantawa da za su fuskanta?
13 Yesu ya gaya wa mabiyansa sau da yawa cewa mutane za su tsananta musu, har ma da danginsu. (Mat. 5:11; 10:22, 36) Kuma ba da daɗewa ba kafin ya mutu, ya gaya wa almajiransa cewa za a iya kashe su don suna bauta wa Jehobah. (Mat. 24:9; Yoh. 15:20; 16:2) Ya gaya musu cewa su kasance da hikima saꞌad da suke waꞌazi kuma kada su riƙa gardama da waɗanda ba sa son waꞌazinsu. Ƙari ga haka, ya ce su mai da hankali ga abubuwan da suke yi da kuma faɗa, don su iya ci gaba da yin waꞌazi.
14. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibanmu su yi shiri don tsanantawa? (2 Timoti 3:12)
14 Za mu iya taimaka wa ɗalibinmu ya yi shiri don tsanantawa, ta wurin gaya masa wasu abubuwan da zai iya ji daga wurin abokansa, ko waɗanda suke aiki tare, ko kuma danginsa. (Karanta 2 Timoti 3:12.) Wasu abokan aikinsa za su iya yi masa dariya domin yana ƙoƙari ya yi rayuwar da ta jitu da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki. Wataƙila danginsa ma ba za su yarda da abin da yake koya daga Littafi Mai Tsarki ba. Idan muka tattauna game da tsanantawa da ɗalibanmu tun da wuri, zai taimaka musu su san abin da za su yi idan hakan ya faru.
15. Mene ne zai iya taimaka wa ɗalibinka idan ana tsananta masa a iyali?
15 Idan iyalin ɗalibinka suna tsananta masa, ka taimaka masa yayi tunani a kan dalilin da ya sa suke tsananta masa don yana nazari da Shaidun Jehobah. Mai yiwuwa suna ganin ruɗin sa ake yi, ko kuma suna ganin cewa Shaidun Jehobah ba mutanen kirki ba ne. Yesu ma ya yi fama da hakan, ba dukan ꞌyanꞌuwansa ne suka so abin da yake yi ba. (Mar. 3:21; Yoh. 7:5) Ka koya wa ɗalibinka yadda zai zama mai haƙuri, kuma ya riƙa yi wa mutane magana da alheri, har da ꞌyan iyalinsa.
16. Ta yaya za ka koya wa ɗalibinka ya riƙa bayyana imaninsa a hanyar da ta dace?
16 Ko da danginsa suna so su san abin da yake koya, ba kome ne zai gaya musu nan tāke ba. In ba haka ba, za su gaji da abin da yake faɗa, kuma ba za su so su sake tattaunawa da shi ba. Saboda haka, ka gaya wa ɗalibinka ya riƙa bayyana imaninsa a hanya mai sauƙi, hakan zai sa mutane su saurare shi wani lokaci. (Kol. 4:6) Zai iya nuna wa danginsa dandalinmu, wato jw.org. Hakan zai sa su koyi game da Shaidun Jehobah a lokacin da suke so.
17. Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibinka ya iya amsa wasu tambayoyi game da Shaidun Jehobah? (Ka kuma duba hoton.)
17 Za ka iya yin amfani da sashen nan “Tambayoyin da Ake Yawan Yi” da ke dandalin jw.org, don ka taimaka wa ɗalibinka ya shirya amsoshin tambayoyi da wataƙila danginsa, ko abokan aikinsa za su tambaye shi a hanya mai sauƙi. (2 Tim. 2:24, 25) A duk lokacin da kuka kammala kowane darassi a littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, ku tattauna sashen nan “Wasu Sun Ce” ko “Wani Yana Iya Cewa.” Kai da ɗalibinka ku ɗan gwada yadda zai bayyana ma wani abin da ya yi imani da shi. Kuma idan da bukata, ka taimaka masa ya ga wasu hanyoyin da zai iya bayyana imaninsa da kyau. Irin wannan gwajin zai iya taimaka masa ya gaya wa mutane abin da ya yi imani da shi babu tsoro.
Ki taimaka wa ɗalibarki ta san yadda za ta bayyana imaninta ta wurin gwada yadda za ta yi hakan a lokacin da kuke nazari (Ka duba sakin layi na 17)c
18. Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibinka ya soma fita waꞌazi tare da ikilisiya? (Matiyu 10:27)
18 Yesu ya umurci almajiransa su yi waꞌazin labari mai daɗi ga dukan mutane. (Karanta Matiyu 10:27.) Idan ɗalibi ya fara fita waꞌazi tare da ikilisiya ba tare da ɓata lokaci ba, zai ga yadda Jehobah yake taimaka masa kuma hakan zai sa ya ƙara dogara gare shi. Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibinka ya soma yin waꞌazi tare da ikilisiya? Idan za a je waꞌazi na musamman a yankinku, kamar lokacin gayyatar mutane zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu ko Taron Yanki, ka yi ƙoƙari ka taimaka wa ɗalibinka ya ga matakin da zai iya ɗauka don ya zama mai shela. Ka bayyana masa cewa yin waꞌazi a irin wannan lokacin yana da sauƙi. Wani abu kuma da za ka iya ƙarfafa shi ya yi shi ne, ya ba da sunansa don ya soma yin aiki a taron tsakiyar maƙo. Yin irin ayyukan nan zai taimaka masa ya san yadda zai riƙa bayyana imaninsa babu tsoro.
KA NUNA WA ƊALIBINKA CEWA KA YARDA DA SHI
19. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya yarda da almajiransa, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?
19 Kafin Yesu ya koma sama, ya gaya wa almajiransa cewa wata rana za su sake haɗuwa. Ba su gane cewa Yesu yana magana ne game da lokacin da za su je sama ba. Duk da haka, Yesu yana da tabbaci cewa suna so su yi abin da Jehobah yake so. (Yoh. 14:1-5, 8) Ya san cewa zai daɗe kafin su fahimci wasu abubuwa, kamar batun begensu na yin rayuwa a sama. (Yoh. 16:12) Mu ma, za mu iya tabbatar wa ɗalibanmu cewa, mun san suna so su yi abin da Jehobah yake so.
Idan ɗalibi ya fara fita waꞌazi tare da ikilisiya ba tare da ɓata lokaci ba, zai ga yadda Jehobah yake taimaka masa kuma hakan zai sa ya ƙara dogara gare shi
20. Ta yaya wata ꞌyarꞌuwa a Malawi ta nuna cewa ta yarda da ɗalibarta?
20 Ka kasance da tabbaci cewa ɗalibinka yana so ya yi abin da Jehobah yake so. Ka yi laꞌakari da labarin wata ꞌyarꞌuwa a Malawi mai suna Chifundo. Ta soma nazari da wata ꞌyar Katolika mai suna Alinafe da littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Da suka gama darasi na 14, sai Chifundo ta tambayi ɗalibarta raꞌayinta game da yin amfani da gumaka a ibada. Alinafe ta yi fushi ta ce: “Ni ne zan zaɓa ko zan yi amfani da gumaka ko aꞌa!” Chifundo ta ɗauka cewa Alinafe za ta daina yin nazari, amma hakan bai faru ba. Ta ci gaba da nazari da Alinafe da fatan cewa a kwana a tashi, za ta fahimci abin da take ƙoƙarin gaya mata. ꞌYan watanni bayan haka, saꞌad da suke nazarin darasi na 34, Chifundo ta yi wa Alinafe tambayar da ke ƙarƙashin batu na shida da ta ce: ‘Ta yaya kika amfana tun lokacin da kika soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma koya game da Jehobah?’ Sai Alinafe ta ambata abubuwa da yawa, har da cewa Shaidun Jehobah ba sa yin duk abin da Littafi Mai Tsarki bai amince da shi ba. Ba da daɗewa ba, Alinafe ta daina amfani da gumaka kuma ta cancanci yin baftisma.
21. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibanmu su zaɓi bauta wa Jehobah?
21 Ko da yake Jehobah ne yake sa “shukar ta yi girma,” za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su sami ci gaba. (1 Kor. 3:7) Ba kawai koya musu abin da Allah yake so ne muke yi ba. Muna koya musu yadda za su ƙara ƙaunar Jehobah. Muna kuma taimaka musu su yi wasu canje-canje don su sa bautar Jehobah farko a rayuwarsu. Ƙari ga haka, muna koya musu yadda za su dogara ga Jehobah saꞌad da suke fuskantar kalubale. Idan muka nuna wa ɗalibanmu cewa mun yarda da su, da kuma cewa za su iya yin abin da Jehobah yake so, hakan zai ƙara musu ƙarfin gwiwa, kuma su zaɓi bauta wa Jehobah.
WAƘA TA 55 Kada Ku Ji Tsoron Su!
a Shekaru biyu da rabi bayan Nikodimus ya haɗu da Yesu, ya ci gaba da zama memba na babban kotun Yahudawa. (Yoh. 7:45-52) Wasu mutane suna ganin cewa Nikodimus ya zama mabiyin Yesu ne bayan da Yesu ya mutu.—Yoh. 19:38-40.
b BAYANI A KAN HOTUNA: Bitrus da sauran masu kamun kifin sun bar sanaꞌarsu don su bi Yesu.
c BAYANI A KAN HOTO: Wata ꞌyarꞌuwa tana taimaka wa ɗalibarta ta yi shirin bayyana imaninta a waꞌazi.