Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 4/1 pp. 13-18
  • Yadda Jehovah Yake Bishe Mu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Jehovah Yake Bishe Mu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yaya Halartan Taro Naka?
  • Ka Zama Mai Saurarawa da Kyau
  • Bari a Ji Muryarka
  • Mara Wayo Yakan Sami Hikima
  • Duk Inda Allah Ya Bishe Mu, Za Mu Bi
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Rika Halartan Taro don Ibada?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ta Yaya Za Ka Amfana Daga Taron Shaidun Jehobah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Kana Sa Hannu Wajen Sa Taron Kirista Ya Kasance Da Ban Ƙarfafa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yin Taro don Ibada
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 4/1 pp. 13-18

Yadda Jehovah Yake Bishe Mu

“Ka bishe ni kuma a cikin hanya sosai.”—ZABURA 27:11.

1, 2. (a) Ta yaya ne Jehovah yake bishe mutanensa a yau? (b) Menene ke ƙunshe a yin amfani sosai da taro?

JEHOVAH shi ne Tushen haske da gaskiya, abin da muka koya a talifi da ya riga wannan ke nan. Kalmarsa tana haskaka hanyarmu yayin da muke tafiya a kan hanyar gaskiya. Jehovah yana bishe mu ta koya mana hanyoyinsa. (Zabura 119:105) Kamar mai-zabura na dā, muna nuna godiya a yin na’am da bishewar Allah kuma muna addu’a haka: “Ya Ubangiji, ka koya mani tafarkinka; Ka bishe ni kuma a cikin hanya sosai.”—Zabura 27:11.

2 Hanya ɗaya da Jehovah yake tanadar da koyarwa a yau ita ce a taron Kirista. Muna yin amfani sosai da wannan tanadi na ƙauna (1) ta halarta a kai a kai, (2) saurarawa a hankali ga tsarin ayyuka, da kuma (3) son yin furci a tsarin da ake bukatan yinsa? Bugu da ƙari, muna nuna godiya yayin da an ba mu shawarwari da zai taimake mu mu kasance a “cikin hanya sosai”?

Yaya Halartan Taro Naka?

3. Ta yaya wata baiwa majagaba ta gina halin halartan taro a kai a kai?

3 Wasu masu shelar Mulki sun fara halartan taro tun suna yara. “Lokacin da ni da yayata muke girma a cikin shekarun 1930, ba ma tambayar iyayenmu ko za mu je taro. Mun san za mu je sai dai ko muna rashin lafiya. Iyalinmu ba sa fasa zuwa taro,” abin da wata majagaba na Shaidun Jehovah ta tuna ke nan. Kamar annabiya Hannatu, wannan ’yar’uwa “ba ta rabuwa” da wajen bauta wa Jehovah.—Luka 2:36, 37.

4-6. (a) Me ya sa wasu masu shelar Mulki ba sa yawan zuwa taro? (b) Me ya sa yake da muhimmanci a halarci taro?

4 Kana cikin waɗanda suke halartan taron Kirista a kai a kai, ko a gareka a wasu lokutta ne kawai? Wasu Kiristoci da suke tsammanin ba su da laifi a zancen haka, sun bincika kansu. Suka lissafa kowane taro da suka halarta na ’yan makonni. Da lokacin da suka ayana ya kai, sun yi mamaki ganin cewa taro da ba su halarta ba suna da yawa.

5 Wani yana iya cewa, ‘abin da ya sa ke nan ai.’ ‘Mutane sun matsu sosai a yau shi ya sa ba shi da sauƙi a garesu su je taro a kai a kai.’ Gaskiya ne, muna rayuwa cikin lokutta da sun matsa mana sosai. Kuma, babu shakka matsin zai daɗa ƙaruwa. (2 Timothawus 3:13) Wannan bai ƙara mana bukatar halartan taro a kai a kai ba? Idan babu tsari mai kyau na cin abinci don ya kiyaye lafiyarmu, ba za mu iya tsayayya wa matsi da wannan shirin ke kawowa ba, wanda muke bukatar jimre masa. Hakika, idan ba tare da yin tarayya na kullum ba, za mu iya shiga jarabar yasar da “tafarkin mai-adilci” gabaɗaya! (Misalai 4:18) Gaskiya ne, idan mun dawo gida daga aiki a gajiye sosai, ba za mu so mu halarci taro ba. Amma dai, idan mun halarta, duk da gajiyarmu, za mu amfani kanmu kuma za mu ƙarfafa ’yan’uwanmu Kiristoci a Majami’ar Mulki.

