Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w21 Fabrairu p. 25
  • Sakamakon Yin Murmushi!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sakamakon Yin Murmushi!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Albarkun Wa’azi da Amalanke a Fadin Duniya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Kauna Ce Alamar Kiristoci na Gaskiya​—Kada Ka Bata Hadin Kai da Muke Mora
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Sun Ci-gaba da Waꞌazi a Lokacin Korona
    Labarai
  • Mata Suna da Mutunci A Gaban Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
w21 Fabrairu p. 25

Sakamakon Yin Murmushi!

Helen tana murmushi yayin da take tsaye kusa da amalanken yin wa’azi. Mata biyu sun zo wucewa.

WASU ’yan mata biyu suna tafiya a wurin da mutane ke kasuwanci a birnin Baguio, a ƙasar Filifin. Sun ga ’yan’uwa da suke wa’azi da amalanke, amma ba su yi musu magana ba. Wata ’yar’uwa mai suna Helen da ta tsaya kusa da amalanken ta yi musu murmushi. ’Yan matan sun ci gaba da tafiya, amma yadda Helen ta yi musu murmushi ya burge su.

Sa’ad da ’yan matan suke mota suna komawa gida, sai suka ga babbar alamar jw.org da ke gaban wata Majami’ar Mulki. Sun tuna cewa sun ga irin wannan alamar a kan wani amalanken wa’azi a ranar. Sai suka sauka daga motar kuma suka je Majami’ar. Sun ga an rubuta lokacin da ikilisiyoyi suke yin taro a ƙofar Majami’ar.

Matan biyu suna murmushi sa’ad da suka ga Helen a Majami’ar Mulki.

’Yan matan sun halarci taro na gaba da aka yi a Majami’ar. Sun yi mamaki sa’ad da suka ga Helen yayin da suka shiga Majami’ar Mulkin. Nan da nan sun tuna cewa ita ce ta yi musu murmushi. Helen ta ce: “Na ji tsoro da suka zo suka same ni, domin ban san dalilin da ya sa suka zo wurina ba.” Amma sun gaya wa Helen cewa sun taɓa ganin ta tana wa’azi da amalanke.

’Yan matan sun ji daɗin taron, kuma sun saki jiki sosai sa’ad da suke tare da ’yan’uwan. Sa’ad da suka ga ’yan’uwa suna shara bayan taro, sai su ma suka bi su yin shara. Ɗaya cikinsu ta bar ƙasar Filifin, amma ɗayan ta soma halartan taro kuma ana nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Hakan ya faru don ’yar’uwarmu ta yi murmushi sa’ad da take wa’azi!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba