Ka Mai Da Hankali Ga Alherin Kungiyar Jehobah
“Ranmu za ya kwanta da alherin gidanka.”—ZABURA 65:4.
1, 2. (a) Yaya tsarin haikalin zai shafi mutanen Allah? (b) Wane taimako ne Dauda ya ba da don gina haikali?
DAUDA na Isra’ila ta dā yana cikin fitattun mutanen da aka ambata a Nassosin Ibrananci. Wannan makiyayi, mawaƙi, annabi, da kuma sarki ya dogara ga Jehobah Allah ƙwarai. Dangantakar Dauda na kud da kud da Jehobah ya sa shi ya so ya gina wa Allah gida. Gidan nan ko kuma haikali, zai zama cibiyar bauta ta gaskiya a Isra’ila. Dauda ya san cewa tsari na haikalin zai kawo farin ciki da albarka ga mutanen Allah. Shi ya sa Dauda ya rera waƙa cewa: “Mai-albarka ne mutum wanda ka [Jehobah] zaɓa, wanda ka ke sa shi gusa gareka, domin shi zauna cikin gidajenka: Ranmu za ya kwanta da alherin gidanka, wuri mai-tsarki na haikalinka ke nan.”—Zabura 65:4.
2 Ba a yarda Dauda ya ja-goranci gina gidan Jehobah ba. Maimakon haka, an ba wa ɗansa Sulemanu wannan gatar. Dauda bai yi gunaguni ba domin an ba wa wani gatar da yake so sosai. Abin da ya fi masa muhimmanci shi ne a gina haikalin. Ya tallafa wa wannan aikin da dukan zuciyarsa ta wajen ba wa Sulemanu fasalin gini da Jehobah ya ba shi. Ƙari ga haka, Dauda ya tsara Lawiyawa da yawa zuwa rukuni rukuni kuma ya ba da zinariya da azurfa masu yawa don gina haikalin.—1 Labarbaru 17:1, 4, 11, 12; 23:3-6; 28:11, 12; 29:1-5.
3. Wane hali ne bayin Allah suke da shi game da tsarin bauta ta gaskiya?
3 Isra’ilawa masu aminci sun tallafa wa tsarin bauta ta gaskiya a gidan Allah. Da yake mu bayin Jehobah ne na zamani, mu ma muna tallafa wa tsarin bauta a cikin ƙungiyar Jehobah na duniya. Ta haka muna nuna cewa muna da irin halin da Dauda yake da shi. Ba halin gunaguni ba ne. Maimakon haka, muna mai da hankali ga alherin ƙungiyar Allah. Ka yi tunanin abubuwa da yawa masu kyau da za mu iya yin godiya a kansu? Bari mu bincika wasu cikinsu.
Nuna Godiya ga Masu Shugabanci
4, 5. (a) Ta yaya “bawan nan mai-aminci, mai hikima” yake cika aikinsa? (b) Yaya wasu Shaidu suke ji game da abinci na ruhaniya da suke ci?
4 Muna da ƙarfafan dalili na yin godiya don “bawan nan mai-aminci, mai hikima” da Yesu Kristi ya naɗa ya kula da mallakarsa a duniya. Rukunin bawa na Kiristoci da aka shafa da ruhu suna ja-gorar wa’azin bishara, suna shirya taro, kuma suna wallafa littattafai masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki a harsuna fiye da 400. Mutane da yawa a dukan duniya suna cin wannan abinci na ruhaniya “a lotonsa.” (Matta 24:45-47) Ba dalilin yin gunaguni game da abincin.
5 Shekaru da yawa, wata tsohuwa Mashaidiyar Jehobah mai suna Elfi ta sami ƙarfafa da taimako ta wajen yin amfani da gargaɗi na Nassi da ke cikin littattafai da rukunin bawan nan ya wallafa. Godiya ta motsa Elfi ta rubuta: “Menene zan yi ba tare da taimakon ƙungiyar Jehobah ba?” Peter da Irmgard suna bauta wa Allah shekaru da yawa yanzu. Irmgard ta yi godiya ga dukan tanadi da “ƙungiyar Jehobah mai kulawa take yi.” Waɗannan littattafai sun haɗa da waɗanda aka shirya don mutane masu bukatu na musamman, kamar makafi da kurame.
6, 7. (a) Ta yaya ake kula da ayyukan ikilisiyoyi a dukan duniya? (b) Menene wasu suka ce game da sashen ƙungiyar Jehobah ta duniya?
6 Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah, wato, ƙaramin rukunin maza da aka shafa da ruhu mai tsarki da suke hidima a hedkwata na Shaidun Jehobah a Brooklyn, New York ne suke wakiltar ‘bawan nan mai aminci.’ Hukumar Mulki na naɗa bayin Jehobah da suka manyanta su yi hidima a ofishin reshe da ke kula da ayyukan ikilisiyoyi fiye da 98,000 a dukan duniya. Ana naɗa maza da suka cika bukatu na Littafi Mai Tsarki su zama dattawa da bayi masu hidima a waɗannan ikilisiyoyi. (1 Timothawus 3:1-9, 12, 13) Dattawan suna shugabanci kuma suna kiwon garken Allah da aka ce su kula da su cikin ƙauna. Abin farin ciki ne mu kasance cikin garken nan kuma mu shaida ƙauna da haɗin kai da ke tsakanin dukan “ ’yan’uwanci”!—1 Bitrus 2:17; 5:2, 3.
7 Maimakon yin gunaguni, sau da yawa mutane suna furta godiyarsu don ja-gora na ruhaniya da suke samu daga wurin dattawa. Alal misali, yi la’akari da Birgit, mace Kirista mai yara a shekarunta na 30. Ta soma mugun tarayya sa’ad da take matashiya kuma ta kusan faɗawa cikin zunubi. Amma gargaɗin dattawa da ke bisa Littafi Mai Tsarki da taimakon ’yan’uwa masu bi ya taimake ta ta bar wannan mummunar yanayi. Yaya Birgit take ji yanzu? Ta ce: “Ina godiya cewa har ila ina cikin ƙungiyar Jehobah mai ban al’ajabi.” Wani matashi ɗan shekara 17 mai suna Andreas ya ce: “Wannan ƙungiyar Jehobah ne da gaske, ƙungiya mafi kyau a duniya.” Bai kamata mu yi godiya ba ne, don alherin sashen ƙungiyar Jehobah ta duniya?
Waɗanda Suke Shugabanci Ajizai Ne
8, 9. Ta yaya wasu cikin tsaran Dauda suka aikata, yaya shi kuma ya aikata?
8 Hakika, waɗanda aka naɗa su yi shugabanci a bauta ta gaskiya ajizai ne. Dukansu suna kuskure kuma wasu suna da kasawa da suke ƙoƙari sosai su magance. Ya kamata mu dami kanmu game da wannan? A’a. Saboda mutane ma da aka ɗanka wa hakki da yawa a Isra’ila ta dā sun yi kuskure mai tsanani. Alal misali, sa’ad da Dauda yake matashi, an kira shi ya zo ya yi kiɗa don ya sanyaya Sarki Saul da ke cikin damuwa. Daga baya, Saul ya yi ƙoƙari ya kashe Dauda, wanda ya gudu don ransa.—1 Samuila 16:14-23; 18:10-12; 19:18; 20:32, 33; 22:1-5.
9 Wasu Isra’ilawa sun ci amana. Alal misali, Joab shugaban sojoji na Dauda ya kashe Abner, dangin Saul. Absalom ya ƙulla wa babansa Dauda don ya ƙwace sarauta. Ahithophel, mashawarcin Dauda ya ci amanarsa. (2 Samuila 3:22-30; 15:1-17, 31; 16:15, 21) Duk da haka, Dauda bai zama mai gunaguni ba; ko kuma ya juya bayansa ga bauta ta gaskiya. Hakika, ya aikata dabam. Wahala ta sa Dauda ya manne wa Jehobah kuma ya ci gaba da halinsa mai kyau sa’ad da ya gudu saboda Saul. A wannan lokacin Dauda ya rera waƙa: “Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai; gama raina yana fake a wurinka: I, cikin inuwar fukafukanka zan fake, har waɗannan masifu sun wuce.”—Zabura 57:1.
10, 11. Menene Gertrud ta fuskanta sa’ad da take matashiya, kuma menene ta faɗa game da kasawar ’yan’uwa masu bi?
10 Ba mu da dalilin yin gunaguni game da cin amana da ake yi a cikin ƙungiyar Allah a yau. Jehobah ko mala’ikunsa ko kuwa makiyaya na ruhaniya ba sa ƙyale mugaye masu cin amana a cikin ikilisiyar Kirista. Duk da haka, dukanmu na fuskantar ajizanci, namu da na sauran bayin Allah.
11 Sa’ad da take matashiya, an yi wa Gertrud da ta bauta wa Jehobah shekaru da yawa zargin ƙarya cewa tana zamba, kuma ita ba mai shelar Mulki na cikakken lokaci ba ce. Menene ta yi? Gertrud ta yi gunaguni ne game da yadda aka bi da ita? A’a. Jim kaɗan kafin ta mutu a shekara ta 2003 tana ’yar shekara 91, ta yi tunani game da rayuwarta kuma ta ce: “Waɗannan abubuwa da na fuskanta a rayuwata sun koya mini cewa kowane irin kuskure da mutane suka yi, Jehobah ne ke ja-gorar aikinsa, kuma yana amfani da mu mutane ajizai.” Sa’ad da take bi da ajizancin wasu bayin Allah, Gertrud ta yi wa Jehobah addu’a da dukan zuciyarta.
12. (a) Wane mummunar misali ne wasu Kiristoci a ƙarni na farko suka nuna? (b) A kan menene za mu sa zuciyarmu?
12 Tun da yake har yawancin Kiristoci masu aminci ajizai ne, sa’ad da bawa da aka naɗa ya yi kuskure, bari mu ci gaba da “aikata abu duka banda gunaguni.” (Filibbiyawa 2:14) Zai zama abin baƙin ciki idan muka bi mummunar misali na wasu cikin ikilisiyar Kirista ta ƙarni na farko! Almajiri Yahuda ya ce malaman ƙarya na wannan zamani suna “waƙala shugabanci, suna zagin sarautai.” Ƙari ga haka, waɗannan masu laifi “masu-gunaguni ne, masu-ƙunƙuni.” (Yahuda 8, 16) Bari mu ƙi tafarkin masu gunaguni kuma mu kafa zuciyarmu a kan abubuwa masu kyau da muka samu ta wajen ‘bawa mai aminci.’ Bari mu ɗauki alherin ƙungiyar Jehobah da tamani kuma mu “aikata dukan abu banda gunaguni.”
“Wannan Batu da Wuya Ya Ke”
13. Ta Yaya ne wasu suka aikata bisa ga wasu koyarwa na Yesu Kristi?
13 Wasu a ƙarni na farko sun yi gunaguni game da bayin da aka naɗa, wasu kuma a kan koyarwar Yesu. Yadda aka rubuta a Yohanna 6:48-69, Yesu ya ce: “Wanda ya ci namana, ya sha jinina, yana da rai na har abada.” Da jin waɗannan kalmomi, “almajiransa fa mutane dayawa . . . suka ce, Wannan batu da wuya ya ke; wanene ya iya jinsa?” Yesu ya sani cewa “almajiransa suna gunaguni a kan wannan.” Amma “da jin wannan mutane dayawa a cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba.” Amma ba dukan almajiran ba ne suka yi gunaguni. Ga abin da ya faru sa’ad da Yesu ya tambayi manzanninsa 12: “Ku kuma kuna so ku tafi?” Manzo Bitrus ya amsa: “Ubangiji, a wurin wa za mu tafi? kai ne da maganar rai na har abada. Mu kuwa mun rigaya mun bada gaskiya, kuma mun sani kai ne Mai-tsarki na Allah.”
14, 15. (a) Me ya sa wasu suka yi fushi da wasu fannoni na koyarwar Kirista? (b) Menene za mu koya daga abin da ya faru da Emanuel?
14 A wannan zamanin, wasu cikin mutanen Allah sun yi fushi da wasu fannin koyarwa na Kirista kuma sun yi gunaguni a kan sashen ƙungiyar Jehobah ta duniya. Me ya sa hakan ya faru? Sau da yawa rashin fahimtar yadda Allah yake yin abubuwa ne ya sa suke yin hakan. Mahalicci na bayyana wa mutanensa gaskiya ne a hankali. Saboda haka, lokaci lokaci za a yi gyara ga fahiminmu na Nassosi. Yawancin mutanen Jehobah suna farin ciki game da irin wannan gyara. Wasu sun “cika yin adalci” kuma suka ƙi gyare-gyaren. (Mai-Wa’azi 7:16) Wasu don fahariya ne suka faɗa cikin tarkon ’yancin kai. Ko menene dalilin, irin wannan gunaguni yana da lahani, tun da yana iya sa mu koma bin duniya da hanyoyinta.
15 Alal misali, Emanuel Mashaidi ne da ya ga laifin wasu abubuwa da ya karanta a littattafan “bawan nan mai-aminci, mai hikima.” (Matta 24:45) Ya daina karanta littattafanmu na Kirista kuma bayan haka ya gaya wa dattawan ikilisiyarsa cewa ba ya son ya zama Mashaidin Jehobah kuma. Amma, bayan ɗan lokaci Emanuel ya fahimci cewa koyarwa ta ƙungiyar Jehobah daidai ce. Ya nemi Shaidu, kuma ya yarda cewa ya yi kuskure, aka dawo da shi Mashaidin Jehobah. Ta haka, ya sake zama mutum mai farin ciki.
16. Menene zai taimake mu mu sha kan shakka game da wasu koyarwar Kirista?
16 Idan aka jarabe mu mu yi gunaguni domin muna shakkar wata koyarwa na mutanen Jehobah fa? Sai mu yi haƙuri. Daga baya ‘bawa mai aminci’ na iya wallafa wani abu da zai amsa tambayoyinmu kuma ya kawar da shakkarmu. Yana da kyau mu nemi taimakon dattawa. (Yahuda 22, 23) Yin addu’a, da nazari na kanmu, da cuɗanya da ’yan’uwa masu ruhaniya zai iya taimaka mana mu daina shakka, kuma ya sa mu yi godiya sosai domin gaskiya mai ƙarfafa bangaskiya ta Littafi Mai Tsarki da muka koya daga ƙungiyar da Jehobah yake amfani da ita.
Ka Kasance da Hali Mai Kyau
17, 18. Maimakon yin gunaguni, wane hali ya kamata mu kasance da shi kuma me ya sa?
17 Hakika, ’yan adam ajizai suna da halin yin zunubi, kuma wasu suna da halin yin gunaguni da bai dace ba. (Farawa 8:21; Romawa 5:12) Amma idan yin gunaguni ya zama halinmu, za mu sa dangantakarmu da Jehobah Allah cikin haɗari. Saboda haka, muna bukatar mu daina halin yin gunaguni.
18 Maimakon mu riƙa yin gunaguni game da abubuwa da ake yi cikin ikilisiya, yana da kyau mu kasance da halin kirki kuma mu bi tsarin aikin da zai sa mu yi farin ciki, mu daidaita, kuma mu zama sahihai a cikin bangaskiya. (1 Korinthiyawa 15:58; Titus 2:1-5) Jehobah ne ke ja-gorar kome da ake yi a cikin ƙungiyarsa, kuma Yesu yana sane da abubuwa da ke faruwa a kowace ikilisiya, kamar yadda ya sani a ƙarni na farko. (Ru’ya ta Yohanna 1:10, 11) Ka jira Allah da Kristi Shugaban ikilisiya cikin haƙuri. Za a iya yin amfani da makiyaya da suka ƙware wajen daidaita al’amura da ake bukata a gyara.—Zabura 43:5; Kolossiyawa 1:18; Titus 1:5.
19. Har sai Mulkin Almasihu ya soma ja-gorar harkokin ’yan adam, a kan menene za mu mai da hankalinmu?
19 Ba da daɗewa ba wannan mugun zamani zai ƙare, kuma Mulkin Almasihu zai ja-goranci harkokin ’yan adam. Har sai lokacin, yana da muhimmanci kowanenmu ya kasance da hali mai kyau! Wannan zai taimake mu mu fahimci halayen ’yan’uwanmu masu kyau, maimakon mu dinga mai da hankali ga kasawarsu. Mai da hankali ga fannonin mutuntakarsu masu kyau zai sa mu farin ciki. Maimakon mu damu kanmu ta wajen yin gunaguni za mu sami ƙarfafa a ruhaniya.
20. Hali mai kyau zai taimake mu mu more wace albarka?
20 Hali mai kyau zai taimake mu mu tuna da albarka mai yawa da muke morewa domin muna tarayya da sashen ƙungiyar Jehobah ta duniya. Wannan ita kaɗai ce ƙungiya a duniya da take da aminci ga Mamallakin sararin samaniya. Yaya kake ji game da wannan gaskiya da kuma gatar bauta wa Jehobah Allah makaɗaici na gaskiya? Bari halinka ya zama irin na Dauda wanda ya rera waƙa yana cewa: “Mai-jin addu’a, a gareka dukan masu-rai za su zo. Mai-albarka ne mutum wanda ka zaɓa, wanda ka ke sa shi gusa gareka, domin shi zauna cikin gidajenka, ranmu za ya kwanta da alherin gidanka.”—Zabura 65:2, 4.
Ka Tuna?
• Me ya sa ya kamata mu yi godiya ga waɗanda suke shugabanci a cikin ikilisiya?
• Yaya ya kamata mu aikata sa’ad da waɗanda suke shugubanci suka yi kuskure?
• Yaya ya kamata mu ɗauki gyara da ake yi game da fahimtar Nassosi?
• Menene zai taimaki Kirista ya daina shakka?
[Hoto a shafi na 8]
Dauda ya ba Sulemanu fasalin gina haikalin kuma ya tallafa wa bauta ta gaskiya da dukan zuciyarsa
[Hoto a shafi na 11]
Dattawa Kirista suna ba da taimako na ruhaniya da farin ciki