Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/15 pp. 29-32
  • Na Samu Abubuwa Masu Kyau Da Yawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Na Samu Abubuwa Masu Kyau Da Yawa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tuna Abubuwa Masu Kyau
  • Yadda Muka Haɗu da Carlos
  • Tafiye-Tafiye Masu Wuya da Karimci Masu Daɗaɗa Zuciya
  • “Ba Ma Son Mu Ja da Baya”
  • Yin Hidima Tare da Amintattun ’Yan’uwa Masu Bi
  • Muna Godiya don Alherin Jehobah
  • “Na Yi Ta Jira Shaidun Jehobah Su Kira Ni”
    Labarai
  • Yin Hidima A Lokacin Faɗaɗawa Mai Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Jehobah Ya Koyar da Ni In Yi Nufinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Jehobah Ya Koyar da Ni Tun Ina Ƙarami
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/15 pp. 29-32

Na Samu Abubuwa Masu Kyau Da Yawa

Arthur Bonno ne ya ba da labarin

A SHEKARA ta 1951, ni da matata, Edith, muna taron gunduma sa’ad da aka yi sanarwa cewa za a yi taro don waɗanda suke son su yi hidima a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje.

Sai na ce: “Bari mu je mu saurara!”

Edith ta ce: “Maigidana ba za mu iya zama masu wa’azi a ƙasashen waje ba!”

“Mu je don Allah matata, saurarawa kawai za mu yi.”

Bayan taron, aka ba mu fam na Makarantar Gileyad.

Sai na ce: “Bari mu cika su mu gani.”

“Amma maigidana, iyalanmu kuma fa?”

Mun halarci Makarantar Gileyad kusan shekara ɗaya da rabi bayan taron gundumar, kuma aka aika mu yin hidima a Ecuador, wata ƙasa da ke Amirka ta Kudu.

Kamar yadda ka lura a tattaunawar da ni da matata muka yi a taron gundumar, ina da ra’ayi cewa za mu iya yin duk abin da muka zaɓa cewa za mu yi. Amma Edith, mai tawali’u ce da kuma filako. Sa’ad da take tasowa a ƙaramin garin Elizabeth, Pennsylvania, a ƙasar Amirka, ba ta taɓa yin kuskuren yin tafiya mai nisa daga gida ba ko kuma ta haɗu da baƙi. Hakan ya sa ya yi mata wuya ta bar gida. Amma duk da haka, ta amince da aikin da aka ba mu na yin hidima a ƙasar waje. Mun isa ƙasar Ecuador a shekara ta 1954 kuma tun lokacin muna hidima a ƙasar. Mun samu abubuwa masu kyau da yawa a shekarun da muka yi a wannan wurin. Za ka so ka ji wasu cikin waɗannan?

Tuna Abubuwa Masu Kyau

Mun yi hidimarmu ta farko a babban birnin, Quito, wanda ke Tudun Andes. Muna tafiyar kwanaki biyu ta jirgin ƙasa da babbar mota daga birnin Guayaquil, da ke baƙin teku, inda jirgin sama yake zuwa cikin mintoci talatin yanzu! Mun yi hidima ta shekara huɗu masu daɗi a birnin Quito. Wani abu mai kyau ya sake faruwa a shekara ta 1958: An gayyace mu mu yi hidimar kula da da’ira.

Akwai ƙananan da’irori biyu kawai a ƙasar baki ɗaya a lokacin. Saboda haka, ƙari ga ziyartar ikilisiyoyi, mun yi wa’azi na makonni da yawa a shekara a ƙananan garurruka inda babu Shaidu da ke zama a wurin. Masaukai da ke garurrukan suna da ƙananan ɗakuna da babu taga, sai gado kaɗai. Mun ɗauki akwatin katako mai ɗauke da rasho da tukunya da kwanuka da kwanon wanki da zanen gado da gidan sauro da tufafi da tsofaffin jaridu da kuma wasu kayayyaki. Mun toshe ramukan da ke bangon gidan da jaridun don kada ɓeraye su shigo da sauƙi.

Ko da waɗannan ɗakuna suna da duhu kuma ba su da kyaun gani, mun tuna taɗin da muke yi sa’ad da muke zaune a kan gado, muna cin abincin da muka dafa da rashonmu. Tun da garaje na yakan sa na yi magana kafin na yi tunani, matata takan yi amfani da wannan lokacin don ta yi mani gyara a kan yadda ya fi dacewa na gabatar da kaina ga ’yan’uwan da muka kai wa ziyara. Na saurare ta, kuma ziyararmu ta daɗa zama mai ƙarfafawa. Kuma, sa’ad da na yi baƙar magana game da wani, za ta ƙi saka baƙi a zancen. Hakan ya sa na samu ra’ayi mai kyau game da ’yan’uwana. Amma sau da yawa, muna tattauna abubuwan da muka koya daga talifofin Hasumiyar Tsaro da hidimar fage da kuma abin da muka fuskanci a ranar. Kuma waɗannan lokatan masu daɗi ne sosai!

Yadda Muka Haɗu da Carlos

An ba mu sunan wani da ke son saƙonmu sa’ad da muke garin Jipijapa da ke yammacin Ecuador, kuma sunan wannan mutumin Carlos Mejía ne, amma ba a ba mu adireshinsa ba. Sa’ad da muka bar ɗakin hayar da muke, ba mu san inda za mu soma nemansa ba, sai muka soma tafiya kawai. Ruwan sama da aka yi da daddare ya ɓata hanyar, kuma mun kauce wa ramukan laka da yawa. Ina gaban matata, sa’ad da farat ɗaya ta yi ihu a baya, ta ce “Maigidana!” Na juya na ga cewa matata ta nitse cikin baƙin laka har gwiwarta. Abin na da ban dariya sosai da har na kusan yin dariya a gabanta idan ba don ta birkice ba.

Na fito da ita daga cikin lakar amma ban da takalmanta. Wani yaro da wata yarinya suna kallonmu, sai na gaya musu, “Zan ba ku kuɗi idan kuka ciro waɗannan takalma daga cikin lakar.” Nan da nan suka ciro takalman, amma matata tana bukatar ta samu inda za ta wanke jikinta. Mahaifiyar yaran tana kallonmu sai ta ce mu shigo gida, inda ta taimaka wa matata ta wanke ƙafafunta kuma yaran suka wanke takalman. Amma wani abu mai kyau ya faru kafin mu tafi. Na tambayi matar ko ta san inda za mu samu wani mutum mai suna Carlos Mejía. Cike da mamaki, ta ce, “Ai maigidana ne.” Da shigewar lokaci muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su, kuma daga baya dukan waɗanda suke wannan iyalin suka yi baftisma. Shekaru da yawa bayan hakan, Carlos da matarsa da biyu cikin yaransu suka zama majagaba na musamman.

Tafiye-Tafiye Masu Wuya da Karimci Masu Daɗaɗa Zuciya

Tafiye-tafiye a hidimar kula da da’ira yana ɗauke da ƙalubale. Mun yi amfani da bas da jiragen ƙasa da manyan motoci da kwalekwale da kuma ƙananan jiragen sama. A wani lokaci, John McLenachan wanda ya yi hidima a matsayin mai kula da gunduma tare da matarsa, Dorothy, sun bi mu zuwa wa’azi a ƙauyuka inda ake kama kifaye kusa da iyakar ƙasar Kolombiya. Mun yi tafiya a kwalekwale mai inji. Babban kifin shark mai girman kwalekwalen yana iyo kusa da mu! Girman kifin ya tsorata matuƙin jirgin ma kuma nan da nan ya tuƙa jirgin zuwa bakin ruwa.

Amma, ƙalubalen da muka fuskanta a hidimar kula da da’ira suna da amfani. Mun san ’yan’uwa masu karimci sosai. Lokatai da yawa iyalai da muke zama da su suna nacewa mu ci abinci sau uku a rana, su kuma su ci sau ɗaya tak. Ko kuma su sa mu kwana a kan gado ɗaya da ke gidan, su kuma su kwanta a ƙasa. Sau da yawa matata ta kan ce, “Waɗannan ’yan’uwa ƙaunatattu sun sa na fahimci cewa muna bukatar abubuwa kaɗan ne kawai.”

“Ba Ma Son Mu Ja da Baya”

A shekara ta 1960, wani abu mai kyau ya faru da mu, an gayyace mu mu yi hidima a ofishin reshe a birnin Guayaquil. Yayin da nake aiki a ofishi, matata tana hidimar fage a wata ikilisiya da ke kusa da reshen. Ban taɓa tunani cewa zan iya yin aiki a ofishi ba kuma saboda haka ina jin ban ƙware ba, amma kamar yadda littafin Ibraniyawa 13:21 ya nuna, Allah ya kamilta mu “cikin kowane kyakkyawan abu garin [mu] aika nufinsa.” Bayan shekara biyu, aka gayyace ni zuwa makarantar Gileyad na watanni goma da za a yi a Bethel da ke Brooklyn, New York. A wannan lokacin, ana bukatar mata su kasance a wurin hidimarsu. An aika wa matata wasiƙa daga Brooklyn. An gaya mata ta yi tunani sosai ko za ta yarda mijinta ya yi tafiya na watanni goma ba tare da ita ba.

Matata ta amsa: “Na san cewa wannan ba zai kasance abu mai sauƙi ba, amma babu shakka mun san cewa Jehobah zai taimake mu a duk matsalolin da za su taso. . . . Ba ma son mu ƙi kowane gata da aka ba mu ko kuma kowane zarafi na cika hakkokinmu da kyau.” A wannan lokacin da nake Brooklyn, matata tana aika mini wasiƙa kowane mako.

Yin Hidima Tare da Amintattun ’Yan’uwa Masu Bi

A shekara ta 1966, ni da matata muka koma birnin Quito domin rashin lafiya, a wurin mun sake soma hidimarmu ta ƙasar waje tare da ’yan’uwa da suke yankin. Hakika, su masu aminci ne ƙwarai!

Wani mutum da ba mai bi ba ne ya saba dukan matarsa amintacciya da mai bi ce. Wata rana, da ƙarfe shida da safe, wani ya kira mu cewa mijin ’yar’uwar ya sake mata duka. Na gudu na je gidan ’yar’uwar. Na yi mamaki sosai da na ganta. Tana kwance a kan gado, duk jikinta ya kumbura cike da raunuka. Mijinta ya yi mata duka da kan tsintsiya har tsintsiyar ta karye. An jima a ranar, na same shi a gida kuma na gaya masa cewa abin da ya yi ba shi da kyau. Ya nemi gafara sosai.

A tsakanin shekara ta 1970 da 1979, na samu sauƙi kuma muka sake soma hidimar kula da da’ira. Birnin Ibarra yana cikin da’irarmu. Sa’ad da muka ziyarci wannan birnin a kusan ƙarshen shekara ta 1950 da 1959, Shaidu biyu ne kaɗai suke wurin, wato wani mai hidima na ƙasar waje da kuma wani ɗan’uwa daga yankin. Saboda haka, muna ɗokin ganin sababbi da yawa da suka shigo cikin ikilisiyar.

A taronmu na farko a wurin, Ɗan’uwa Rodrigo Vaca ya hau kan dakalin yin magana kuma ya gudanar da sashen da ’yan’uwa za su ba da kalami. A duk lokacin da ya yi tambaya, waɗanda suka halarci taron sukan yi ihu suna cewa “Yo, yo!” wato (“Ni, ni!”) maimakon su ɗaga hannayensu. Ni da matata Edith mun kalli juna muna mamaki. Ina tunani ‘Mene ne yake faruwa a nan?’ Daga baya muka ji cewa Ɗan’uwa Vaca makaho ne amma ya san muryoyin waɗanda suke cikin ikilisiyar yayin da suke ihu. Makiyayi ne da ya san tumakinsa sosai! Wannan ya tuna mana kalaman Yesu da ke Yohanna 10:3, 4, 14 game da Nagarin Makiyayi da kuma tumaki da suka san juna sosai. A yau, a cikin birnin Ibarra akwai ikilisiyoyi guda shida na Sfanisanci ɗaya na yaren Quichua ɗayan kuma na yaren kurame. Ɗan’uwa Vaca ya ci gaba da hidima da aminci a matsayin dattijo da kuma majagaba na musamman.a

Muna Godiya don Alherin Jehobah

A shekara ta 1974 mun samu wani alheri daga Jehobah sa’ad da aka gayyace mu mu koma Bethel, inda aka sake ce na yi aiki a ofishi kuma daga baya aka naɗa ni ɗaya cikin Kwamitin Reshe. Da farko, matata Edith ta yi aiki a kicin, daga baya ta soma aiki a ofishi, inda take hidimar raba wasiƙu har yau.

A cikin shekaru da yawa, muna farin ciki marabtar ’yan’uwa ɗarurruwa da aka koyar da su a Gileyad, waɗanda suka manyanta kuma suna ƙwazo a cikin ikilisiyoyi da suke hidima. Dubban ’yan’uwa maza da mata da suka zo daga ƙasashe 30 don su yi hidima a wannan ƙasar sun kuma ƙarfafa mu. Halinsu na sadaukarwa yana burge mu! Wasu sun sayar da gidaje da kuma kasuwancinsu don su zo nan su yi hidima a wurare da ake da bukata mai girma na masu shelar Mulki. Sun sayi motoci don su yi wa’azi a wurare masu nisa, sun kafa sababbin ikilisiyoyi, kuma sun taimaka wajen gina Majami’un Mulki. ’Yan’uwa mata da yawa da ba su yi aure ba sun zo daga wasu ƙasashe don su yi hidimar majagaba a nan, kuma mata ne masu ƙwazo da masu aiki tuƙuru!

Hakika, na samu abubuwa masu kyau da yawa a shekarun nan da na yi ina bauta wa Allah. Abin da ya fi muhimmanci a cikin waɗannan shekarun shi ne dangantaka ta da Jehobah. Ina kuma godiya cewa Jehobah ya ba ni ‘mataimakiya.’ (Far. 2:18) Sa’ad da na tuna shekaru 69 da muka kasance tare a matsayin ma’aurata, sai in tuna da Misalai 18:22 da ta ce: “Wanda ya sami mata, abin kirki ya samu.” Abin farin ciki ne kasancewa tare da matata Edith. Ta taimake ni a hanyoyi da yawa. Kuma ’ya ƙaunatacciya ce ga mahaifiyarta. Matata tana aika wa mahaifiyarta wasiƙa a kowane mako sa’ad da muka isa ƙasar Ecuador har sai shekara ta 1990, sa’ad da mahaifiyarta ta rasu tana da shekara 97.

Yanzu shekarata 90 ne kuma matata Edith tana da shekara 89. Muna ɗaukan farin ciki da muka yi don taimaka wa mutane 70 su zo ga sanin Jehobah da tamani. Muna farin ciki sosai da yake mun cika waɗannan fam don Makarantar Gileyad shekaru 60 da suka shige. Wannan shawarar da muka tsai da ta sa rayuwarmu ta cika da abubuwa masu kyau.

[Hasiya]

a Tarihin Ɗan’uwa Vaca ya fito a Awake! na 8 ga Satumba, 1985.

[Hoton da ke shafi na 29]

A filin wasa na Yankee a birnin New York tare da masu wa’azi a ƙasashen waje da muka yi makarantar Gileyad tare, a shekara ta 1958

[Hoton da ke shafi na 31]

Ziyarar wata iyalin Shaidu sa’ad da muke hidimar kula da da’ira a shekara ta 1959

[Hoton da ke shafi na 32]

A ofishin reshe a ƙasar Ecuador a shekara ta 2002

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba