Waɗanda Suka Tsufa Suna Taimaka wa Ikilisiya a Hanyoyi da Yawa
Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Connie mai shekaru 83 ta ce: “Ina mamakin yawan abubuwan da na yi saꞌad da nake matashiya. Amma yanzu da na tsufa, ba na iya yin dukan abubuwan da nake iya yi a dā.”
Mai yiwuwa kai ma ba ka iya yin wasu abubuwan da kake yi a dā domin ka soma tsufa. Ko da yake ka yi shekaru kana bauta wa Jehobah da aminci, idan ka gwada abubuwan da ka yi a dā da waɗanda kake yi a yanzu, za ka iya yin baƙin ciki. Idan abin da ke faruwa da kai ke nan, me zai taimaka maka ka daina baƙin ciki?
ABIN DA JEHOBAH YAKE BUKATA A GARE KA
Ka tambayi kanka, ‘Mene ne Jehobah yake bukata daga wurina?’ Abin da ke Maimaitawar Shariꞌa 6:5, zai iya ƙarfafa ka. Wurin ya ce: “Ku ƙaunaci Yahweh Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku.”
Ayar ta nuna cewa, Jehobah yana so ka bauta masa da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka. Sanin hakan zai taimaka maka kada ka riƙa gwada abin da kake yi da abin da wasu suke yi, ko kuma ka gwada abin da kake yi yanzu da abin da ka yi a dā.
Saꞌad da kake matashi, babu shakka ka bauta wa Jehobah da dukan zuciyarka. Kuma ko da yake yanzu ka tsufa, kana kan bauta masa da dukan zuciyarka. Idan ka yi tunani a kan hakan, mai yiwuwa za ka ga cewa har ila yadda kake bauta wa Jehobah bai canja ba. Yadda kake iya ƙoƙarinka a dā, haka ma kake yi a yanzu.
Ka yi ƙoƙari a bautar Jehobah a lokacin da kake da ƙarfi, yanzu da ka tsufa ma, kana iya ƙoƙarinka
ZA KA IYA TAIMAKA WA MUTANE SOSAI
Maimakon ka riƙa yin tunani a kan abubuwan da ba ka iya yi yanzun da ka tsufa, ka yi tunani a kan yadda za ka yi amfani da hikimar da ka samu da shigewar lokaci wajen taimaka wa mutane. Ban da haka, akwai wasu abubuwan da za ka iya yi yanzu da a dā ba za ka iya yi ba. Ga wasu abubuwan da za ka iya yi yanzu:
Ka gaya wa mutane wasu abubuwan da ka koya a rayuwa. Ka yi tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a nassosin da ke gaba:
Sarki Dauda ya ce: “Dā dai ni yaro ne, yanzu kam na tsufa, amma ban taɓa ganin Yahweh ya yashe mai adalci ba, ko kuwa a ga ꞌyaꞌyansa suna roƙon abinci.”—Zab. 37:25.
Joshuwa ya ce: “Yanzu ina dab da bin hanyar da kowa a duniya yakan bi. Kowannenku ya sani a zuciyarsa da ransa cewa Yahweh Allahnku ya ba ku dukan abubuwa masu kyau waɗanda ya yi muku alkawari. Kowane alkawarin da ya yi muku ya cika, ba ko ɗayan da ya kāsa cikawa.”—Yosh. 23:14.
Mai yiwuwa kai ma ka taɓa faɗan wani abu makamancin haka don ka ƙarfafa mutane. Amma da yake Dauda da Joshuwa sun shaida abubuwan da suka faɗa tun daga lokacin da suke matasa har suka tsufa, hakan ya sa abin da suka faɗa sun daɗa ƙarfafa masu jin su.
Idan ka daɗe kana bauta wa Jehobah, za ka iya gaya wa mutane game da yadda Jehobah ya taimaka maka da kuma bayinsa. Shin, ka tuna da wani lokacin da Jehobah ya taimaka wa bayinsa a wata hanya ta musamman? Ka gaya wa ꞌyanꞌuwa labarin! Irin labaran nan za su ƙarfafa ꞌyanꞌuwa maza da mata sosai.—Rom. 1:11, 12.
Wata hanya kuma da za ka iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa ita ce ta wurin halartar taro a Majamiꞌar Mulki a duk lokacin da hakan zai yiwu. ꞌYanꞌuwa da suke ganin ka za su sami ƙarfafa, kuma su ma za su ƙarfafa ka. ꞌYarꞌuwa Connie da aka ambata ɗazu ta ce: “Halartan taro a Majamiꞌar Mulki yana taimaka mini kada in yi sanyin gwiwa. Zai yi wuya in yi sanyin gwiwa idan ina tare da ꞌyanꞌuwana masu ƙauna a taro. Kuma nakan nuna godiyata ta wajen ba su ƙananan kyaututtuka. Ina tabbata cewa nakan yi abubuwan ibada tare da ꞌyanꞌuwa.”
