Ka Tuna?
Ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
• Shin Kiristoci na gaske suna yin amfani da sunan Allah a matsayin laya?
Wasu mutane suna yin amfani da wasu abubuwa a matsayin laya don su kāre kansu da shi ta hanyar sihiri, amma mutanen Allah ba sa ɗaukan sunan Allah a matsayin laya. Suna dogara ga Jehobah kuma suna ƙoƙari su yi nufinsa, da hakan suna neman mafaka a sunansa. (Zaf. 3:12, 13)—1/15, shafuffuka na 5-6.
• Me ya sa Jehobah ya ƙi Sarki Saul?
Ya kamata Saul ya jira annabin Allah ya zo ya miƙa hadayar, amma sarkin ya yi rashin biyayya ta wurin miƙa hadayar da kansa. Daga baya, bai bi umurnin da aka ba shi cewa ya halaka maƙiyansu ba.—2/15, shafuffuka na 22-23.
• Ta yaya za mu iya nuna cewa mun tsani mugunta?
Za mu sha barasa daidai wa daida, za mu guji ayyukan sihiri, kuma za mu yi biyayya ga gargaɗin Yesu game da lalata. Alal misali, za mu ƙi kallon hotunan batsa da kuma sha’awoyin da yin hakan zai iya jawowa. (Mat. 5:27, 28) Kuma ba za mu yi cuɗanya da waɗanda aka yi wa yankan zumunci ba.—2/15, shafuffuka na 29-32.
• A wace hanya ce Irmiya yake kamar itacen da aka “dasa a bakin ruwaye, wanda yana miƙa sawayensa”? (Irm. 17:7, 8)
Bai taɓa dena ba da ’ya’ya ba kuma bai ƙyale masu hamayya su rinjaye shi ba. Maimakon hakan, ya manne wa Mai Ba Da ruwaye da ke kiyaye rai, kuma ya saurari abin da Allah ya gaya masa.—3/15, shafi na 14.