Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/1 pp. 28-29
  • “Idan Ka Isa Kogin Coco, Ka Juya Dama”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Idan Ka Isa Kogin Coco, Ka Juya Dama”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/1 pp. 28-29

Wasiƙa Daga Nicaragua

“Idan Ka Isa Kogin Coco, Ka Juya Dama”

“ZA KA bukaci motar shiga daji, ƙarfen ɗaga mota, da kuma jarkoki cike da man fetur. Ka kasance kuma a shirye domin taɓo mai haɗiye taya. Idan ka isa Kogin Coco, sai ka juya dama.”

Hakika, waɗannan kalmomin ɗan’uwana mai wa’azi a ƙasashen waje bai ƙarfafa ni ba. Duk da haka, ranar wata Talata da safe na fara tafiya ta na halarci taron Kiristoci a Wanblan wani ƙaramin gari a arewacin Nicaragua.

Na tashi da asuba, ina tuƙa motata da ta tsufa amma mai ƙarfi a kan Babbar Hanya da ta haɗa Amirka ta arewa da ta kudu. Da na isa Jinotega sai na bi hanyar da mutanen wurin suke kira feo, wato mummuna. Kafin na fita daga garin, na lura da wasu shaguna biyu, ɗaya ana kiransa Mu’ujizar Allah ɗayan kuma, Tashin Matattu.

Hanyar sai lanƙwasa sai tudu da kwari. Na yi tafiyar hawainiya a waɗannan tudu da kwari. Hanyar ta kai wani tafki da ke wani kwari a kan dutsen da gajimare ya rufe. Ta cikin hazo na ga itatuwa da furanni suka kewaye su.

A wani kwana saura kaɗan na yi karo da wata mota da take tafiya a tsakiyar hanya. Ta fito da baƙin hayaki kuma tayoyinta suna harba duwatsu sa’ad da ta wuce. A nan Nicaragua, za ka ga laƙabin mahaukatan direbobi a rubuce a gilashin mota, kamar su: Mai Nasara, Kunama, Mesa, ko kuma, Maharbi.

Da rana ta yi tsaka na riga na kai filayen Fantasma. A nan, na wuce wani gidan katako. Wajen ya yi kamar da hoto da nake gani a tsohon littafi: Wani tsoho yana zaune a kan benci, ƙare yana barci a ƙarƙashin itace, da kuma shanu biyu suna ɗauke da karkiya mai tayoyin katako. A wani ƙaramin gari, na ga taron yara suna fitowa daga makaranta. Suna sanye da kayan makaranta mai launi shuɗi, sun cika hanya kamar rakuman ruwa a bakin teku.

Rana ta yi zafi sa’ad da na kusa da Wiwili kuma na hangi Kogin nan Coco. Babban kogi ne kuma yana gudu. Na tuna kwatanci da aka yi mini, na juya dama na fara tafiya a kan hanya mai ban tsoro mai nisan mil 23 zuwa Wanblan.

Na yi tuƙi a kan hakika mummunar hanya, motata tana wasa ruwa sa’ad da ta fice ta cikin rafi na takwas ko tara. Na yi ƙoƙari na guji kwari da ke cikin busasshiyar taɓo, sai na yi nasara wajen tada kura. Hakika, “na ƙi jinin ƙura,” kamar mutanen yankin. A ƙarshe, na isa ƙarshen hanyar, a can cikin kwari mai itatuwa ga Wanblan, inda na nufa.

Kamar dai kowa ya riga ya farka da ƙarfe 4:30 washegari. Da yake caran zakaru sun riga sun tashe ni kafin wannan lokacin, na tashi na bi babban hanya. Iska ta cika da ƙanshin burodin da ake gasawa.

Jifa jifa da zane-zane na aljanna a jikin bango. Da kuma zane-zanen talla a jikin wasu bango. Hotuna kuma suna tuna wa mutane abubuwan da gwamnatoci uku da suka shige suka yi alkawari. Da ƙananan ɗakuna da aka gina da kwano.

Ni na fara magana, na yi gaisuwa na ce “Adiós.” Mutane suka yi murmushi suka marabce ni. Muka yi hira a inda da yawan karan motoci da na dawakai da alfadarai.

Iyalai sun riga sun iso domin taron na kwanaki biyu ranar Jumma’a da yamma. Wasu sun zo da ƙafa, wasu da dawakai, wasu kuma cikin mota. Wasu yara ƙanana maza da mata sun yi tafiyar awa shida da takalman roba. Bam da ake binnewa na iya tashi da su, suna kuma bi ta cikin ruwa cike da matsattsaku. Wasu daga wurare masu nisa sun zo da ɗan abinci, shinkafa da aka gauraya da man alade. Me ya sa dukan su suka zo?

Sun zo ne domin su ƙarfafa begensu game da rayuwa mai kyau ta nan gaba. Sun zo a yi musu bayani daga Littafi Mai Tsarki. Sun zo domin su faranta wa Allah rai.

Washegari Asabar. Mutane wajen 300 suka taru, wasu suka zauna a kan bencunan katako wasu kuma a kan kujerun roba a ƙarƙashin rumfar kwano. Iyaye mata suka ba wa jariransu mama. Aladu suka yi ta kuka, zakaru suka yi cara a gonar da take kusa.

Ba da daɗewa ba aka fara zafi, zafin kuma ya zo ya yi yawa. Duk da haka, masu sauraro suka kasa kunne suka mai da hankali ga shawara da gargaɗi da ake bayarwa. Suna bi suna karatu sa’ad da masu jawabi suke karatun Littafi Mai Tsarki, suka yi kuma waƙoƙi da suke da jigo daga Littafi Mai Tsarki, kuma suka saurara da ban girma sa’ad da ake yin addu’a a madadinsu.

Bayan sashen, ni da wasu muka yi wasa tare da yara. Sai muka maimaita abubuwan da yaran suka rubuta. Na nuna musu hoton taurari da damin taurari a kwamfuta ta ta-tafi-da-gidanka. Yaran suka yi ta murmushi, iyayensu kuma suka yi farin ciki.

Kamar dai taron ya yi saurin ƙarewa, kuma dole kowa ya koma gida. Na tashi koma wa gida washegari, zuciyata ta cika da abubuwan da suka faru da kuma ƙaunar sabbin abokane da na samu. Na ƙuduri anniyar yin koyi da su game da yadda zan kasance da wadatar zuci da kuma yin tawakkali ga Allah.

[Hotuna a shafi na 29]

Iyalai sun yi tafiyar mil masu yawa domin su halarci taron da’ira a Wanblan

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba