Me Ya Sa Ya Dace Ka Yi Abubuwa a Kan Lokaci?
YIN abubuwa da wuri ko a kan lokaci, ba shi da sauƙi. Wasu daga cikin ƙalubalen da za mu iya fuskanta su ne yin tafiya mai nisa, go-sulo, da kuma ayyuka masu yawa. Duk da haka, zuwa da wuri ya fi muhimmanci. Alal misali, a wajen aiki, an fi son mai zuwa da wuri kuma marar wasa. A wani ɓangare kuma, mai yawan makara yana iya ɓata aikin wasu, ingancin kayayyakinsu da ayyukansu. Yawan makara zai iya sa ɗalibi ya rasa wasu darussa kuma ya hana shi cin jarabawa. Zuwa asibiti don lafiyar jiki ko na haƙori a makare zai shafi jinyar da za a yi wa mutum.
Amma, a wasu wurare ba a ɗaukan yin abubuwa a kan lokaci da muhimmanci. A irin waɗannan wuraren, yin abubuwa a makare zai iya zama jininmu. Idan haka ne, yana da muhimmanci mu koyi halin yin abubuwa a kan lokaci. Fahimtar muhimmancin yin abubuwa a kan lokaci zai hana mu makara. Waɗanne dalilai ne za su sa mu riƙa yin abubuwa a kan lokaci? Yaya za mu yi nasarar yin abubuwa da wuri? Kuma waɗanne amfani ne za mu iya samu daga yin abubuwa a kan lokaci?
Jehobah, Allah Ne Mai Yin Abubuwa a Kan Lokaci
Dalili na musamman da ya sa za mu so yin abubuwa a kan lokaci shi ne cewa muna son mu yi koyi da Allahn da muke bautawa. (Afis. 5:1) Jehobah ya kafa misali mafi kyau na yin abubuwa a kan lokaci. Bai taɓa makara ba. Yana manne wa tsarinsa sosai wajen cika nufe-nufensa. Alal misali, sa’ad da Jehobah ya tsai da shawarar halaka muguwar duniya da rigyawa, ya gaya wa Nuhu: “Sai ka yi jirgi na itacen jufra.” Yayin da lokacin ƙarshe ya kusa, Jehobah ya gaya wa Nuhu ya shiga cikin jirgin kuma ya gaya masa: “Da sauran kwana bakwai, kāna zan sa a yi ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in; kowane abu mai-rai da na yi kuma zan shafe shi daga dukan fuskar ƙasa.” A daidai lokaci, “bayan kwanan nan bakwai, sai ga ruwan tufana bisa duniya.” (Far. 6:14; 7:4, 10) Ka yi tunanin abin da zai sami Nuhu da iyalinsa da a ce ba sa cikin jirgin a kan lokaci. Kamar Allahn da suke bauta ma wa, dole ne su kasance masu yin abubuwa a kan lokaci.
Shekaru 450 bayan Rigyawa, Jehobah ya gaya wa Ibrahim uban iyali cewa zai haifi ɗan da ta wurinsa za a haifi Zuriyan da aka yi alkawarinsa. (Far. 17:15-17) Allah ya ce za a haifi Ishaku “a cikin wannan lokaci baɗi war haka.” Hakan ya faru kuwa? Nassosi sun gaya mana: “Saratu fa ta yi juna biyu, ta haifa wa Ibrahim ɗa namiji cikin tsufarsa, bisa ayananniyar sa’a wanda Allah ya faɗa masa.”—Far. 17:21; 21:2.
Littafi Mai Tsarki yana cike da misalai da suka nuna cewa Allah yana yin abubuwa a kan lokaci. (Irm. 25:11-13; Dan. 4:20-25; 9:25) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana mu ci gaba da sauraron ranar hukuncin Jehobah na nan gaba. Ko idan kamar ta “jima” a ra’ayin ’yan Adam, an tabbatar da mu cewa “ba za ta yi jinkiri ba.”—Hab. 2:3.
Zuwa a Kan Lokaci Yana da Muhimmanci a Bauta
Dukan mazan Isra’ila suna bukatan su hallara a inda aka keɓe don “ayanannun idodi na Ubangiji” kuma za su yi hakan a kan lokaci. (Lev. 23:2, 4) Allah ya kuma keɓe lokacin da za a miƙa wasu hadayu. (Fit. 29:38, 39; Lev. 23:37, 38) Hakan ya nuna cewa Allah yana son bayinsa su riƙa zuwa wurin bautarsu a kan lokaci, ko ba haka ba?
A ƙarni na farko, sa’ad da manzo Bulus ya umurci mutanen Koranti game da yadda ya kamata a gudanar da taron Kirista, ya aririce su: “A yi abu duka da hankali bisa ga ƙa’ida kuma.” (1 Kor. 14:40) Saboda haka, za a soma taro na Kirista don bauta wa Allah a kan lokaci. Ra’ayin Jehobah game da yin abubuwa a kan lokaci bai canja ba. (Mal. 3:6) Saboda haka, menene za mu yi don mu riƙa halartan waɗannan tarurruka na Kirista a kan lokaci?
Yadda Za a Yi Nasarar Yin Abubuwa a Kan Lokaci
Wasu sun ga cewa tsara abubuwa tun da wuri yana taimakawa sosai. (Mis. 21:5) Alal misali, idan za mu yi tafiya mai nisa kuma muna bukatan mu isa inda za mu a ƙayyadadden lokaci, zai dace mu soma tafiyar a lokacin da za mu isa inda za mu saura ƙiris ƙayyadadden lokacin ya kai? Zai fi kyau mu ba da ƙarin ’yan mintoci don kada mu makara, ko kuma idan “tsautsayi” ya faru a hanya. (M. Wa. 9:11, Littafi Mai Tsarki) “Wani abin da zai taimaki mutum ya isa da wuri shi ne sanin yawan lokaci na tafiyar da za a yi,” in ji wani matashi da ba ya makara mai suna José.a
Ga wasu, suna bukatan su yi shiri don barin wurin aikinsu da wuri domin su isa taron Kirista a kan lokacin. Abin da wani Mashaidi a Habasha ya yi ke nan sa’ad da ya fahimci cewa zai yi makarar minti 45 zuwa taron ikilisiya domin canje-canje a tsarin aikinsa. Ya shirya wani abokin aiki ya zo wajen aiki da wuri don ya ɗauki matsayinsa a ranar taro da yamma. Mashaidin kuma ya yarda ya yi aikin ƙarin awa bakwai don abokin aikinsa.
Idan muna da yara ƙanana, zuwa taro da wuri zai yi wuya. A yawancin lokaci uwa ce take shirya yaran, amma ya kamata wasu a cikin iyali su taimaka. Wata uwa ’yar Mexico mai suna Esperanza ta kula da yara takwas ita kaɗai. Shekarunsu yanzu ya soma daga 5 zuwa 23. Esperanza ta bayyana yadda iyalinta suke ƙoƙari su isa taro a kan lokaci: “Yarana mata manya suna taimakawa wajen shirya ƙananan. Hakan ya sa in gama aikin gida kuma mu tafi taro a kan lokacin da muka tsara.” Wannan iyalin ta kafa lokacin barin gida, kuma kowa yana ba da haɗin kai.
Amfanin Halartan Taronku na Kirista a Kan Lokaci
Yin tunani game da albarkar da muke samu daga halartan taron Kirista a kan lokaci zai iya ƙarfafa muradinmu da ƙudurinmu na yin duk wani abin da za mu iya yi don mu kasance a wajen taron da wuri. Wata matashiya mai suna Sandra, wadda take da halin zuwan taro a kan lokaci, ta ce: “Abin da nake so game da zuwa da wuri shi ne cewa ina da zarafin gai da ’yan’uwa, tattaunawa da su, kuma na san su sosai.” Idan muka isa Majami’ar Mulki da wuri, za mu amfana daga ji game da jimiri da hidima na aminci na waɗanda suka halarta. Ta wajen halartan taron da kuma yin tattaunawa mai ƙarfafawa, za mu kasance da tasiri mai kyau ga ’yan’uwanmu, kuma mu ‘tsokane su zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka.’—Ibran. 10:24, 25.
Waƙa da addu’a da ake buɗe kowane taron Kirista da su sashe ne mai muhimmanci na bautarmu. (Zab. 149:1) Waƙoƙinmu suna yabon Jehobah, suna tuna mana halaye da ya kamata mu koya, kuma suna ƙarfafa mu mu saka hannu a hidima da farin ciki. Addu’ar buɗewa kuma fa? A zamanin dā, Jehobah ya kira haikali ‘gidansa na addu’a.’ (Isha. 56:7) A yau, muna taruwa don mu miƙa addu’o’i ga Allah a taronmu. A addu’ar buɗewa ana roƙon samun ja-gorancin Jehobah da kuma ruhu mai tsarki kuma tana shirya zukatanmu su karɓi bayanin da za a tattauna. Ya kamata mu ƙuduri aniya mu isa taronmu a kan lokaci don waƙa da addu’ar buɗewa.
Sa’ad da take magana game da dalilin da ya sa take zuwa taro da wuri, Helen ’yar shekara 23 ta ce: “Ina ganin cewa hanya ce ta nuna ƙaunata ga Jehobah, tun da yake shi ne ke yin tanadin dukan bayanin da ake ba da wa, har da waƙoƙi da addu’ar buɗewa.” Bai kamata mu ma mu ɗauki batun kamar haka ba? Hakika, ya kamata. Saboda haka, bari mu yi ƙoƙari mu gina halin yin dukan ayyukanmu a kan lokaci, musamman waɗanda suka shafi bautarmu ga Allah na gaskiya.
[Hasiya]
a An canja sunayen.
[Hoton da ke shafi na 26]
Ka yi shiri sosai tun da wuri
[Hoton da ke shafi na 26]
Ka bar lokaci don “tsautsayi”
[Hotuna da ke shafi na 26]
Ka girbe amfanin zuwa taro a kan lokaci