Ka Sani?
Wane Yare na Yesu Ya Yi?
Akwai saɓani ne tsakanin masana akan yare da Yesu ya yi. Amma sa’ad da shi mutum ne a duniya, kamar dai Yesu ya yi amfani da wani irin Ibrananci da wani karin harshe na Aramaic. Da Yesu ya zo Nazarat na Galili ya karanta annabcin Ishaya da wataƙila an rubuta a harshen Ibrananci. Littafi Mai Tsarki bai ce wai Yesu ya fassara annabcin zuwa Aramaic ba—Lu 4:16-21.
Game da harsuna da ake amfani da su a Falasɗinu da Yesu yake duniya, Farfesa Ernest Wright ya ce: “An fi yin harshen Hellenanci da na Aramaic . . . sojojin Roma da ma’aikatanta suna yin yaren Romanci kuma Yahudawa na gargajiya wataƙila sun yi yaren Ibrananci da juna.” Shi ya sa alamar da Bilatus ya yi akan gungumen Yesu an rubuto ta a cikin harsuna uku, wato Ibrananci, Romanci da Hellenanci. —Yohanna 19:20.
A cikin littafinsa Discoveries From the Time of Jesus, Alan Millard ya ce: “Sa’ad da suke aikinsu irin na yau da kullum wataƙila gwamnonin Roma sun yi Hellenanci kuma mai-yiwuwa sa’ad da Bilatus yake gwada shi, Yesu ya amsa a yaren Hellenanci.” Ko da shike Littafi Mai Tsarki bai ce ko hakan ya kasance ba, abin muhimmanci shine ba a ce wai an yi amfani da mai fasara ba.—Yohana 18:28-40.
Farfesa Wright ya ce: “Ba za mu iya mu tabbata ko yaren da Yesu ya yi Hellenanci ne ko Romanci amma a hidimarsa ya yi amfani da Aramaic ko Ibrananci da harshen Aramaic ya shafe ta sosai.”—Biblical Archaeology, 1962, page243.
Yaya girman duwatsu da ke haikali a Urushalima?
Sa’ad da suke magana da Yesu game da haikalin da ke Urushalima, wani cikin almajirinsa ya ce: “Malam, ka duba, waɗanne irin duwatsu ke nan, waɗanne irin ginegine kuma ke nan!” (Markus 13:1) Yaya girman waɗannan duwatsun?
A lokacin da Yesu yake duniya, Sarki Hirudus ya ƙara girman dakalin magana na haikali kusan so biyu fiye da yadda yake a zamanin Sulemanu. Wannan shine dakali mafi-girma a duniya ta dā mai girman tsawo 1,575 ta tsawo 910. Wasu duwatsun suna da tsawon ƙafa 35, faɗin ƙafa 15, kuma tsawonsu a miƙa wajen ƙafa 10. Ƙasan suna da nauyin tan 50 kowannensu. Wani ma yana da nauyin kusan tan 400 kuma babu wanda ya “kai shi girma a ko’ina a dā,” in ji wani masani.
Sa’ad da yake amsa wa almajiransa, Yesu ya ce: “Ka ga manyan gine-ginen nan? Ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan’uwansa, ba a baje shi ba.” (Mar. 13:2) Da yawa cikin waɗannan manyan duwatsu za a kansu inda suka faɗa sa’ad da sojojin Roma suka ture su a shekara ta 70 K.Z.
[Hoto a shafi na 23]
Dutsen haikali da aka ture wajen daga haikali a Urushalima