RAYUWAR KIRISTA
Albarkun Wa’azi da Amalanke a Faɗin Duniya
Littafin Ayyukan Manzanni sura 5 ya nuna cewa Kiristocin ƙarni na farko sukan je haikali inda ake samun jama’a da yawa don su yi musu wa’azi. (A. M 5:19-21, 42) A yau ma, akwai albarka da yawa da aka samu daga yin wa’azi a inda jama’a suke.
KU KALLI BIDIYON NAN ALBARKUN WA’AZI DA AMALANKE A FAƊIN DUNIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
A wace shekara ce aka soma amfani da amalanke a wa’azi kuma ta yaya aka yi hakan?
Me ya sa amalanken wa’azi ya fi na teburi amfani sosai?
Wane darasi ne muka koya daga labarin ’Yar’uwa Mi Jung You?
Mene ne labarin Jacob Salomé ya koya mana game da amfanin yin wa’azi da amalanke?
Me labarin Annies da mijinta ya koya mana game da yin wa’azi da kyau sa’ad muke amfani da amalanke?