Ka Koyi Halin Kasancewa a Kan Kari
1. Wane misali ne Jehobah ya kafa mana a batun kasancewa a kan kari?
1 Jehobah ba ya taɓa yin latti. Alal misali, yana taimaka wa bayinsa “a kan kari.” (Ibran. 4:16, Littafi Mai Tsarki) Yana kuma yi mana tanadin abubuwa da ke kama da ‘abinci a lotonsa’ don ya ƙarfafa mu. (Mat. 24:45) Saboda haka, muna da gaba gaɗi cewa ranar hukuncinsa da ke tafe “ba za ta yi jinkiri ba.” (Hab. 2:3) Hakika muna amfana sosai daga yadda Jehobah yake yin abubuwa a kan kari. (Zab. 70:5) Amma da yake mu ajizai ne, yin abubuwa a kan lokaci zai iya zama mana jan aiki. Me ya sa yana da kyau mu kasance da halin yin abubuwa a kan kari?
2. Me ya sa yin abubuwa a kan kari yana sa a ɗaukaka Jehobah?
2 Latti ya zama ruwan dare a waɗannan kwanaki na ƙarshe da mutane sun zama masu son kansu da kuma marasa kamewa. (2 Tim. 3:1-3) Saboda haka, mutane suna ganinmu a duk lokacin da muka tafi aiki da taro da kuma wasu harkoki a kan lokaci, kuma hakan yana sa su ɗaukaka Jehobah. (1 Bit. 2:12) Shin mun lura cewa muna zuwa aiki da wuri amma muna yawan halartan taro a makare? Idan muna halartan taro da wuri kafin a soma waƙa da kuma addu’ar buɗewa, za mu nuna cewa muna so mu yi koyi da Ubanmu na sama, wanda yake yin abubuwa bisa tsari.—1 Kor. 14:33, 40.
3. Me ya sa yin abubuwa a kan kari hanya ce na nuna cewa mun damu da wasu?
3 Idan muka kasance da halin yin abubuwa a kan kari, za mu nuna cewa mun damu da wasu. (Filib. 2:3, 4) Alal misali, idan muna halartan taron ikilisiya da kuma na fita wa’azi da wuri, ba za mu raba hankalin ’yan’uwanmu ba. Idan zuwa latti ya zama jikinmu, za mu sa ’yan’uwa su ji kamar lokacinmu ya fi nasu muhimmanci. Ta yin abubuwa a kan kari, za mu nuna cewa muna da himma kuma mun isa a amince da kuma dogara da mu.
4. Idan mun lura cewa muna yawan yin latti, ta yaya za mu iya yin gyara?
4 Idan mun lura cewa muna yawan yin latti, zai dace mu bincika dalilan da ke jawo hakan. Ka tsara ayyukanka a hanyar da za ka iya yinsu a daidai lokacin da ka ayyana. (M. Wa. 3:1; Filib. 1:10) Ka nemi taimakon Jehobah. (1 Yoh. 5:14) Yin abubuwa a kan kari wata hanya ce na bin dokoki biyu mafi girma, wato mu ƙaunaci Allah da kuma maƙwabtanmu.—Mat. 22:37-39.