6 Ibraniyawa 10:25 ta ambata wata muhimmiyar dalili da ya sa ya kamata mu kasance a taro a kai a kai. A wurin, manzo Bulus ya aririci ’yan’uwa Kiristoci su haɗa kansu ‘musamman ma da suke ganin ranan nan tana gusowa.’ Hakika, kada mu manta gaskiyar cewa “ranar Allah” tana gusowa kusa. (2 Bitrus 3:12) Idan mun ɗauka cewa ƙarshen wannan shirin yana da nisa sosai, za mu ƙyale biɗe-biɗe na kanmu ya kawar da ayyuka na ruhaniya da yake da muhimmanci, irinsu halartan taro. Sai kuma, kamar yadda Yesu ya yi kashedi, ‘sai farat ɗaya ranar nan ta faɗo kanmu.’—Luka 21:34.

Ka Zama Mai Saurarawa da Kyau

7. Me ya sa yake da muhimmanci yara su mai da hankali a wajen taro?

7 Halartan taro kawai ba shi ke nan ba. Tilas ne mu saurara da kyau, mu mai da hankali ga abin da ake faɗa a wurin. (Misalai 7:24) Wannan ya haɗa da yaranmu. Idan yaro ya je makaranta, ana bukatar ya saurara ga malaminsa, ko idan ba ya son wani darasi ko kuma bai gane darasin ba. Malamin ya sani cewa idan yaron ya yi ƙoƙari ya mai da hankali, zai koyi wani abu daga cikin darasin. To, bai dace ba ne cewa yara da suke zuwa makaranta su mai da hankali ga koyarwa da ake yi a taro na ikklisiya maimakon a ƙyale su su yi barci nan da nan da an fara taro? Gaskiya ne cewa, gaskiya da take da tamani da ke cikin Nassosi da akwai ‘wasu abubuwa masu-wuyan ganewa.’ (2 Bitrus 3:16) Amma bai kamata mu rena fahimta na yaro ba. Allah ba ya yin haka. A cikin lokuttan Littafi Mai-Tsarki, Allah ya umurce bayinsa ƙanana su ‘ji su koyi jin tsoron Jehovah kuma su kiyaye dukan zantattukan wannan doka,’ waɗanda wasu cikinsu kuwa na da wuya yara su gane. (Kubawar Shari’a 31:12; gwada da Leviticus 18:1-30.) Jehovah yana bukatar abu dabam ne daga yara a yau?

8. Waɗanne matakai wasu iyaye suke ɗauka don taimakon yaransu su mai da hankali a taro?

8 Iyaye sun sani cewa ana ƙosar da rabin bukatun ruhaniya na yaransu ta abin da suke koya daga taro ne. Shi ya sa, wasu iyaye suka shirya don yaransu su yi ɗan barci kafin lokacin taro don su kai Majami’ar Mulki da kuzari kuma a shirye don su koyi wani abu. Wasu iyaye kuma sukan rage ko kuma hana yaransu kallon telibijin a maraicen da akwai taro. (Afisawa 5:15, 16) Kuma irin iyayen nan suna rage abubuwan da suke raba hankali, suna ƙarfafa yaransu su saurara kuma su koya, daidai da girmansu da kuma iyawarsu.—Misalai 8:32.

9. Me zai iya taimaka mana mu gina iyawarmu na sauraro?

9 Yesu magana yake yi wa manya lokacin da ya ce: “Ku yi lura fa yadda ku ke ji.” (Luka 8:18) A zamanin yanzu, yana da sauƙi a faɗa fiye da a yi. Babu shakka, saurarawa da kyau aiki ne mai wuya, amma ana iya gina yadda za a saurara. Yayin da ka ke sauraron jawabi daga Littafi Mai-Tsarki ko kuma wani sashe na taro, ka yi ƙoƙarin ware muhimman darussa. Ka yi ƙoƙarin tsammanin abu na gaba da mai ba da jawabin zai faɗa. Ka biɗi wasu darussa da za ka yi amfani da su cikin hidima ko kuma wanda za ka yi amfani da su a rayuwarka. Ka maimaita darussan cikin azancinka yayin da ake tattauna su. Ka ɗan rubuta batuttuwa.

10, 11. Ta yaya wasu iyaye suka taimake yaransu su zama masu saurarawa da kyau, kuma waɗanne matakai ka gano suke da amfani a gareka?

10 Ya fi kyau a koyi halin saurarawa da kyau daga yarantaka. Wasu yara da ba su shiga makaranta ba tukuna, da ba su fara koyon karatu da rubutu ba, iyayensu suna ƙarfafa su su “rubuta batuttuwa” a taro. Suna rubuta wani abu a kan falle yayin da ake ambata kalmomin nan kamar su “Jehovah,” “Yesu,” ko kuma “Mulki.” Ta hanyar nan, yara suna iya mai da hankali ga abin da ake faɗa daga dakalin magana.

11 Har yara da sun yi ɗan girma ma suna bukatar ƙarfafa don su mai da hankali. Wani maigida ya lura cewa yaronsa ɗan shekara 11 yana mafarki a zaune a babban taro na Kirista, sai uban ya ba yaron Littafi Mai-Tsarki kuma ya ce masa ya dinga buɗewa duk lokacin da mai ba da jawabi ya ambata wata aya a ciki. Uban, wanda yake rubuta muhimman batuttuwa, ya lura yayin da ɗan ya riƙe Littafi Mai-Tsarkin. A bayan haka, yaron ya mai da hankali sosai ga tsarin ayyuka na taron da marmari.

Bari a Ji Muryarka

12, 13. Me ya sa yake da muhimmanci mu rera waƙa a cikin ikklisiya?

12 Sarki Dauda ya rera haka: “Ya Ubangiji, zan kewaye bagadinka: Domin in ɗaukaka muryar godiya.” (Zabura 26:6, 7) Taro na Shaidun Jehovah yana tanadar mana da zarafi mai kyau don mu furta bangaskiyarmu da murya mai ƙarfi. Hanya ɗaya da za mu iya yin haka ita ce ta rera waƙa a cikin ikklisiya. Wannan muhimmiyar sashen bautarmu ce, amma da take da sauƙi an yi banza da ita.

13 Wasu yara da ba su iya karatu ba suna haddace kalmomin waƙoƙin Mulki da za a rera a taro kowane mako. Suna murna su rera waƙa tare da manya. Amma kuma, yayin da yaran sun yi girma kaɗan, sai su rage ƙwazonsu a rera waƙoƙin Mulki. Wasu manya ma suna jin kunyar rera waƙa a taro. Amma, rera waƙa sashen bautarmu ce, yadda hidimar fage sashen bautarmu ce. (Afisawa 5:19) Muna yin iyakacin ƙoƙarinmu mu yi yabon Jehovah cikin hidimar fage. Ba za mu so mu ɗaukaka shi ba ta tada muryoyinmu—ko da daɗin ji ko babu—ta wajen rera waƙoƙin yabo daga zuci?—Ibraniyawa 13:15.

14. Me ya sa ake bukatar shirya abin da muke nazarinsa a taron ikklisiya kafin lokaci?

14 Muna yaba wa Allah yayin da muke yin furci masu ginawa a lokacin sashen taron da ake bukatar furci daga jama’a. Wannan yana bukatar yin shiri. Yana cin lokaci don a yi bimbini a kan fasaloli masu zurfi na Kalmar Allah. Manzo Bulus ya gane wannan, da shi ke shi ɗalibin Nassosi ne ƙwarai. Ya rubuta: “Ya zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa!” (Romawa 11:33) Magidanta, ya wajaba ku taimake kowa a cikin iyalinku ya bincika hikimar Allah, yadda take bayyane cikin Nassosi. Ku yi amfani da ɗan lokaci a lokacin nazarin Littafi Mai-Tsarki na iyali don fassara wasu darussa masu wuya kuma ku taimake iyalinku su shirya taro.

15. Waɗanne shawarwari ne za su iya taimaka wa mutum ya yi furci a taro?

15 Idan kana son ka yi furci a taro kullum, me ya sa ba za ka shirya wani abin da za ka so ka furta tun da wuri ba? Ba a bukatar doguwar magana. Za a gode in an karanta wata ayar Littafi Mai-Tsarki da gabagaɗi ko kuma kalmomi kalilan masu kyau daga zuci. Wasu masu shela sukan ce wa mai gabatar da nazari ya kira su don su amsa wata tambaya ta wani izifi, don kada su yi rashin zarafi na furta bangaskiyarsu.

Mara Wayo Yakan Sami Hikima

16, 17. Wane gargaɗi ne dattijo ya ba wani bawa mai hidima, kuma me ya sa ya kasance da amfani?

16 A wurin taron Shaidun Jehovah, ana yawan tunatar da mu mu karanta Kalmar Allah kowace rana. Yin haka tana wartsakarwa. Tana kuma taimakon mu mu tsai da shawara da hikima, mu gyara munanan halaye, mu tsayayya jarabobbi, kuma mu sake daidaita a ruhaniya idan dā mun kauce a hanya.—Zabura 19:7.

17 Riƙaƙƙun dattiɓai a shirye suke su tanadar da gargaɗi na Nassi da ya yi daidai da bukatunmu. Abin da ya kamata mu yi shi ne, mu “jawo ta” ta wurin biɗan gargaɗi da ke daga Littafi Mai-Tsarki. (Misalai 20:5) Wata rana wani bawa mai hidima mai ƙwazo ya tambayi wani dattijo yadda zai zama da ƙarin amfani cikin ikklisiya. Dattijon, da yake ya san saurayin sosai, ya buɗe Littafi Mai-Tsarki zuwa 1 Timothawus 3:3, wanda ya ce ya kamata maza da aka naɗa su, su kasance ‘masu-siyasa.’ A cikin sauƙin hali ya ambata hanyoyi da saurayin zai iya nuna siyasa cikin dangantarkarsa da wasu. Ɗan’uwa saurayin ya yi fushin da gargaɗin nan da aka ba shi ne? Ko kaɗan! “Dattijon ya yi amfani da Littafi Mai-Tsarki,” in ji shi, “don haka na gane cewa gargaɗin ya fito ne daga wurin Jehovah.” Bawan nan mai hidima ya yi amfani da gargaɗin da kyau kuma yana ci gaba da kyau.

18. (a) Menene ya taimake wata budurwa Kirista ta tsayayya wa jaraba a makaranta? (b) Waɗanne ayoyin Littafi Mai-Tsarki ne ka ke tuna da su, yayin da ka fuskanci jaraba?

18 Kalmar Allah ma za ta taimake matasa su “guje ma sha’awoyin ƙuruciya.” (2 Timothawus 2:22) Wata budurwa Shaidar Jehovah wadda ba ta daɗe da sauƙe karatu daga babbar makaranta ba, ta ƙi jarabobbi a duk shekarun da ta yi a makaranta, ta yi bimbini kuma ta yi amfani da wasu ayoyin Littafi Mai-Tsarki. Sau da yawa tana tunani a kan gargaɗin da ke Misalai 13:20: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima.” Ta mai da hankali ga haka, ta yi abokantaka da waɗanda suke daraja ƙa’idodin Nassi ne kawai. Ta ce: “Ban fi kowa ba. Idan na bi jama’a da bai dace ba, zan so na gamsar da abokanena kuma wannan zai kai ni cikin masifa.” Gargaɗin Bulus da ke a 2 Timothawus 1:8 ma ya taimake ta. Ya rubuta: “Kada fa ka ji kunyar shaidar Ubangijinmu, . . . amma ka daure shan wuya tare da bishara.” Daidai da wannan gargaɗin, ta faɗi imaninta da gabagaɗi da ke daga Littafi Mai-Tsarki wa abokan ajinta a lokacin da ya dace. Duk lokacin da aka ce ta gabatar da wani labari a cikin aji, cikin hikima takan zaɓi wani jigo da zai ba ta zarafin da zata ba da shaida game da Mulkin Allah wa ajin.

19. Me ya sa wani saurayi bai iya tsayayya wa matsi na wannan duniya ba, amma menene ya ba shi ƙarfi na ruhaniya?

19 Idan za mu kauce daga “tafarkin mai-adilci,” Kalmar Allah za ta iya taimaka mana mu daidaita tafiyarmu. (Misalai 4:18) Wani saurayi da yake da zama a Afirka ya shaida wannan. Lokacin da ɗaya cikin Shaidun Jehovah ya ziyarce shi, ya yi na’am ya yi nazarin Littafi Mai-Tsarki. Ya ji daɗin abin da yake koyo amma bai daɗe ba sai ya shaƙu da mugayen abokai a makaranta. A kwana a tashi, ya bauɗe cikin yayin rayuwa ta lalata. “Lamirina ya yi ta sūka na, sai kuma na daina zuwa taro,” in ji shi. Daga baya, ya fara halartan taro. Saurayin ya furta gaskiyar cewa: “Na gano cewa dalilin wannan domin na yi yunwa a ruhaniya. Ba na yin nazari na kaina. Abin da ya sa ke nan ban iya tsayayya wa jaraba ba. Sai na fara karanta Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! A hankali, na samo ƙarfina na ruhaniya kuma na tsabtace rayuwata. Wannan ya zama wa’azi mai kyau ga waɗanda suka ga canje-canje da na yi. Na yi baftisma, kuma yanzu na fi farin ciki.” Menene ya ba wannan saurayin ƙarfi don ya sha kan kumamancinsa na jiki? Ya samo ƙarfinsa na ruhaniya ta nazari da kansa na Littafi Mai-Tsarki, a kai a kai.

20. Ta yaya ne matashi zai iya tsayayya ma farmakin Shaiɗan?

20 Matasa Kiristoci, ana kai maku farmaki a yau! Idan fa za ku tsayayya wa farmakin Shaiɗan, tilas ne ku dinga ci abinci na ruhaniya a kai a kai. Mai-zabura, wanda shi ma saurayi ne ya gane haka. Ya gode wa Jehovah don tanadar da Kalmarsa, domin ‘saurayi ya tsarkake al’amuransa.’—Zabura 119:9.

Duk Inda Allah Ya Bishe Mu, Za Mu Bi

21, 22. Me ya sa bai kamata mu kammala da cewa hanyar gaskiya tana da wuya ba?

21 Jehovah ya bishe al’ummar Isra’ila daga Masar zuwa Ƙasar Alkawari. Hanyar da ya zaɓa, a ganin mutane dai, mai wuya ce. Maimakon bin wadda take da sauƙi, hanya da ke miƙe ta hanyar Bahar Maliya, Jehovah ya bishe mutanensa ta hanyar daji da ba ta da sauƙi. Amma, wannan alheri ne daga wurin Allah. Ko da shi ke gajeriya ce, da hanyar tekun ta kai Isra’ilawa ta ƙasar mutanen Philistiyawa masu zafin hali. Da ya zaɓi wata hanya dabam kuwa, Jehovah ya tsare mutanensa daga fuskantar Philistiyawa tun lokaci bai kai ba.

22 Hakazalika, hanyar da Jehovah yake bishe mu a yau za ta zama kamar tana da wuya a wasu lokutta. Kowane mako, muna da tsarin ayyuka na Kirista, haɗe da taro na ikklisiya, nazari da kanmu, da kuma hidimar fage. Ƙila wasu hanyoyi kamar da sauƙi suke. Amma idan mun bi ja-gorar Allah ne kawai za mu isa masauƙinmu da muke aiki tukuru don mu isa. Saboda haka, bari mu ci gaba da karɓan koyarwa da sun dace daga Jehovah kuma mu kasance a kan “hanya sosai” har abada!—Zabura 27:11.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Me ya sa musamman muke bukatar mu halarci taro na Kirista a kai a kai?

• Menene iyaye za su iya yi don su taimake yaransu su mai da hankali a taro?

• Menene zama mai saurarawa da kyau ya ƙunsa ?

• Menene zai taimake mu mu yi furci a taro?

[Hoto a shafi nas 14, 15]

Halartan taro yana taimaka mana mu tuna da ranar Jehovah

[Hotuna a shafi na 16]

Da akwai hanyoyi dabam dabam na yabon Jehovah a taro na Kirista

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba