26 ga Nuwamba–2 ga Disamba
AYYUKAN MANZANNI 6-8
Waƙa ta 124 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“An Gwada Bangaskiyar ’Yan’uwa a Sabuwar Ikilisiya”: (minti 10)
A. M 6:1—An nuna wa gwauraye ’yan Helas bambanci a cikin ikilisiya (mwbr18.11-HA an ɗauko daga bt 41 sakin layi na 17)
A. M 6:2-7—Manzannin sun yi hanzarin warware matsalar (mwbr18.11-HA an ɗauko daga bt 42 sakin layi na 18)
A. M 7:58–8:1—An soma tsananta wa Kiristoci a ƙarni na farko
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
A. M 6:15—Ta yaya fuskar Istifanus “ta zama kamar ta mala’ika”? (mwbr18.11-HA an ɗauko daga bt 45 sakin layi na 2)
A. M 8:26-30—Ta yaya Kiristoci a yau suke yin wa’azi kamar yadda Filibus ya yi? (mwbr18.11-HA an ɗauko daga bt 58 sakin layi na 16)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) A. M 6:1-15
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Komawa Ziyara ta Biyu: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka gayyaci mutumin zuwa taro.
Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi, bayan haka, ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su don nazari.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) lv 33 sakin layi na 16-17
RAYUWAR KIRISTA
“Ba da Kyauta ga Jehobah”: (minti 15) Tattaunawar da dattijo zai yi. Ka fara da nuna bidiyon nan ‘Ba da Kyauta ga Jehobah’. Ka karanta wasiƙar da ofishinmu ya aika don yi wa ’yan’uwa godiya don gudummawar da suka yi a shekarar hidima da ta shige. Ka tattauna yadda muke amfana daga gudummawar da ake yi. Ka faɗi kuɗin da ake kashewa a ikilisiya kowane wata. Ka tattauna yadda za mu ba da gudummawa da kuma yadda ake amfani da ita. Ka yaba wa ’yan’uwa don gudummawar da suke bayarwa.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 16 sakin layi na 9-14 da akwatin da ke shafi na 192-193
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 67 da Addu’a