Ka Yi La’akari Da ‘Yadda Ƙarshen Zai Zama’
A TAFIYAR mu ta rayuwa, muna fuskantar zaɓi masu yawa. Hakika, hikima ce mu nemi sanin inda hanya za ta ƙare kafin mu soma taku na fari cikinta. Wasu sun yi nadama ƙwarai domin shawarar da suka ɗauka. Wataƙila, kai ma ka ce, ‘Da na san hakan zai faru da ban soma ba.’
Ƙwararren matafiyi zai so ya san inda kowace hanya za ta kai shi. Wataƙila zai dubi taswira kuma ya yi magana da mutane da suka san yankin. Hakika, zai mai da hankali ga alamun hanya da ya gani. A tafiyarmu ta rayuwa, ta yaya za ka san hanya mafi kyau da za ka bi? Ga mutanen Isra’ila ta dā, Allah ta bakin Musa ya ce: “Da suna da hikima, da sun gane wannan, Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!”LMT—Kubawar Shari’a 32:29.
Shawara Mafi Kyau
Ba ma bukatar mu yi shakkar inda tafiya ta rayuwa za ta ƙarasa. Domin matsayinsa, Allah ne ya fi dacewa ya ba ’yan adam shawara a kan hanya mafi kyau da za su bi. Ya lura da hanyoyi dabam dabam da ’yan adam suka bi kuma ya gan sakamakonsu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama al’amuran mutum a gaban Ubangiji su ke, ya kan daidaita dukan tafarkunsa.”—Misalai 5:21.
Jehovah yana kula da waɗanda suke ƙaunarsa. Ta wajen Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki ya shirya musu hanya mafi kyau da za su bi. Mun karanta: “Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.” Saboda haka, kafin ka soma bin kowace hanya, hikima ce idan muka nemi shawarar Jehobah kamar yadda Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya yi yayin da ya roƙa: “Ka sa in san tafarkin da zan bi.”—Zabura 32:8; 143:8.
Bin hanyar da amintaccen mai tafiya da ya ƙware ya nuna, zai sa ka kasance da tabbaci da kuma kwanciyar rai. Ba za ka damu da inda hanyar za ta kai ka ba. Dauda ya nemi ja-gorar Jehobah kuma ya bi ta. Saboda haka, ya more kwanciyar zuciya da aka kwatanta da kyau a zabura 23. Dauda ya rubuta: “Ubangiji makiyayina ne; ba zan rasa kome ba. Yana sanya ni in kwanta a cikin makiyaya mai-ɗanya: Yana bishe ni a gefen ruwaye na hutawa. Yana wartsakadda raina: Yana bishe ni a cikin hanyoyin adilci, sabili da sunansa. Hakika, ko tafiya ni ke yi ta tsakiyar kwari na inuwar mutuwa, Ba za ni tsoron kowace masifa ba.”— Zabura 23:1-4.
Menene Ƙarshensu?
Wani matafiyi da ya bi hanya ta rayuwa, mai zabura wanda wataƙila Asaph ne ko wani cikin zuriyarsa ya ce ya ‘kusa ya zāme’ daga hanya. Me ya faru? Ya ga ni’imar mutane marasa gaskiya da muguye kuma ya yi kishin “arzikin masu-mugunta.” A ganinsa su na “zamne a huce tuttur.” Mafi muni, mai zabura ya fara shakkar hikimar bin tafarkin adalci da ya zaɓa.—Zabura 73:2, 3, 6, 12, 13.
Mai zaburar ya shiga wuri mai tsarki na Jehobah, ya yi addu’a kuma ya yi tunani a kan rabon masu mugunta. “Na lura da matuƙarsu,” ya ce. Ya yi tunanin yadda waɗanda yake yin kishinsu za su ƙarata. Ina matuƙarsu? Ya fahimci cewa suna tsaye ne “cikin wurare masu-samtsi” kuma “sun kare sarai da razaizani!” To, tafarkin da mai zaburar yake bi fa? Ya ce: “Bayan wannan kuma za ka karɓe ni zuwa daraja.”— Zabura 73:17-19, 24
Yin bimbini a kan matuƙar waɗanda suka yi arziki ta cuwa-cuwa ya ƙarfafa mai zabura cewa tafarkin da ya bi mai kyau ne. Ya kammala da cewa: “Amma ya yi mani kyau in kusanci Allah.” Kusantar Jehobah Allah kullum yana kawo sakamako masu kyau.—Zabura 73:28.
“Ka San Inda Ka Nufa”
A yau muna iya fuskantar irin waɗannan zaɓi. Za a iya yi maka alkawarin kwangila mai babban riba, ko kuma a gayyace ka ka sa hannun jari cikin wani kasuwanci da zai kawo riba sosai. Hakika, kowane irin kasuwanci yana da haɗarin da ke tattare da shi. Amma ba zai kasance hikima ba idan muka dubi ‘yadda ƙarshen zai zama’ ga abin da muka zaɓa? Menene hakan zai jawo? Zai bukaci ka yi kwanaki ba ka gida kuma ka jawo wa kanka ko abokiyar aurenka matsala? Hakan zai kai ka ne ga yin tarayya marar kyau da abokan kasuwanci ko kuwa waɗanda suke otel da wasu wurare? Ta wajen hangen hanyar da ke gaba, za ka yi zaɓi mai kyau. Ka bi shawarar Sulemanu: “Ka daidaita tafarkin ƙafafunka.”—Misalai 4:26.
Dukanmu muna bukatar mu yi bimbini a kan wannan shawara, musamman ma matasa. Wani matashi ya ranci wani bidiyo da ya san yana cike da hotuna masu ta da sha’awar jima’i. Ya ce bayan da ya kalli bidiyon, ya ta da masa sha’awar jima’i sosai har ya je ya yi jima’i da wata karuwa da ya sani take yankin. A sakamakon haka, ya yi baƙin ciki, lamirinsa ya dame shi kuma ya damu domin yana zaton ya kwashi cuta. Abin da ya faru ya yi daidai da abin da aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki: “Farat ya bi ta, kamar sa mai-tafiya wurin fawa.” Da ma ya yi la’akari da ’yadda ƙarshen zai zama,’ da hakan bai faru ba.— Misalai 7:22, 23.
Ka Dogara da Alamun Hanyar
Galibin mutane za su yadda cewa ba hikima ba ce a yi banza da alamun hanya. Abin baƙin ciki, wasu suna kasancewa da irin wannan halin yayin da suke tafiya a hanya ta rayuwa kuma sa’ad da aka ba da umurni da bai gamshe su ba. Yi la’akari da wasu Isra’ilawa a zamanin Irmiya. Al’ummar tana bukatar ta yanke shawara, kuma Jehobah Allah ya ba su shawara: “ku tambayi hanyoyi na dā inda hanyar kirki ta ke, ku yi tafiya a ciki.” Amma mutanen sun yi taurin kai suka ce ba za su “yi tafiya a ciki ba.” (Irmiya 6:16) Yaya ‘ƙarshen’ tawayensu ya kasance? A shekara ta 607 A.Z, Babiloniyawa suka hallaka birnin Urushalima kuma suka kwashi mazaunansa zuwa bauta.
Idan muka yi banza da hanyar da Allah ya bayar ba za mu taɓa amfana ba. Nassosi sun gargaɗe mu: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.”—Misalai 3:5, 6.
Wasu gargaɗi daga Allah kamar alama ce da take ɗauke da “Kada Ka Shiga.” Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ka shiga hanyar miyagu, kada ka yi tafiya cikin tafarkin mutane masu-mugunta.” (Misalai 4:14) Ɗaya cikin waɗannan ayyuka masu lahani shine aka kwatanta a Misalai 5:3,4: “Gama leɓunan karuwa suna ɗiɗiga zuma, bakinta kuma ya fi mai sulɓi: Amma ƙarshenta da ɗaci ne kamar tafashiya, Da kaifi kamar takobi mai-kaifi biyu.” Ga wasu, yin jima’i da karuwa ko da wata dabam yana ba su sha’awa. Amma yin watsi da alamar da ta ce “Kada ka shiga,” zai kai ne ga bala’i.
Kafin ka soma taku na farko a kan wannan mummunar hanyar, ka tambaye kanka ‘Ina ne wannan zai kai ni?’ Idan ka dakata, ka yi tunani a kan ‘yadda ƙarshen zai zama’ hakan zai iya hana ka yin tafiya da za ta kai ga mummunan sakamako. Cutar sida da wasu cututtuka da ake ɗauka ta jima’i, cikin shege, zubar da ciki, matsala da abokanan zama da kuma lamiri mai sūka sun zama sakamako da waɗanda suka yi watsi da hanyar nan suka fuskanta. Manzo Bulus ya faɗi “yadda ƙarshe zai zama” ga waɗanda suke yin lalata. “Ba za su gāji mulkin Allah ba.”—1Korinthiyawa 6:9, 10.
“Wannan Ita Ce Hanya”
A wasu lokatai ba za mu iya hangan sakamakon shawara da muka yanke ba. Muna matuƙar godiya domin ja-gorancin da Allah yake yi kai tsaye cikin ƙauna. Jehobah ya ce: “Wannan ita ce hanya, ku bi ta.” (Ishaya 30:21) Yaya ‘ƙarshe zai zama’ ga hanyar da Jehobah ya nuna mana? Ko da yake hanyar ƙunƙunta ce kuma mai wuya, Yesu ya ce tana kai wa ga rai na har abada.—Matta 7:14.
Ka dakata ka yi tunani a kan hanyar da ka ke bi. Hanyar mai kyau ce? Ina take kai mutane? Ka nemi ja-gorancin Jehobah cikin addu’a. Ka dubi taswirar, wato Littafi Mai Tsarki. Kana ma iya ka nemi shawarar wani matafiyi da ya ƙware wanda yake ƙoƙarinsa ya bi umurnin Allah. Idan ka lura cewa kana bukatar ka sake hanya, ka yi hakan ba tare da ɓata lokaci ba.
Ko da yaushe matafiyi yana samun ƙarfin gwiwa daga alamun kan hanya da ke tabbata masa cewa yana kan hanyar da ta dace. Idan ka bincika rayuwarka kuma ka lura cewa kana kan hanyar adalci, ana ƙarfafa ka ka ci gaba da tafiya kanta. Lada mafi kyau ta tafiyarka tana nan kusa.—2Bitrus 3:13.
Kowace hanya tana kai wa ga wani waje. Idan ka kai ƙarshen hanyar da ka zaɓa, ina za ka kasance? Yin “da na sani” ba zai taimake ka ba! Saboda haka, kafin ka yi takun da ke gaba, ka dakata, ka tambayi kanka, ‘Yaya ‘ƙarshen zai zama’?
[Box/Hotuna a shafi na 26]
Yaya ‘Ƙarshen Zai Zama’?
Sau tari matasa suna fuskantar jaraba da kuma matsi su gwada wasu abubuwa da suka zama ruwan dare. Ga wasu yanayi da su na iya fuskanta.
◼ Wani ya ce in ka isa na miji ga taba ka sha.
◼ Malamin da yake da aniya mai kyau ya aririce ka ka biɗi ilimi a jami’a.
◼ An gayyace ka zuwa wata liyafar da za a yi facaka da giya da kuma wataƙila ƙwayoyi.
◼ Wani ya ba ka shawara ka sa hotonka da kuma tarihin ka cikin intane.
◼ Wani abokinka ya gayyace ka ka kalli bidiyon da ake nuna ƙarfi ko kuma lalata.
Idan ka fuskanci ɗaya cikin irin waɗannan yanayi, me za ka yi? Za ka ba da kai ne ko kuwa za ka yi la’akari da yadda ƙarshen zai zama’? Za ka kasance da hikima idan ka tambaye kanka: “Ya yiwu mutum shi sa wuta a ƙirjinsa, Tufafinsa su rasa ƙonewa? Ko kuwa a taka garwashi, sawaye su rasa babbakewa?”— Misalai 6:27, 28.