Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 11/1 pp. 21-25
  • Nuna Daraja Ga Taronmu Masu Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Nuna Daraja Ga Taronmu Masu Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Taro a Isra’ila ta Dā
  • Taronmu Masu Tsarki Ne
  • Hanyoyi da Za Mu Daraja Taronmu
  • Halin da Ya Dace da Iyalin Allah
  • Fasali Na Dindindin a Bautarmu
  • Ta Yaya Za Ka Amfana Daga Taron Shaidun Jehobah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Rika Halartan Taro don Ibada?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Yadda Jehovah Yake Bishe Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Kana Sa Hannu Wajen Sa Taron Kirista Ya Kasance Da Ban Ƙarfafa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 11/1 pp. 21-25

Nuna Daraja Ga Taronmu Masu Tsarki

‘Zan kawo su wurin dutsena mai-tsarki, in faranta zuciyarsu a cikin gidana na addu’a.’—ISHAYA 56:7.

1. Wane dalili ne da ke cikin Nassosi ya sa muke daraja taronmu?

JEHOBAH ya tattara mutanensa shafaffu Kiristoci da abokansu, su bauta masa a ‘dutsensa mai-tsarki.’ Yana faranta zuciyarsu a cikin ‘gidansa na addu’a,’ wato haikalinsa na ruhaniya, wanda shi ne “gidan addu’a domin dukan al’ummai.” (Ishaya 56:7; Markus 11:17) Wannan yana nuna cewa bautarmu ga Jehobah abu ne mai tsarki, mai tsabta kuma mai ɗaukaka. Idan muka daraja taronmu da kuma bautarmu ga Jehobah, za mu nuna cewa muna daraja abubuwa masu tsarki na Jehobah.

Taro a Isra’ila ta Dā

2. Menene ya nuna cewa Jehobah yana daraja wurin da ya zaɓa don bautarsa, kuma ta yaya ne Yesu ya nuna cewa shi ma yana daraja wurin bautar?

2 A Isra’ila ta dā, ana ɗaukan wurin da Jehobah ya zaɓa domin bautarsa da tsarki. Ana kuma tsarkake mazauninsa da abubuwan da ke cikinsa da kuma tukwanensa, “domin su zama mafificin tsarki.” (Fitowa 30:26-29) Ana kiran ɓangarori biyu na mazaunin “Wuri Mai-tsarki da kuma “Mai-tsarki na tsarkaka.” (Ibraniyawa 9:2, 3) Daga baya kuma aka canja mazaunin zuwa haikali a Urushalima. Shi ya sa ake kiran cibiyar bauta ta Jehobah a Urushalima “birni mai-tsarki.” (Nehemiah 11:1; Matta 27:53) A lokacin da ya yi hidimarsa a duniya, Yesu da kansa ya daraja haikalin. Shi ya sa ya fusata sa’ad da mutane suka nuna rashin daraja ga haikalin, suka mai da wurin ya zama wurin kasuwanci da kuma wurin ɗaukan kaya zuwa wasu ɓangarori na Urushalima.—Markus 11:15, 16.

3. Menene ya nuna cewa taron Isra’ila mai tsarki ne?

3 Isra’ilawa suna taruwa kullum domin su bauta wa Jehobah kuma su saurari karatu daga Kalmarsa. Ana kiran wasu kwanaki na idodinsu taro mai tsarki ko kuma taro mai muhimmanci sosai, wanda yake nuna cewa wannan taron mai tsarki ne. (Leviticus 23:2, 3, 36, 37) A wani taron da aka yi a zamanin Ezra da Nehemiah, Lawiyawa sun “fahimtadda jama’a shari’a.” Tun da yake “dukan mutane suna kuka lokacinda suka ji zantattukan shari’an,” Lawiyawa “suka kawaitadda jama’a duka, suna cewa, Ku yi shuru, gama tsatsarkar rana ce.” Sa’an nan Isra’ilawa suka yi bikin kwana bakwai na Idin Bukkoki da “farin ciki ƙwarai.” Bugu da ƙari, ‘Kuma rana kan rana, tun daga rana ta fari har rana ta ƙarshe, sukan karanta daga cikin littafin shari’ar Allah. Suka yi kwana bakwai suna kiyaye idi; rana ta takwas kuwa taro mai-saduda, bisa ga farilla.’ (Nehemiah 8:7-11, 17, 18) Hakika, wannan taro ne mai tsarki da ke bukatar waɗanda suka halarci taron su saurara sosai.

Taronmu Masu Tsarki Ne

4, 5. Waɗanne abubuwa ne ake yi a taronmu da suka sa ya zama taro mai tsarki?

4 Hakika, Jehobah ba shi da birni mai tsarki a duniya, da ke ɗauke da haikali na musamman da aka keɓe domin bautarsa. Duk da haka, kada mu manta cewa taro na bauta wa Jehobah abu ne mai tsarki. Sau uku a sati, muna taruwa don mu karanta Littafi Mai Tsarki kuma mu yi nazarin Nassosi. Ana bayyana Kalmar Jehobah ‘sosai’ kuma kamar a zamanin Nehemiah, ana “bada fasararsa.” (Nehemiah 8:8) A duka taronmu muna farawa da addu’a kuma mu kammala da addu’a, kuma a kusan dukansu muna raira waƙar yabo ga Jehobah. (Zabura 26:12) Taronmu na ikilisiya sashe ne na bautarmu kuma yana bukatar mu ba da kai mu kuma saurara sosai a lokacin taro.

5 Jehobah yana yi wa mutanensa albarka idan sun taru domin su bauta masa, su yi nazarin Kalmarsa, kuma su ji daɗin zumunci da ’yan’uwa Kirista. Idan lokacin taro ya kai, muna da tabbaci cewa nan ne ‘Ubangiji ya umurta albarkarsa.’ (Zabura 133:1, 3) Za mu kasance masu albarka idan muka halarci taron kuma muka saurara sosai. Bugu da ƙari, Yesu ya ce: “Gama wurinda mutum biyu ko uku sun taru cikin sunana, nan ni ke a tsakiyarsu.” Hakika, wannan furcin yana nuni ne ga taron dattawa Kiristoci a inda suke daidaita matsaloli masu tsanani tsakanin mutane, amma kuma ya shafi taronmu. (Matta 18:20) Sa’ad da Kiristoci suka taru a cikin sunansa, Yesu yana kasancewa a taron ta wurin ruhu mai tsarki, to bai kamata ba ne mu tsarkaka taron?

6. Menene za a iya cewa game da wuraren taronmu, manya da ƙanana?

6 Hakika, Jehobah ba ya zama a cikin haikalu da mutane suka gina. Duk da haka, Majami’un mu na Mulki wurare ne na bauta ta gaskiya. (Ayukan Manzanni 7:48; 17:24) Muna taruwa domin mu yi nazarin Kalmar Jehobah, mu yi masa addu’a, kuma mu raira yabonsa. Hakika, haka yake a Majami’un Taro. Manyan gine-gine kamar su majami’ar taro, filin wasan kwallo da aka yi haya domin taro, waɗannan wuraren sun zama wajen bauta a lokacin da ake amfani da su domin taro mai tsarki. Muna bukatar mu daraja manyan taro da kuma ƙananan taro, kuma ya kamata hakan ya bayyana a halayenmu.

Hanyoyi da Za Mu Daraja Taronmu

7. Ta wace hanya ce za mu nuna daraja ga taronmu?

7 Akwai hanyoyi da za mu nuna daraja ga taronmu. Hanya ɗaya ita ce mu kasance a wurin a lokacin da ake raira waƙoƙin Mulki. Ya kamata a rera waƙoƙin da daraja, saboda yawancin kalmomin addu’a ne. Sa’ad da ya yi ƙaulin Zabura sura 22, manzo Bulus ya rubuta game da Yesu: “Zan bayyana sunanka ga ’yan’uwana, A tsakiyar jama’a zan raira yabonka.” (Ibraniyawa 2:12) Saboda haka, mu ƙoƙarta mu zauna kafin mai kujera ya gabatar da waƙa, sa’an nan mu raira waƙa kuma mu kula da ma’anar kalmomin. Bari waƙoƙinmu su kasance kamar na mai zabura da ya ce: “Zan yi godiya ga Ubangiji da dukan zuciyata, A cikin fadar masu-adalci, da cikin taron jama’a kuma.” (Zabura 111:1) Hakika, raira waƙar yabo ga Jehobah shi ne dalilin da ya sa ya kamata mu kasance a wurin taro tun da wuri kuma mu tsaya har ƙarshe.

8. Wane misali ne a cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna bukatar mu saurara sosai sa’ad da ake addu’a a taronmu?

8 Wani abin da yake tsarkaka duka taronmu shi ne, addu’a da ake yi daga zuciya domin waɗanda suka halarci taron. Akwai lokacin da Kiristoci na ƙarni na farko a Urushalima suka taru suka ɗaga “muryarsu ga Allah da nufi ɗaya” a cikin addu’a. A sakamakon haka, sun ci gaba da ‘faɗin maganar Allah da ƙarfin zuciya’ duk da tsanantawa. (Ayukan Manzanni 4:24-31) Kana ganin cewa a cikin waɗanda suka halarci taron, akwai wanda ya ƙyale wani abu ya ɗauke masa hankali? A’a, sun yi addu’ar da “nufi ɗaya.” Addu’o’in da ake yi a taronmu suna nuna yadda mutanen da suka halarci taron suke ji. Muna bukatar mu saurara sosai a lokacin da ake addu’a.

9. Ta yaya za mu nuna darajarmu ga taronmu masu tsarki ta wurin adonmu da kuma hali?

9 Bugu da ƙari, za mu nuna muna daraja wurin taronmu ta yadda muke sa tufafi. Yadda muke sa tufafi da kuma adon gashinmu za su nuna yadda muke daraja taronmu. Manzo Bulus ya ba da shawara: “Ina ta so maza su yi addu’a cikin kowane wuri, suna cira hannuwa masu-tsarki, ba da fushi ba, ba kuwa da jayayya ba. Hakanan kuma, mata su yafa tufafi na ladabi tare da tsantseni da hankali; ba da tubkakken gashi ba, ko da zinariya ko da lu’ulu’ai, ko da tufafi masu-yawan tamani; amma ta wurin kyawawan ayyuka (abinda ya dace ga mata masu-shaidan ibada ke nan).” (1 Timothawus 2:8-10) Sa’ad da muka halarci manyan taro a filin wasa marar rumfa, ya kamata mu sa tufafi masu kyau da suka dace da yanayin. Bugu da ƙari, yadda muke daraja taron zai sa mu daina cin abu ko kuma tauna cingam a lokacin manyan taro da na gunduma. Yin ado mai kyau da kuma nuna hali mai kyau a lokacin taronmu yana daraja Jehobah, bautarsa, da kuma ’yan’uwanmu.

Halin da Ya Dace da Iyalin Allah

10. Ta yaya ne manzo Bulus ya nuna cewa muna bukatar halin da ya dace a taron Kirista?

10 A 1 Korinthiyawa, sura 14, manzo Bulus ya ba da shawara mai kyau game da yadda za a gudanar da taron Kirista. Ya kammala da cewa: “A yi abu duka da hankali bisa ga ƙa’ida.” (1 Korinthiyawa 14:40) Taronmu sashe ne masu muhimmanci a ikilisiyar Kirista, kuma ana bukatar mu nuna halin da ya dace da iyalin Jehobah a wurin.

11, 12. (a) Menene ya kamata a koya wa yara da suke halartar taronmu? (b) Ta yaya ne yara za su iya bayyana bangaskiyarsu a taronmu?

11 Musamman yara, suna bukatar a koyar da su yadda za su yi a taronmu. Ya kamata iyaye su bayyana wa ’ya’yansu cewa Majami’ar Mulki da Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya ba wajen wasa ba ne. Wurare ne da muke bauta wa Jehobah kuma muke nazarin Kalmarsa. Sarki Sulemanu mai hikima ya rubuta: “Lura da ƙafarka sa’anda ka tafi gidan Allah; gama zuwa garin ji ya fi.” (Mai-Wa’azi 5:1) Musa ya koya wa Isra’ilawa su tattara jama’a manya da “ƙanana.” Ya ce: ‘Ka tattara jama’a . . . domin su ji, su koya, su ji tsoron Ubangiji Allahnka, su kiyaye dukan zantattukan wannan shari’a domin su aikata; ’ya’yansu kuma, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koya tsoron Ubangiji Allahnku.’—Kubawar Shari’a 31:12, 13.

12 Haka nan ma a yau, yara suna halartar taro da iyayensu domin su ji kuma su koya. Idan suka iya saurara suka kuma fahimci aƙalla muhimman gaskiya na Littafi Mai Tsarki, yara za su iya “shaida” bangaskiyarsu ta wurin ba da gajerar kalami a taro. (Romawa 10:10) Yaro ƙarami zai iya fara amsa tambaya a gajerar kalmar da ya fahimta. Da farko, wataƙila zai karanta amsar, amma da shigewar lokaci, zai yi ƙoƙari ya yi bayani da kalmarsa. Wannan yana da muhimmanci ga yaron, kuma irin wannan bayani na bangaskiya yana faranta zuciyar manya da suka halarci taron. Hakika, iyaye za su nuna misali ta wurin yin kalami. Yana da kyau yara suna da na su Littafi Mai Tsarki, littafin waƙa, da kuma littafin da ake nazarinsa. A koya masu yadda za su daraja littattafan. Duka waɗannan abubuwan za su sa yara su fahimci cewa taronmu masu tsarki ne.

13. Menene begenmu game da waɗanda suka halarci taronmu da farko?

13 Hakika, ba ma son taronmu ya zama kamar na cocin Kiristendom. Kada ya zama wurin da ake nuna halin ko in kula, da kuma wurin da mutane ke nuna sun fi wasu tsarki ko kuma inda ake yawan surutu kamar inda ake kiɗe-kiɗe. Muna son taron da muke yi a Majami’ar Mulki ya zama mai ƙarfafawa kuma mai jawo mutane, kada ya zama kamar inda mutane suke taruwa don yin hira. Muna taruwa ne domin mu bauta wa Jehobah, saboda haka, ya kamata mu riƙa tsarkaka taronmu a koyaushe. Abin da muke so shi ne, bayan waɗanda lokacinsu ne na farko na halartan taron sun gama jin jawabin da aka gabatar kuma suka lura da halinmu da na yaranmu, za su ce: “Allah yana wurinku.”—1 Korinthiyawa 14:25.

Fasali Na Dindindin a Bautarmu

14, 15. (a) Ta yaya za mu guje wa ‘rabuwa da gidan Allahnmu’? (b) Ta yaya ne Ishaya 66:23 ta riga ta cika?

14 Kamar yadda aka ambata a baya, Jehobah yana tattara mutanensa kuma yana faranta zuciyarsu a cikin ‘gidansa na addu’a,’ wato, haikalinsa na ruhaniya. (Ishaya 56:7) Nehemiah wanda mutum ne mai aminci ya tuna wa ’yan’uwansa Yahudawa cewa su daraja haikali na zahiri da arzikinsu. Ya ce: ‘Kada mu rabu da gidan Allahnmu.’ (Nehemiah 10:39) Bugu da ƙari, kada mu yi watsi da gayyatar da Jehobah ya yi mana na yin bauta a ‘gidansa na addu’a.’

15 Ishaya ya nuna muhimmancin kasancewa a taro don bauta, sa’ad da ya annabta: “Za ya zama kuma, daga wani sabon wata zuwa wani, daga wata asabar kuma zuwa wata asabar, dukan masu-rai za su zo su yi sujada a gabana, in ji Ubangiji.” (Ishaya 66:23) Hakan na faruwa a yau. Hakika, a kowane sati na kowane wata, Kiristoci da suka keɓe kansu suna taruwa domin su bauta wa Jehobah. Suna yin haka ta wurin halartar taron Kirista da kuma zuwa hidimar fage. Kana cikin waɗanda suke zuwa ‘su yi sujada a gaban Ubangiji’?

16. Me ya sa ya kamata halartar taro a kowane lokaci ya zama wani sashe na dindindin a rayuwarmu?

16 Ishaya 66:23 tana maganar irin rayuwar da za a yi a sabuwar duniya da Jehobah ya yi alkawarin ta. A lokacin nan, “dukan masu-rai,” a zahiri za su zo daga sati zuwa sati da kuma wata zuwa wata, su yi ‘sujada a gaban’ Jehobah har abada. Tun da yake taruwa don bauta wa Jehobah zai zama sashe na dindindin a rayuwarmu ta ruhaniya a sabuwar duniya, ya kamata halartan tsarkakken taronmu a yau ya zama sashe na dindindin a rayuwarmu.

17. Menene ya sa muke bukatar mu halarci taronmu “balle fa yanzu, da [muke] ganin ranan nan tana gusowa”?

17 Yayin da ƙarshe ke kusatowa, ya kamata mu ƙudurta fiye da dā mu halarci taronmu na Kirista don bauta wa Allah. Domin taronmu abu ne mai tsarki, kada mu bari aiki, ko aikin makaranta, ko makarantar yamma, su hana mu taruwa da ’yan’uwanmu masu bi. Muna bukatar ƙarfafa da ake samu ta wurin tarayya da ’yan’uwanmu. Taronmu na Kirista suna ba mu zarafi na sanin juna, mu ƙarfafa junanmu, kuma mu motsa juna don mu yi “ƙauna da nagargarun ayyuka.” Ya kamata mu yi haka don “ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Saboda haka, ya kamata mu tsarkake taronmu ta wurin halartar taro a kowane lokaci, yin adon da ya dace da kuma nuna hali mai kyau. Ta yin haka, za mu nuna muna daraja abubuwa masu tsarki kamar Jehobah.

Domin Bita

• Menene ya nuna cewa Jehobah yana ɗaukan taron da mutanensa suke yi don su bauta masa da tsarki?

• Menene ake yi a taronmu da suka nuna cewa taron masu tsarki ne?

• Ta yaya ne yara za su nuna darajarsu ga taronmu?

• Me ya sa ya kamata halartar taro a kowane lokaci ya zama wani sashe na dindindin a rayuwarmu?

[Hoto a shafi na 22]

Taruwa don bauta wa Jehobah abu ne mai tsarki a duk inda aka yi shi

[Hoto a shafi na 25]

Ƙananan ’ya’yanmu suna halartar taro domin su ji kuma su koya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba