Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 8/1 pp. 3-7
  • ‘Ka Guji Yin Gunaguni’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Guji Yin Gunaguni’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Muguwar Jama’a ta Yi Gunaguni a Kan Jehobah
  • Gunaguni a Ƙarni na Farko
  • Ka Mai da Hankali da Mugun Rinjaya na Gunaguni
  • Ka Ɗauki Abubuwa Bisa Ra’ayin Jehobah
  • Gafartawa na Kawo Haɗin Kai
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Da Zuciya Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Mai Da Hankali Ga Alherin Kungiyar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Kāre Hali Mai Kyau na Ikilisiyar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Jehobah Yana Ɗaukan Tawali’u da Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 8/1 pp. 3-7

‘Ka Guji Yin Gunaguni’

“Sai ku aikata abu duka banda gunaguni.”—FILIBBIYAWA 2:14.

1, 2. Wane gargaɗi ne manzo Bulus ya yi wa Kiristocin da ke Filibbi da kuma Koranti, kuma me ya sa?

MANZO Bulus ya yaba wa ikilisiyar Kirista da ke Filibbi a wasiƙar da Allah ya hura shi ya rubuta musu a ƙarni na farko. Ya yaba wa ’yan’uwansa masu bi da ke wannan birnin don halinsu na karimci da kuma himma, kuma ya furta farin cikinsa game da nagargarun ayyukansu. Duk da haka, Bulus ya tuna musu su “aikata abu duka banda gunaguni.” (Filibbiyawa 2:14) Me ya sa manzon ya ba da wannan gargaɗin?

2 Bulus ya san matsala da gunaguni ke jawowa. ’Yan shekaru da suka shige, ya tuna wa ikilisiyar da ke Koranti cewa yin gunaguni yana da lahani. Bulus ya faɗi cewa sa’ad da Isra’ilawa suke cikin jeji, sun sa Jehobah fushi a kai a kai. Ta yaya? Ta wurin son yin mugayen abubuwa, bautar gunki da fasikanci, ta wajen gwada Jehobah da kuma yin gunaguni. Bulus ya ƙarfafa Korantiyawa su koya daga waɗannan misalan. Ya rubuta: “Kada ku yi gunaguni kuma, kamar yadda waɗansu daga cikinsu suka yi, suka lalace a hannun mai-halakarwa.”—1 Korinthiyawa 10:6-11.

3. Me ya sa batun gunaguni yake da muhimmanci a yau?

3 Da yake mu bayin Jehobah ne na zamani, muna nuna hali irin na ikilisiya da ke Filibbi. Muna da himma don nagargarun ayyuka kuma muna ƙaunar juna. (Yohanna 13:34, 35) Amma, domin matsala da gunaguni ya haddasa tsakanin mutanen Allah a dā, muna da dalili mai kyau mu bi wannan gargaɗin: “Ku aikata abu duka banda gunaguni.” Bari mu fara bincika misalan gunaguni da aka ambata a cikin Nassosi. Sa’annan za mu tattauna wasu abubuwa da za mu iya yi don kada gunaguni ya jawo matsala a yau.

Muguwar Jama’a ta Yi Gunaguni a Kan Jehobah

4. Ta yaya ne Isra’ilawa suka yi gunaguni a cikin jeji?

4 An yi amfani da kalmar Ibrananci da ke nufin ‘gunaguni, mita, ko gurnani a cikin Littafi Mai Tsarki game da abubuwan da suka faru shekaru 40 da Isra’ilawa suka yi a cikin jeji. Akwai lokacin da Isra’ilawa ba su gamsu ba da yanayinsu, kuma suka nuna haka ta wajen yin gunaguni. Alal misali, ’yan makonni kawai bayan an cece su daga bauta a Masar, “dukan jama’ar ’ya’yan Isra’ila suka yi gunaguni bisa Musa da Haruna.” Isra’ilawa sun yi gunaguni game da abinci, suna cewa: “Da ma muka mutu ta hannun Ubangiji cikin ƙasar Masar, lokacin da muka zauna wurin tukanen nama, muna cin gurasa muna ƙoshi: gama kun fito da mu kun kawo mu wannan faƙo, domin ku kashe dukan taron nan da yunwa.”—Fitowa 16:1-3.

5. Sa’ad da Isra’ilawa suka yi gunaguni, a kan wa ainihi suka yi gunagunin?

5 Hakika, Jehobah ya biya bukatar Isra’ilawa a cikin jeji, ya yi musu tanadin abinci da ruwa. Babu batun cewa mutanen Isra’ila za su mutu don rashin abinci a cikin jeji. Amma don ba su gamsu ba, sun zuguiguita yanayinsu kuma suka soma gunaguni. Ko da yake Musa da Haruna ne suke yi wa gunaguni, amma a gaban Jehobah shi ne ainihi suke wa gunaguni. Musa ya gaya wa Isra’ilawa: “Ubangiji yana jin gunagunin da ku ke yi bisansa: mu fa, mi mu ke? ba mu ne ku ke yin gunaguni bisanmu ba, amma bisa Ubangiji ne.”—Fitowa 16:4-8.

6, 7. Ta yaya halin Isra’ilawa ya canja kamar yadda aka nuna a Litafin Lissafi 14:1-3?

6 Ba da daɗewa ba, Isra’ilawa suka sake yin gunaguni. Musa ya aika mutane 12 su leƙo asirin Ƙasar Alkawari. Guda goma cikinsu suka dawo da mummunan rahoto. Menene sakamakon? “Dukan ’ya’yan Isra’ila fa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna: dukan jama’a suka ce masu, da ma mun mutu cikin ƙasar Masar! da ma mun mutu cikin jejin nan! Don menene fa Ubangiji ya kawo mu cikin wannan ƙasa [Kan’anan], mu fāɗi ta kaifin takobi? matayenmu da ƙanananmu za su zama ganima: ba gwamma mu koma Masar ba.”—Litafin Lissafi 14:1-3.

7 Halin mutanen Isra’ila ya canja! Da farko, godiya don an sake su daga Masar da kuma cetonsu daga Jar Teku ya motsa su su rera wa Jehobah waƙar yabo. (Fitowa 15:1-21) Da yake za su fuskanci matsala a cikin jeji da kuma tsoron mutanen Kan’ana, mutanen Allah sun nuna halin rashin gamsuwa maimakon su yi godiya. Maimakon su gode wa Allah don ’yancinsu, sun ɗora masa alhakin abin da suke ganin hani ne. Gunaguni rashin godiya ne ga tanadin Jehobah. Shi ya sa ya ce: “Har yaushe zan jimre da wannan mugunyar jama’a da ke gunaguni a kaina?”—Litafin Lissafi 14:27; 21:5.

Gunaguni a Ƙarni na Farko

8, 9. Ka ambata misalan gunaguni da aka rubuta a Nassosin Kirista na Helenanci.

8 Misalai na baya sun ƙunshi mutane ne da suka nuna rashin gamsuwarsu a fili. Lokacin da Yesu Kristi yake a Urushalima don Idin Bukkoki a shekara ta 32 A.Z., an ‘yi gardama dayawa a cikin taro a kansa.’ (Yohanna 7:12, 13, 32) Suna maganarsa a raɗe, waɗansu suna cewa mutum ne nagari, wasu kuma suka ce ba haka ba.

9 A wani lokaci, an gayyaci Yesu da almajiransa zuwa gidan Lawi, ko Matiyu, mai karɓan haraji. “Farisawa da marubutansu suka yi ma almajiransa gunaguni, suka ce, Don menene ku ke ci da sha tare da masu-haraji da masu-zunubi?” (Luka 5:27-30) Wani lokaci a Galili, “Yahudawa fa suka yi gunaguni a kansa [Yesu], saboda ya ce, Ni ne gurasa wadda ta sauko daga cikin sama.” Har wasu ma cikin mabiyan Yesu sun ji haushin abin da ya faɗa kuma suka soma gunaguni.—Yohanna 6:41, 60, 61.

10, 11. Me ya sa Yahudawa masu jin Helenanci suka yi gunaguni, ta yaya dattawa za su amfana daga yadda suka bi da gunagunin?

10 Sakamakon gunaguni da aka yi jim kaɗan bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z, mai kyau ne. Almajirai sababbi da yawa daga wasu ƙasashe ban da Isra’ila suna moran karimci na ’yan’uwa masu bi a Yahudiya, amma matsala ta taso game da raba gudummawa. Labarin ya ce: “Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni, domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, wajen rabon gudummawa kowace rana.”—Ayukan Manzanni 6:1.

11 Waɗannan masu gunaguni ba kamar Isra’ilawa da suke cikin jeji ba ne. Yahudawa masu jin Helenanci ba su furta rashin gamsuwarsu game da yanayinsu a rayuwa ba don son kai. Sun yi magana a kan rashin kula da bukatun wasu gwauraye. Ban da haka, masu gunagunin ba su aikata kamar ’yan rigima ba kuma ba su yi gunaguni a fili a kan Jehobah ba. Sun kai ƙara ne ga manzanni, waɗanda suka aikata nan da nan domin ƙara da aka kai ya dace. Manzannin sun kafa wa dattawa a yau misali mai kyau! Waɗannan makiyaya na ruhaniya suna mai da hankali don kada su ‘toshe kunnuwansu ga jin kukan talaka.’—Misalai 21:13; Ayukan Manzanni 6:2-6.

Ka Mai da Hankali da Mugun Rinjaya na Gunaguni

12, 13. (a) Ka kwatanta sakamakon gunaguni. (b) Menene zai sa mutum ya yi gunaguni?

12 Yawancin misalai na Nassi da muka bincika sun nuna cewa gunaguni ya jawo matsala tsakanin mutanen Allah a dā. Saboda haka, yana da kyau mu yi tunani sosai game da mummunar rinjayar da gunaguni za ta iya jawowa a yau. Wannan misali zai taimaka. Ainihi ƙarafa da yawa suna yin tsatsa. Idan aka yi banza da ƙarfe lokacin da ya soma tsatsa, zai yi tsatsa da har ba za a iya yin amfani da shi ba. An daina yin amfani da motoci da yawa ba don injin motocin ba ya aiki ba ne, amma domin ƙarafan da aka ƙera su da shi sun yi tsatsa sosai, shi ya sa motocin suke da haɗari. Ta yaya za mu yi amfani da wannan misalin don gunaguni?

13 Kamar yadda wasu ƙarafa sukan yi tsatsa, ’yan adam ajizai suna da halin gunaguni. Ya kamata mu mai da hankali mu fahimci alamar wannan. Kamar yadda laima da gishiri ke sa ƙarfe ya yi tsatsa da sauri, wahala tana sa mu fi yin gunaguni. Wahala za ta iya sa ɗan kasawa ya zama babban matsala. Yayin da yanayi a kwanaki na ƙarshe na wannan zamani ke suƙuƙucewa, abubuwa da za su kawo gunaguni za su ƙaru. (2 Timothawus 3:1-5) Saboda haka, wani bawan Jehobah zai iya soma gunaguni game da wani. Abin da zai iya kawo wannan zai zama batu da ba shi da muhimmanci, kamar su rashin gamsuwa da kasawar wani, iyawa, ko kuma gatar hidima.

14, 15. Me ya sa ya kamata mu bincika ko muna da halin gunaguni?

14 Ko da menene dalilin baƙin cikinmu, idan muka ci gaba da halinmu na gunaguni, zai sa mu zama masu rashin gamsuwa kuma mu zama masu gunaguni a kai a kai. Hakika, mummunan sakamako na gunaguni a ruhaniya zai iya lalata mu gabaki ɗaya. Sa’ad da Isra’ilawa suka yi gunaguni game da rayuwa a cikin jeji, sun ɗora wa Jehobah alhaki. (Fitowa 16:8) Kada wannan ya faru da mu!

15 Za a iya hana ƙarfe yin tsatsa ta wajen shafa masa fenti da ke hana tsatsa da kuma gyara wasu wurare da suka soma tsatsa. Hakanan ma, idan muka gane cewa muna da halin gunaguni za mu iya rage wannan ta wajen yin addu’a nan da nan game da batun. Ta yaya?

Ka Ɗauki Abubuwa Bisa Ra’ayin Jehobah

16. Ta yaya za mu daina halin gunaguni?

16 Gunaguni na sa mu mai da hankali a kanmu da kuma matsalarmu kuma mu mance da albarka da muke morewa da yake mu Shaidun Jehobah ne. Don mu sha kan halin gunaguni, muna bukatar mu riƙa tuna wa kanmu wannan albarka. Alal misali, kowannenmu na da gata mai girma na zama mai ɗauke da sunan Jehobah. (Ishaya 43:10) Muna iya ƙulla dangantaka na kud da kud da shi, kuma za mu iya yi wa “mai-jin addu’a” magana a kowane lokaci. (Zabura 65:2; Yaƙub 4:8) Rayuwarmu tana da ma’ana domin mun fahimci batun ikon mallaka kuma mun san cewa gatarmu ne mu kasance da aminci ga Allah. (Misalai 27:11) Za mu iya fitan wa’azin bisharar Mulki a kai a kai. (Matta 24:14) Ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu Kristi na taimaka mana mu kasance da lamiri mai kyau. (Yohanna 3:16) Waɗannan ne albarkatai da muke morewa ko da menene muke jimrewa.

17. Me ya sa za mu yi ƙoƙari mu ga al’amura bisa ra’ayin Jehobah, ko idan muna da dalili mai kyau na yin gunaguni?

17 Bari mu yi ƙoƙari mu ga abubuwa yadda Jehobah yake ganinsu, ba bisa namu ra’ayi kawai ba. Mai Zabura Dauda ya rera waƙa, yana cewa: “Ya Ubangiji, ka nuna mini tafarkunka; ka koya mini hanyoyinka.” (Zabura 25:4) Idan muna da dalili mai kyau na yin gunaguni, Jehobah yana gani. Yana iya ya magance batun nan da nan. Amma, me ya sa wani lokaci yake barin wahala ta ci gaba? Mai yiwuwa domin ya taimake mu mu koyi halaye masu kyau, kamar su haƙuri, jimiri, bangaskiya, da tsawon jimrewa.—Yaƙub 1:2-4.

18, 19. Ka ba da misalin sakamakon jimrewa da yanayi mai wuya ban da yin gunaguni.

18 Jimre wa irin waɗannan matsaloli ba tare da yin gunaguni ba, yana taimakon mu mu kyautata mutuntakarmu kuma mu burge waɗanda suke lura da halinmu. A shekara ta 2003, wani rukunin Shaidun Jehobah suna tafiya daga Jamus cikin mota don su halarci taron gunduma a Hungary. Direban motar ba Mashaidi ba ne, kuma ba ya son ya kasance da Shaidun har tsawon kwanaki goma. Amma a ƙarshen tafiyar ya canja ra’ayinsa gaba ɗaya. Me ya sa?

19 A lokacin da suke tafiya, abubuwa da yawa sun faru. Amma Shaidun ba su yi gunaguni ba. Direban ya ce wannan ne fasinjoji mafiya kyau da ya taɓa ɗauka! Ya yi alkawari cewa duk lokacin da Shaidu suka zo gidansa, zai marabce su kuma ya saurare su sosai. Fasinjojin sun burge shi domin sun “aikata abu duka banda gunaguni!”

Gafartawa na Kawo Haɗin Kai

20. Me ya sa ya kamata mu riƙa gafarta wa juna?

20 Idan wani ɗan’uwa mai bi ya yi mana laifi fa? Idan batun mai tsanani ne, ya kamata mu yi abin da Yesu ya ce, yadda yake rubuce a Matta 18:15-17. Ba koyaushe ba ne za a yi wannan da yake yawancin laifin ba masu tsanani ba ne. Ka ɗauki yanayin cewa zarafi ne na yin gafara. Bulus ya rubuta: “Kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowanne mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku, hakanan kuma sai ku yi: gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kolossiyawa 3:13, 14) A shirye muke mu gafarta? Jehobah yana da dalilin yin ƙara game da mu. Duk da haka, yana juyayi kuma yana gafartawa a kai a kai.

21. Ta yaya gunaguni zai shafi waɗanda suke saurarawa?

21 Ko da menene matsalar, yin gunaguni ba zai gyara al’amura ba. Ma’anar kalmar Ibrananci da ke nufin “gunaguni” yana iya zama “gurnani.” Babu shakka, ba za mu saki jiki wurin wanda koyaushe yana gunaguni ba, ba za mu ma yi kusa da shi ba. Idan mu ma muka yi gunaguni ko kuma gurnani, waɗanda suke saurarar mu, su ma ba za su kusance mu ba. Hakika, ba za su saki jiki da mu ba kuma ba za su yi tarayya da mu ba! Gurnani zai iya jawo hankalin wani wurinmu, amma ba zai yi kusa da mu ba.

22. Menene wata yarinya ta ce game da Shaidun Jehobah?

22 Mutanen Jehobah suna son halin gafartawa don yana kawo haɗin kai. (Zabura 133:1-3) A wata ƙasar Turai, wata yarinya mai shekara 17 mai zuwan cocin Katolika ta rubuta wa ofishin reshe na Shaidun Jehobah don ta furta yadda take sha’awar su. Ta ce: “Wannan ita kaɗai ce ƙungiyar da na sani cewa waɗanda suke cikinta ba sa rabuwa don ƙiyayya, haɗama, rashin jimrewa, son kai ko kuma rashin haɗin kai.”

23. Menene za mu tattauna a talifi na gaba?

23 Godiya don dukan albarka ta ruhaniya da muke samu da yake muna bauta wa Jehobah Allah na gaskiya zai taimake mu mu ɗaukaka haɗin kai kuma mu guje wa gunaguni a kan al’amura na wasu mutane. Talifi na gaba zai nuna yadda halaye na ibada zai hana mu yin gunaguni mai lahani, wato yin gunaguni game da ƙungiyar Jehobah na duniya.

Ka Tuna?

• Menene yin gunaguni ya ƙunsa?

• Ta yaya za a iya kwatanta sakamakon gunaguni?

• Menene zai taimake mu mu daina gunaguni?

• Ta yaya son gafartawa zai taimake mu mu guji yin gunaguni?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba