Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 11/1 pp. 6-11
  • Aure Mai Daraja A Gaban Allah Da Mutum

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Aure Mai Daraja A Gaban Allah Da Mutum
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Aure Mai Daraja Wanda Yake Cika Bukatu na Doka
  • Auren Al’ada da Na Doka
  • Aurenka Ya Kasance da Daraja
  • Yadda Za Ku Shirya Bikin Auren da Zai Ɗaukaka Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Me Ake Yi a Bikin Daurin Auren Shaidun Jehobah?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Ka Nuna Bangaskiya Ta Yadda Kake Rayuwarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 11/1 pp. 6-11

Aure Mai Daraja A Gaban Allah Da Mutum

“Ana ɗauren aure cikin Kana . . . Aka faɗa ma Yesu da almajiransa, su zo wurin ɗauren aure.”—YOHANNA 2:1, 2.

1. Ga menene labarin Yesu a Kana ya jawo hankalinmu?

YESU da uwarsa, da kuma wasu cikin almajiransa sun san irin farin cikin da aure mai daraja ke kawowa a tsakanin mutanen Allah. Kristi ya sa wani aure ya zama fitacce ta wajen yin mu’ujizarsa na farko a wurin, wanda hakan ya ƙara wa bikin armashi. (Yohanna 2:1-11) Wataƙila ka taɓa halarta kuma ka ji daɗin ɗaurin aure na Kiristocin da suke son su bauta wa Jehobah a matsayin ma’aurata masu farin ciki. Ko kuwa kana sa rai cewa nan gaba kai ma za ka yi irin wannan auren ko kuwa kana son ka taimaka wa wani abokinka don bikin auren shi ko ita ya yi nasara. Menene zai sa a cim ma haka?

2. Wane bayani ne Littafi Mai Tsarki ke ɗauke da shi game da ɗaurin aure?

2 Kiristoci sun fahimci cewa shawarar da ke cikin hurarriyar Kalmar Allah tana taimakawa sosai sa’ad da mace da namiji suke shirin aure. (2 Timothawus 3:16, 17) Hakika, Littafi Mai Tsarki bai bayyana ainihin tsarin ɗaurin auren Kirista ba. Saboda al’adodi da dokokin ƙasa sun bambanta daga wuri da kuma zamani. Alal misali, a Isra’ila ta dā mutane ba sa taruwa don a ɗaura aure. A ranar ɗaurin auren, angon zai kawo amaryarsa cikin gidansa, ko na mahaifinsa. (Farawa 24:67; Ishaya 61:10; Matta 1:24) Wannan matakin da mutane suka gani shi ne ɗaurin auren, ba sai mutane sun taru ba kamar yadda ake yi a yawancin ɗaurin aure a yau.

3. Ga wane aukuwa ne a Kana Yesu ya ba da gudummawa?

3 Isra’ilawa sun yarda cewa wannan matakin shi ne ɗaurin aure. Bayan haka, suna iya yin liyafa kamar yadda aka bayyana a Yohanna 2:1. Yawancin fassaran Littafi Mai Tsarki sun fassara wannan ayar kamar haka: “An yi ɗaurin aure a Kana.” Amma an fassara kalmar ta ainihi kamar haka, “bikin aure” ko kuwa “liyafar aure.”a (Matta 22:2-10; 25:10; Luka 14:8) Labarin ya bayyana dalla-dalla cewa Yesu ya halarci wannan bikin aure na Yahudawa kuma ya ba da gudummawa. Batu mai muhimmanci a nan shi ne, yadda ake ɗaura aure a dā ya bambanta da yadda ake yi a yau.

4. Wane irin aure wasu Kiristoci suke zaɓa, kuma me ya sa?

4 A yawancin ƙasashe a yau, dole ne Kiristocin da suke son su yi aure su cika wasu dokoki na ƙasa. Idan suka yi hakan, za su iya yin aure a kowace hanya da ke bisa doka. Hakan na iya zama ƙaramin biki wanda alƙali, magajin gari, ko kuwa wani mai hidima na addini wanda Ƙasa ta ba ikon yin haka ya shugabanci bikin. Wasu sukan zaɓi su yi aure a wannan hanyar, wataƙila ta wajen gayyatar kaɗan daga cikin ’yan’uwansu ko kuwa abokai Kiristoci su kasance a wurin don zama shaidu, ko kuwa don su shaida murnar wannan biki mai muhimmanci. (Irmiya 33:11; Yohanna 3:29) Hakazalika, wasu Kiristoci suna iya yanke shawara cewa ba za su yi bikin aure mai girma ba ko kuwa liyafa wadda za ta bukaci shiri mai yawa da kuma kuɗi. Maimakon haka, suna iya shirya ’yar ƙaramar liyafa da wasu abokai kaɗan. Ko da menene zaɓenmu, ya kamata mu fahimci cewa wasu ƙwararrun Kiristoci suna iya kasancewa da ra’ayoyin da suka bambanta da namu.—Romawa 14:3, 4.

5. Me ya sa yawancin Kiristoci suke son a ba da jawabin aure sa’ad da suke aure, kuma menene ya ƙunsa?

5 Yawancin Kiristoci ma’aurata sukan zaɓi a yi musu jawabi da aka ɗauko daga cikin Littafi Mai Tsarki a ɗaurin aurensu.b Sun fahimci cewa Jehobah ne ya kafa aure kuma ya yi tanadin shawara mai kyau a cikin Kalmarsa game da yadda aure zai yi nasara da kuma yadda zai kawo farin ciki. (Farawa 2:22-24; Markus 10:6-9; Afisawa 5:22-33) Yawancin ma’aurata suna son abokai da ’yan’uwa Kiristoci su shaida wannan biki na farin ciki. Duk da haka, yaya ya kamata mu ɗauki dokokin ƙasa, tsare-tsare, har da al’adu? Wannan talifin zai tattauna yanayi na ƙasashe dabam dabam. Wasu suna iya bambanta daga waɗanda ka sani ko kuwa wanda ake yi a inda kake da zama. Duk da haka, za ka ga wasu mizanan da ka sani ko kuwa wasu fasaloli masu muhimmanci ga bayin Allah.

Aure Mai Daraja Wanda Yake Cika Bukatu na Doka

6, 7. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga fasaloli na doka game da aure, kuma ta yaya za mu nuna haka?

6 Ko da yake Jehobah ne tushen aure, gwamnati tana da wasu iko a kan abubuwan da waɗanda suke son su yi aure za su yi. Hakan na da kyau. Yesu ya ce: “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, Allah kuma abin da ke na Allah.” (Markus 12:17) Hakazalika, manzo Bulus ya ce: “Bari kowane mai-rai shi yi zaman biyayya da ikon masu-mulki: gama babu wani iko sai na Allah; ikokin da ke akwai kuma sanyayyu ne na Allah.”—Romawa 13:1; Titus 3:1.

7 A yawancin ƙasashe, Kaisar, ko kuwa gwamnati ce take yanke shawarar wanda ya isa yin aure. Da haka, sa’ad da Kiristoci biyu suke son su auri juna kuma suna da izinin yin haka bisa Nassi, suna yin biyayya ga dokar ƙasar game da aure. Wataƙila hakan zai ƙunshi karɓar takardar izini daga wajen ma’aikacin gwamnati da aka ba ikon yin haka, kuma a yi wa auren rajista. Sa’ad da Kaisar Augustus ya ce a je a yi “rubutu” wato, yin rajista, Maryamu da Yusufu sun bi wannan umurnin, kuma suka je Baitalahmi don su ‘rubuta kansu.’—Luka 2:1-5.

8. Ta yaya ne aure zai zama na dindindin, kuma menene Shaidun Jehobah suke yi da ya nuna haka?

8 Sa’ad da Kiristoci suka yi aure a bisa doka, wannan dangantakar ta zama na dindindin a gaban Allah. Da haka, Shaidun Jehobah ba sa maimaita aure ta wajen ɗaura aure da ke bisa doka sau biyu, kuma ba sa maimaita alkawarin da suka ɗauka na aure, kamar a ranar tuna bikin aure na shekara 25 ko 50. (Matta 5:37) (Wasu coci sun yi watsi da ɗaurin aure da ke bisa doka ta gwamnati, suna da’awar cewa auren ba ya bisa ƙa’ida sai idan firist ko limami ya yi wasu abubuwa na al’ada ko kuwa sai ya ce sun zama mata da miji.) A yawancin ƙasashe, gwamnati ce take ba wani mai hidima na Shaidun Jehobah ikon haɗa aure. Idan ya yiwu, zai so ya yi hakan tare da ba da jawabin aure a Majami’ar Mulki. Wannan shi ne wurin da ake bauta ta gaskiya kuma wurin da ya dace a ba da jawabi game da wannan tsari da Jehobah Allah ya kafa.

9. (a) Game da aure na bisa doka ta gwamnati, menene Kiristoci ma’aurata za su iya yi? (b) Ta yaya dattawa za su iya saka hannu a shirin auren?

9 A wasu ƙasashen, doka ta ce waɗanda suke son su yi aure suna bukatar su yi haka a ofishin gwamnati, kamar babban ɗakin taro, ko kuwa a gaban wani zaɓaɓɓen ma’aikacin gwamnati. A yawancin lokaci Kiristoci sukan zaɓi a ba da jawabin aure a Majami’ar Mulki bayan sun cika bukatu na doka a rana guda ko a washegari. (Ba za su bari kwanaki su wuce ba tsakanin aure bisa doka ta gwamnati da kuma jawabin na Littafi Mai Tsarki, domin sun zama mata da miji a gaban Allah da mutum, da kuma ikilisiyar Kirista.) Idan ma’aurata da za su yi aure na bisa doka ta gwamnati suna son a ba da jawabin aurensu a wata Majami’ar Mulki, ya kamata su nemi izinin yin haka daga dattawan da sune Kwamitin Hidima na Ikilisiyar. Bayan sun tabbatar da cewa waɗanda za su yi auren suna da suna mai kyau, waɗannan masu kula za su tabbatar da cewa lokacin ɗaurin auren ba zai shafi taro ba da kuma tsarin ayyuka na majami’ar. (1 Korinthiyawa 14:33, 40) Za su duba irin shirin da waɗanda za su yi auren suka ce za su yi wa majami’ar kuma za su yanke shawarar ko zai dace a sanar da haka.

10. Idan za a yi aure da ke bisa doka ta gwamnati, ta yaya ne hakan zai shafi jawabin aure?

10 Dattijon da zai ba da jawabin auren ya ƙoƙarta ya ba da jawabin yadda zai daɗaɗa zuciya, ya ƙarfafa ruhaniya, da kuma daraja. Idan an riga an haɗa ma’auratan a bisa doka ta gwamnati, mai jawabin zai bayyana sarai cewa sun riga sun yi aure a bisa dokar Kaisar. Idan ba su ɗauki alkawarin aure ba a lokacin da suka yi aure a bisa doka ta gwamnati, ma’auratan za su iya yin haka a lokacin jawabin.c Idan sun riga sun ɗauki alkawari a lokacin da suka yi aure na bisa doka ta gwamnati, kuma sababbin ma’auratan suna son su sake ɗaukan alkawari a gaban Jehobah da ikilisiya, za su yi haka ta wajen yin amfani da furcin da zai nuna cewa an riga an “gama” su.—Matta 19:6; 22:21.

11. A wasu wurare, yaya mace da na miji suke yin aure, kuma ta yaya hakan zai shafi jawabin auren?

11 A wasu ƙasashe, dokar ƙasar ba za ta bukaci ma’auratan su je su tara mutane don ɗaurin aure ba, har ma a gaban ma’aikacin gwamnati. Auren ya ɗauru ne sa’ad da suka gabatar da takardar ɗaurin aure wanda aka sa hannu ga ma’aikacin gwamnatin. Bayan haka, za a yi rajistan takardar ɗaurin aure. Da haka, mutanen sun zama mata da miji, kuma kwanan watan da ke kan takardar aurensu shi ne ranar ɗaurin aurensu. Kamar yadda aka ambata a baya, wataƙila waɗanda suka yi auren za su so a ba da jawabi da ke bisa Littafi Mai Tsarki nan da nan bayan an yi rajistan a Majami’ar Mulki. Ƙwararren ɗan’uwan da aka zaɓa ya ba da jawabin zai sanar da waɗanda suka hallara cewa ma’auratan sun riga sun yi aure domin rajistar da suka yi. Duk wani alkawarin da za a ɗauka, za a yi shi ne kamar yadda aka bayyana a sakin layi na 10 da kuma hasiya. Waɗanda suka hallara a Majami’ar Mulkin za su yi murna da ma’auratan kuma za su amfana daga shawarar da aka bayar daga Kalmar Allah.—Waƙar Waƙoƙi 3:11.

Auren Al’ada da Na Doka

12. Menene auren al’ada, kuma menene ya kamata a yi bayan auren?

12 A wasu ƙasashe, mata da miji suna yin irin auren da ake kira auren al’ada. Wannan ba ya nufin mutane biyu da suke zaune tare da ba su yi aure ba, ko kuma mutane biyu da suka yi shekaru da yawa suna zaune tare, amma auren ba na bisa doka ba ne.d Muna magana ne game da auren al’ada wanda sananne ne ga wani yare ko wuri. Wannan ya ƙunshi biyan sadaki, wanda hakan zai nuna cewa ma’auratan sun yi aure bisa doka da kuma Nassi. Gwamnati ta ɗauki irin wannan aure na al’ada a matsayin wanda aka yi bisa doka, ingantacce, kuma ba ya canjawa. Bayan haka, ya kamata a yi rajistar auren al’adar da aka yi, kuma ma’auratan za su iya karɓar takardar shaida bayan haka. Takardar za ta iya zama kāriya ga ma’auratan ko kuwa matar da kuma ’ya’yan da za su haifa nan gaba sa’ad da mijin ya rasu. Ikilisiyar za ta umurci duk wanda ya yi irin wannan aure na al’ada ya je ya yi rajistar aurensa nan da nan. Kamar ma a ƙarƙashin Dokar Musa, ana yin rajistar aure da haihuwa.—Matta 1:1-16.

13. Bayan auren al’ada, menene zai sa a ba da jawabin aure?

13 Mutane biyu da suka yi irin wannan auren na al’ada sun zama mata da miji ke nan. Kamar yadda aka ambata a baya, Kiristocin da suka yi irin wannan auren suna iya so a ba da jawabin aurensu, tare da ɗaukan alkawarin aure a Majami’ar Mulki. Idan aka yi haka, mai jawabin zai bayyana cewa ma’auratan sun riga sun yi aure bisa dokar Kaisar. Jawabi guda ne kawai za a yi. Auren guda ne kawai, wato auren al’ada da ke bisa doka, da kuma jawabi guda da ke bisa Nassi. Yin auren al’ada da kuma jawabin a lokaci guda, idan zai yiwu a rana ɗaya, zai sa a ƙara daraja auren Kirista a yankin.

14. Menene Kirista zai yi idan ana yin aure na al’ada da na doka a inda yake da zama?

14 A wasu ƙasashen da aka amince da auren al’ada, akwai tanadin da aka yi na yin aure a bisa doka ta gwamnati. A yawancin lokaci, ana yin aure na bisa doka ta gwamnati a gaban ma’aikacin gwamnati, kuma hakan zai iya haɗawa da ɗaukan alkawari na aure da kuma saka hannu a takarda. Wasu Kiristoci sun fi son aure na bisa doka ta gwamnati fiye da na al’ada. Ba a bukatar a yi duka biyun, domin duk suna bisa doka. Abin da aka ce a sakin layi na 9 da 10 game da jawabin aure da alkawari sun shafi wannan. Abu mafi muhimmanci shi ne ma’auratan su yi aure a hanya mai daraja a gaban Allah da mutum.—Luka 20:25; 1 Bitrus 2:13, 14.

Aurenka Ya Kasance da Daraja

15, 16. Me ya sa ya kamata daraja ya zama sashe mai muhimmanci a aure?

15 Sa’ad da aka sami matsala a auren sarkin Farisa, babban mai ba da shawara, mai suna Memukan, ya ba da shawara da ke da amfani, wato ‘mata duka su ba da girma ga mazansu.’ (Esther 1:20) A aure na Kirista, ba a bukatar wani sarki ya ba da wannan dokar; mata na bukatar su daraja mazansu. Hakazalika, maza Kiristoci suna ‘ba da girma ga matansu’ kuma suna yaba musu. (Misalai 31:11, 30; 1 Bitrus 3:7) Ba wai sai bayan shekaru masu yawa ba ne za mu soma daraja aurenmu ba. Za mu soma ne nan da nan, wato tun daga ranar ɗaurin auren.

16 Ba mata da mijin ba ne kawai za su nuna daraja a ranar ɗaurin auren. Idan dattijo Kirista zai ba da jawabin aure, ya kamata hakan ya nuna daraja. Za a yi jawabin ne ga ma’auratan. Domin ya daraja su, mai jawabin ba zai gabatar da wasan yara ba. Kuma ba zai faɗi wasu abubuwa da ya sani ba game da matar da mijinta wanda zai iya kunyatar da su da kuma masu sauraro. Maimakon haka, zai zama mai daɗaɗawa da kuma ƙarfafawa, zai bayyana Tushen aure da kuma shawararsa mai muhimmanci. Hakika, idan dattijon ya ba da jawabin aure mai daraja, hakan zai sa auren ya daraja Jehobah Allah.

17. Me ya sa akwai sashen doka a auren Kirista?

17 A wannan talifin ka ga cewa akwai bayanai masu yawa game da aure da ke bisa doka. Wataƙila wasu sashen ba su shafi inda kake zaune ba kai tsaye. Duk da haka, ya kamata dukanmu mu fahimci cewa yana da muhimmanci tsarin aure na Shaidun Jehobah ya nuna daraja ga dokar ƙasa, wato bukatun Kaisar. (Luka 20:25) Bulus ya umurce mu: “Ku ba kowa hakinsa: gandu ga wanda gandu ya wajaba; garama ga mai-garama; . . . bangirma ga wanda ya isa bangirma.” (Romawa 13:7) Hakika, ya kamata Kiristoci su nuna daraja ga tsarin da Allah ya riga ya kafa tun daga ranar ɗaurin aurensu.

18. Wane sashe ne na ɗaurin aure wanda ba tilas ba ne muke bukatar mu mai da wa hankali, kuma a ina za mu iya samun bayani game da wannan batun?

18 Ana yin liyafa bayan an gama ɗaurin aure na yawancin Kiristoci. Ka tuna cewa Yesu ya halarci irin wannan liyafar. Idan za a yi irin wannan liyafar, ta yaya ne shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki za ta taimaka mana mu tabbata cewa liyafar za ta sa a daraja Allah, kuma za ta ɗaukaka sababbin ma’auratan da kuma ikilisiyar Kirista? Talifi na gaba zai tattauna wannan batun.

[Hasiya]

a Ana iya yin amfani kuma da wannan kalmar ga bikin da ba shi da nasaba da aure.—Esther 9:22.

b Shaidun Jehobah suna yin amfani da awutlayi na minti 30 na jawabin aure, mai jigo “Aure Mai Daraja a Idanun Allah.” Yana ƙunshe da shawara mai kyau na Nassi da ke cikin littafin nan Asirin Farinciki Na Iyali da kuma sauran littattafai na Shaidun Jehobah. Jawabin zai taimaka wa waɗanda suke son su yi aure da kuma waɗanda suka halarci ɗaurin auren.

c Sai dai idan dokar ƙasar ta bukaci abin da ya bambanta da wannan, wannan alkawarin da ke daraja Allah ne ake amfani da shi. Na ango: “Ni [sunan angon] na karɓe ki [sunan amaryar] ki zama matata, in yi ƙaunarki kuma in so ki kamar yadda dokar Allah da ke cikin Nassosi Masu Tsarki ta tsara domin maza Kirista, har iyakar rayuwarmu tare cikin duniya bisa ga tsarin aure na Allah.” Na amarya: “Ni [sunan amarya] na karɓe ka [sunan ango] ka zama mijina, in yi ƙaunarka kuma in so ka kamar yadda dokar Allah da ke cikin Nassosi Masu Tsarki ta tsara domin mata Kirista, har iyakar rayuwarmu tare cikin duniya bisa ga tsarin aure na Allah.”

d Hasumiyar Tsaro na 1 ga Mayu, 1962, shafi na 287, ya yi bayani game da irin wannan auren.

Ka Tuna?

• Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga aure bisa doka ta gwamnati da kuma na nassi?

• Idan Kiristoci biyu suka yi aure bisa doka ta gwamnati, menene za su iya yi nan da nan?

• Me ya sa ake ba da jawabin ɗaurin aure a Majami’ar Mulki?

[Hoto a shafi na 6]

A auren Isra’ila ta dā, ango na kawo amaryarsa gidansa ko na ubansa

[Hoto a shafi na 9]

Bayan aure na al’ada, Kiristoci na iya zaɓan a yi musu jawabi a Majami’ar Mulki

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba