Abin Da Ke Ciki
15 Ga Mayu, 2011
Na Nazari
TALIFOFIN NAZARI NA MAKONNIN:
27 ga Yuni, 2011–3 ga Yuli, 2011
Ku “Zauna a Faɗake” a Matsayin Iyalan Kirista
SHAFI NA 7
WAƘOƘI: 69, 57
4-10 ga Yuli, 2011
“Ku Yi Shiri” a Matsayin Iyalan Kirista
SHAFI NA 11
WAƘOƘI: 32, 63
11-17 ga Yuli, 2011
Wane ne Ya Fi Muhimmanci a Rayuwarka?
SHAFI NA 16
WAƘOƘI: 51, 49
18-24 ga Yuli, 2011
SHAFI NA 21
WAƘOƘI: 95, 116
25-31 ga Yuli, 2011
Cikakkiyar Dogara ga Jehobah Tana Sa Mu Gaba Gaɗi
SHAFI NA 28
WAƘOƘI: 46, 23
Manufar Talifofin Nazari
TALIFOFIN NAZARI NA 1, 2 SHAFUFFUKA NA 7-15
Talifi na farko ya tattauna hakkin da kowanne mutum da ke cikin iyalin Kirista yake da shi wajen kasancewa a faɗake a ruhaniya. Talifi na biyu ya tattauna yadda sa idonmu ya kasance sarai da biɗan maƙasudai na ruhaniya da kuma yin Bauta ta Iyali da yamma suke da muhimmanci ga zaman lafiya na ruhaniya na dukan iyalin.
TALIFIN NAZARI NA 3 SHAFUFFUKA NA 16-20
Ya kamata Jehobah ya zama Wanda ya fi muhimmanci a rayuwar bayinsa. Wannan talifin ya nanata darussan da muka koya game da wannan daga abin da ya faru da Hauwa’u mace ta farko da Ayuba mutum mai aminci da kuma Ɗan Allah kamiltacce, Yesu Kristi.
TALIFIN NAZARI NA 4 SHAFUFFUKA NA 21-25
A Romawa sura ta 11, manzo Bulus ya yi maganar itacen zaitun na alama. Mene ne fannoni dabam dabam na wannan itacen yake wakilta? Za mu ƙara koya game da nufe-nufen Jehobah kuma za mu yi mamaki game da yawan hikimarsa, yayin da muke bincika abin da suke nufi a wannan talifin.
TALIFIN NAZARI NA 5 SHAFUFFUKA NA 28-32
Wannan talifin ya tattauna Zabura ta 3 da ta 4 da Sarki Dauda ya rubuta. Waɗannan waƙoƙi da aka hure sun nuna cewa za mu aikata da tabbaci idan muka yi addu’a ga Jehobah cewa ya taimaka mana kuma muka dogara gare shi gabaki ɗaya. Dauda ya yi hakan sa’ad da ɗansa Absalom ya ci amanarsa.
A FITOWAR NAN
3 Kana Jin Daɗin Karanta da Kuma Yin Nazarin Kalmar Allah Kuwa?
6 “Mai Kula Mai Kyau da Kuma Aboki Ƙaunatacce”
26 Ka Bi Kristi, Kamiltaccen Shugaba