JEHOBAH YANA JIN DAƊIN YADDA KAKE BAUTA MASA DA AMINCI
A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai labarin mutane da yawa da Jehobah ya ƙaunace su duk da cewa yanayinsu bai bar su su yi abin da suka saba yi a hidimarsa ba. Ɗaya daga cikinsu shi ne wani mutum mai suna Simeyon. Shi Ba’isra’ile ne, kuma ya tsufa lokacin da aka haifi Yesu. Mai yiwuwa a duk lokacin da Simeyon ya je haikali, yakan ga matasan da suke yin ayyuka masu muhimmanci a wurin. Kuma wataƙila wasu sukan ga kamar ba ya da daraja a gun Jehobah domin ba ya iya yin abubuwan da matasan suke yi. Amma ba haka yake a gun Jehobah ba. A gun Jehobah, Simeyon “mutum mai adalci ne” da ke bauta wa Allah da dukan zuciyarsa. Kuma Jehobah ya ba shi gatan ganin Yesu lokacin da yake jariri. Ban da haka ma, Jehobah ya sa Simeyon ya annabta cewa, Yesu ne Almasihun da aka yi alkawarinsa! (Luk. 2:25-35) Babu shakka, Jehobah bai mai da hankali a kan yadda Simeyon ya tsufa ba. A maimakon haka, ya mai da hankali a kan cewa shi mutum ne mai bangaskiya kuma “ruhu mai tsarki kuwa yana tare da shi.”
Jehobah ya ba wa Simeyon gatan ganin Yesu lokacin da yake jariri kuma ya annabta cewa Yesu ne Almasihun da aka yi alkawarin sa
Kai ma za ka iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana jin daɗin yadda kake bauta masa da aminci duk da cewa yanayinka ya canja. Jehobah ba ya son mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Muddin muna bauta masa iya gwargwadon ƙarfinmu, yana amincewa da hakan.—2 Kor. 8:12.
Saboda haka, ka riƙa mai da hankali a kan abubuwan da za ka iya yi. Alal misali, ka yi tunani a kan hanyoyi dabam-dabam da za ka iya yin waꞌazi ko da na ɗan lokaci ne. Ƙari ga haka, za ka iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa ta wurin kiransu a waya, ko kuma tura musu saƙon gaisuwa. Duk wani abin da kake yi, komen ƙanƙantarsa, zai ƙarfafa ꞌyanꞌuwa, da yake kana yin hakan ne don ka nuna kana ƙaunarsu.
Ko da kana rashin lafiya, Jehobah zai iya amfanin da kai wajen taimaka wa mutane. Ka yi laꞌakari da labarin wata ꞌyarꞌuwa daga Gabashin Afirka da ke akwatin nan mai jigo “Ta Taimaka wa Wata Matashiya.”
Ka riƙa tuna cewa, yadda ka yi shekaru da yawa kana bauta wa Jehobah da aminci, zai iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa sosai. Ka kuma kafa misali mai kyau ta wajen jimrewa. Ka tabbata cewa, “Allah ba marar adalci ba ne.” Ba zai manta da aikinka, da kuma ƙaunar da ka nuna ga sunansa ba.—Ibran. 6:10.
KA CI-GABA DA TAIMAKA WA MUTANE
Bincike ya nuna cewa tsofaffi da suke taimaka wa mutane suna kasancewa da koshin lafiya, suna tunani da kyau, kuma suna kasancewa da tsawon rai.
Gaskiyar ita ce, yi wa mutane alheri, ba zai hana mutum fama da matsalolin da ke tattare da tsufa ba. Mulkin Allah ne kaɗai zai iya kawar da ainihin abin da ke jawo tsufa da mutuwa, wato zunubin da muka gāda.—Rom. 5:12.
Amma ko a yanzu ma, idan ka ci-gaba da yin abubuwan da Jehobah yake so ka yi, kamar taimaka wa mutane su koyi gaskiya game da shi, hakan zai ƙarfafa begenka, kuma zai iya inganta lafiyarka. Tsofaffi, ku tuna cewa Jehobah yana daraja abubuwan da kuke yi a hidimarsa, kuma bangaskiyarku tana sa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya su daraja ku sosai.