Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 12/1 pp. 14-19
  • Ka Ci Gaba Da Bauta Da Zuciya Ɗaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ci Gaba Da Bauta Da Zuciya Ɗaya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bai Kamata a Yi Tara Ba
  • Kada Ka Yi Gunaguni
  • Ka Guje wa Tsegumi
  • Kada Ka Zartar!
  • Ba Su da Ƙarfi Amma Suna da Daraja
  • Ka Ci Gaba da Bauta da Zuciya Ɗaya
  • ‘Ka Guji Yin Gunaguni’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Kāre Hali Mai Kyau na Ikilisiyar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Mai Da Hankali Ga Alherin Kungiyar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Mutanen Duniya Suna da Yare Daya”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 12/1 pp. 14-19

Ka Ci Gaba Da Bauta Da Zuciya Ɗaya

“Zan juya ma al’ummai da harshe mai-tsarki, domin dukansu su kira sunan Ubangiji, su bauta masa da zuciya ɗaya.”—ZEPHANIAH 3:9.

1. Menene yake faruwa wajen cika Zephaniah 3:9?

MISALIN harsuna 6,000 ake yi a duniya duka. Ban da waɗannan, da akwai yare da sun rabu dabam dabam. Ko mutane suna harsuna da suka bambanta kamar na Arabiya da Zulu, Allah ya yi abu na ban mamaki. Ya sa ya yiwu mutane a ko’ina su koyi harshe ɗaya mai tsarki. Wannan yana aukuwa ne ya cika alkawari da aka yi ta bakin annabi Zafaniya. “Zan [Jehovah Allah] juya ma al’ummai da harshe mai-tsarki, [a zahiri, “leɓe mai tsarki] domin dukansu su kira sunan Ubangiji, su bauta masa da zuciya ɗaya.”—Zephaniah 3:9.

2. Menene “harshe mai-tsarki,” kuma me ya sa ya yiwu?

2 “Harshe mai-tsarki” gaskiyar Allah ce da ke cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Gaskiya ce musamman game da Mulkin Allah, wanda zai tsarkake sunan Jehovah, ya kunita ikon mallakarsa, kuma ya kawo wa mutane albarka. (Matta 6:9, 10) Da yake shi kaɗai ne harshe na ruhaniya mai tsarki a duniya, mutane na dukan al’ummai da ƙabilu ne suke harshe mai tsarki. Yana taimakonsu su bauta wa Jehovah da “zuciya ɗaya.”

Bai Kamata a Yi Tara Ba

3. Menene ke taimaka mana mu bauta wa Jehovah da haɗin kai?

3 Kiristoci, muna godiya da haɗin kan harsuna dabam dabam da ke tsakaninmu. Ko da muna wa’azin bishara na Mulki a harsuna da yawa, muna bauta wa Allah da haɗin kai. (Zabura 133:1) Wannan ya yiwu domin, a ko’ina da muke da zama a duniya, muna harshe ɗaya mai tsarki domin yabon Jehovah.

4. Me ya sa ba za a yi tara ba tsakanin mutanen Allah?

4 Ba za a yi tara ba tsakanin mutanen Allah. Manzo Bitrus ya bayyana wannan sa’ad da ya yi wa’azi a gidan soja na Al’umma Karniliyus a shekara ta 36 A.Z. ya ce: “Hakika na gane Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Tun da wannan gaskiya ne, ikilisiyar Kirista ba wurin yin tara ba ce, rukuni, ko kuma nuna son kai ba.

5. Me ya sa ba shi da kyau mu kafa wani rukuni cikin ikilisiya?

5 Game da ziyararta zuwa Majami’ar Mulki, wata ɗaliba ta ce: “Yadda yake, cococi suna jawo mutanen ƙabila ɗaya ne. . . . Shaidun Jehovah duka sun zauna tare, ba rukuni rukuni ba.” Amma, wasu da suke cikin ikilisiyar Koranti ta dā suna rabuwa zuwa rukuni. Ta haka suna haddasa jayayya, suna hamayya da ayyukan ruhun Allah mai tsarki, don yana ɗaukaka haɗin kai da salama. (Galatiyawa 5:22) Idan za mu ɗaukaka rukuni a cikin ikilisiya, muna gāba da ja-gorar ruhun ke nan. Saboda haka, bari mu tuna da kalmomin Bulus zuwa ga Korantiyawa: “ ’Yan’uwa, ina roƙonku, ta wurin sunan Ubangijinmu Yesu Kristi, dukanku ku yi magana ɗaya, kada tsatsaguwa su kasance a tsakaninku; amma ku zama cikakku cikin hankali ɗaya da shawara ɗaya.” (1 Korinthiyawa 1:10) Bulus ya kuma nanata haɗin kai a wasiƙarsa zuwa Afisawa.—Afisawa 4:1-6, 16.

6, 7. Wane gargaɗi ne Yakubu ya bayar game da son kai, kuma ta yaya kalmominsa suka shafe mu?

6 An bukaci Kiristoci kada su yi tara. (Romawa 2:11) Domin wasu a cikin ikilisiya na ƙarni na farko suna nuna son kai ga mawadata, almajiri Yakubu ya rubuta: “ ’Yan’uwana, kada ku riƙe bangaskiya ta Ubangiji Yesu Kristi, Ubangijin daraja, tare da tara. Gama idan wani mutum ya shigo majami’arku da zobe na zinariya, da tufafi masu-kwarjini, wani fakiri kuma ya shigo da tufafi tsumma; ku kuwa kuna la’akari da wanda ya ke yafe da tufafi masu-kwarjini, ku ce, Ka zauna daganan a wuri mai-kyau; amma ku ce ma fakirin, Ka tsaya dagacan, ko kuwa ka zauna ƙarƙashin matashin sawuna. Ba tara ku ke yi ba a cikin rayukanku, har kun zama masu-shari’a da miyagun tunani?”—Yaƙub 2:1-4.

7 Idan marasa bi mawadata da zobe na zinariya da tufafi masu kwarjini da kuma matalauta marasa bi waɗanda suka saka tsumma suka zo taron Kirista, ana yi wa mawadata maraba ta musamman. Ana ba su kujeru “a wuri mai-kyau,” yayin nan kuma a gaya wa matalauta su tsaya ko su zauna a ƙasa ƙarƙashin matashin sawun wani. Amma Allah da ba ya tara ya yi tanadin hadayar fansa ta Yesu ga mawadata da matalauta. (Ayuba 34:19; 2 Korinthiyawa 5:14) Saboda haka, idan za mu faranta wa Jehovah rai kuma mu bauta masa da zuciya ɗaya, ba za mu nuna son kai ba ko kuma ‘mu yi tara domin ribar kanmu.’—Yahuda 4, 16.

Kada Ka Yi Gunaguni

8. Me ya faru don Isra’ilawa sun yi gunaguni?

8 Domin mu riƙe haɗin kanmu kuma ci gaba da samun tagomashin Allah, dole ne mu yi biyayya ga gargaɗin Bulus: “Sai ku aikata abu duka banda gunaguni.” (Filibbiyawa 2:14) Isra’ilawa marar bangaskiya da aka ’yanto su daga bauta a ƙasar Masar sun yi gunaguni game da Musa da Haruna, har ma da Jehovah Allah. Domin haka, duka maza daga mai shekara 20 zuwa sama, ban da Joshua da Kaleb Lawiyawa masu aminci, ba su shiga Ƙasar Alkawari ba amma sun mutu lokacin tafiyar Isra’ilawa na shekara 40 a cikin daji. (Litafin Lissafi 14:2, 3, 26-30; 1 Korinthiyawa 10:10) Lallai sun ga sakamakon gunaguni!

9. Menene Maryamu ta fuskanta domin ta yi gunaguni?

9 Wannan ya nuna abin da zai iya faruwa ga al’umma gabaki ɗaya da take gunaguni. Mutane da suke gunaguni fa? To, ’yar’uwar Musa, Maryamu tare da ƙaninta Haruna, suka yi gunaguni: “Ubangiji ya yi magana da Musa kaɗai ne? ba ya yi magana kuma da mu ba?” Labarin ya daɗa: “Ubangiji kuwa ya ji.” (Litafin Lissafi 12:1, 2) Menene sakamakon wannan? Maryamu wadda babu shakka ta yi ja-gorar gunagunin, Allah ya wulakanta ta. Ta yaya? An harbe ta da kuturta kuma tilasta mata ta zauna waje da sansanin na kwanaki bakwai har sai an tsarkake ta.—Litafin Lissafi 12:9-15.

10, 11. Gunaguni da idan ba a mai da hankali ba zai kawo wane sakamako? Ka ba da misali.

10 Gunaguni ba kawai ƙara ba ne game da wani abin da ba daidai ba. Masu gunaguni a kai a kai suna damuwa ainu da yadda suke ji ko matsayinsu, suna mai da hankali ga kansu maimakon ga Allah. Idan ba su mai da hankali ba, wannan yana kawo jayayya tsakanin ’yan’uwa masu bi kuma ɓata ƙoƙarinsu na bauta wa Jehovah da zuciya ɗaya. Wannan haka ne domin masu gunaguni koyaushe suna ƙara, babu shakka da tsammanin cewa wasu za su ji tausayinsu.

11 Alal misali, wani zai iya sūkar hanyar da wani dattijo yake ba da jawabinsa cikin ikilisiya ko kuma yadda yake kula da hakkinsa. Idan mun saurari wanda ya kawo ƙarar, za mu iya soma tunani irin nasa. Kafin a shuka irin rashin gamsuwa a zuciyarmu, ayyukan dattijon ƙila ba su dame mu ba, amma yanzu suna damunmu. Bayan haka, ba abin da dattijon zai yi ya zama daidai a idanunmu, mu ma wataƙila za mu soma magana game da shi. Irin wannan halin bai dace ba a ikilisiyar mutanen Jehovah.

12. Me gunaguni zai iya yi ga dangantakarmu da Allah?

12 Gunaguni game da mutane da aikinsu su yi kiwon garken Allah ne zai kai ga alfasha. Irin wannan gunaguni ko kuma tsinewa zai yi lahani ga dangantakarmu da Jehovah. (Fitowa 22:28) Masu alfasha da ba su tuba ba ba za su gaji Mulkin Allah ba. (1 Korinthiyawa 5:11; 6:10) Almajiri Yahuda ya rubuta game da masu gunaguni da suke “waƙala shugabanci, suna zagin sarautai,” ko kuma masu hakki a cikin ikilisiya. (Yahuda 8) Waɗannan masu gunaguni ba su da yardan Allah, ya kamata mu ƙi mummunan tafarkinsu.

13. Me ya sa wasu ƙara suke da kyau?

13 Amma, ba duka ƙara ba suke ɓata wa Allah rai. Bai ƙyale “ƙarar” Saduma da Gwamrata ba amma ya halaka waɗannan miyagun birane. (Farawa 18:20, 21; 19:24, 25) A Urushalima, ba da daɗewa ba bayan Fentakos na 33 A.Z., “gunaguni ya tashi a wurin Helenawa a kan Ibraniyawa, domin aka ƙyale gwaurayensu a cikin raba abinci kowacce rana.” Shi ya sa, “goma sha biyu” suka gyara yanayin ta naɗa “mutum bakwai” bisa “wannan sha’ani” na raba abinci. (Ayukan Manzanni 6:1-6) Dattawa na zamani ba za su ‘toshe kunnuwansu’ ba ga ƙarar da ta yi daidai. (Misalai 21:13) Maimakon kushe wa ’yan’uwa masu bi, ya kamata dattawa su ƙarfafa su kuma su toƙara musu.—1 Korinthiyawa 8:1.

14. Don a guje wa gunaguni, wane hali musamman ake bukata?

14 Dukanmu muna bukatar mu guje wa gunaguni, domin halin gunaguni yana da lahani a ruhaniya. Irin wannan halin zai ɓata haɗin kanmu. Maimakon haka, bari koyaushe mu ƙyale ruhu mai tsarki ya saka ƙauna cikinmu. (Galatiyawa 5:22) Yin biyayya ga ‘doka ta ƙauna da aka ba sarakuna’ za ta taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehovah da zuciya ɗaya.—Yaƙub 2:8; 1 Korinthiyawa 13:4-8; 1 Bitrus 4:8.

Ka Guje wa Tsegumi

15. Yaya za ka bambanta gulma daga tsegumi?

15 Tun da gunaguni zai kai ga gulma, dole mu mai da hankali game da abin da muke faɗa. Gulma magana ce game da mutane da harƙoƙinsu. Tsegumi kuma ƙarya ne da nufin ɓata sunan wani. Irin wannan magana ta ƙiyayya ce da rashin ibada. Saboda haka, Allah ya gaya wa Isra’ilawa: “Ba za ka yi yawon kai da kawowa kana yawon tsegumi a cikin mutanenka.”—Leviticus 19:16.

16. Menene Bulus ya ce game da wasu masu gulma, kuma ta yaya ya kamata gargaɗinsa ya shafe mu?

16 Tun da gulma za ta kai ga tsegumi, Bulus ya tsauta wa wasu masu gulma. Bayan ya ambata gwauraye da suka cancanta ikilisiya ta taimake su, ya yi maganar gwauraye da suka koyi, “su zama ragwaye, suna yawo suna bin gidaje; ba kuwa ragwaye kaɗai ba, amma masu-tsegumi kuma, masu-shishigi, suna faɗin abin da ba ya kamata garesu ba.” (1 Timothawus 5:11-15) Idan mace Kirista ta ga cewa tana da damuwa a irin wannan magana da za ta kai ga tsegumi, zai yi kyau ta yi biyayya ga gargaɗin Bulus ta zama “ma[i]-shimfiɗaɗen hankali, ba ma[i]-tsegumi ba.” (1 Timothawus 3:11) Hakika, maza Kirista dole su ma su guji gulma.—Misalai 10:19.

Kada Ka Zartar!

17, 18. (a) Menene Yesu ya ce game da zartar da ɗan’uwanmu? (b) Ta yaya za mu yi amfani da kalmomin Yesu game da zartarwa?

17 Ko idan ma ba mu tsegunta kowa ba, za mu yi ƙoƙari mu guje zartar da wasu. Yesu ya haramta irin wannan halin sa’ad da ya ce: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku. Gama da irin shari’a da ku ke shar’antawa, da shi za a shar’anta muku: da mudun nan da ku ke aunawa kuma da shi za a auna muku. Don me kuwa ka ke duban ɗan hakin da ke cikin idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke cikin ido naka ba? Ko kuwa ƙaƙa za ka ce ma ɗan’uwanka, bari in cire ɗan hakin daga cikin idonka; ga shi kuwa, gungume yana cikin ido naka? Kai mai-riya, ka fara cire gungume daga cikin ido naka; kāna za ka gani sarai da za ka cire ɗan hakin daga cikin idon ɗan’uwanka.”—Matta 7:1-5.

18 Bai kamata mu ɗauki matsayin cire “ɗan hakin” daga idon ɗan’uwanmu ba don mu taimake shi yayin da “gungume” ta alama ya sa ba za mu iya yin shari’a da ta yi daidai ba. Hakika, idan mun fahimci yadda Allah yake jinƙai, ba za mu so mu zartar da ’yan’uwanmu na ruhaniya ba. Yaya za mu iya fahimtar su yadda Ubanmu na samaniya ya fahimce su? Shi ya sa Yesu ya yi mana kashedi ‘kada mu zartar, domin kada a zartar da mu’! Bincika ajizancinmu sosai ya kamata ya hana mu yin hukunci da Allah ba zai so ba.

Ba Su da Ƙarfi Amma Suna da Daraja

19. Yaya ya kamata mu ɗauki ’yan’uwa masu bi?

19 Idan mun ƙuduri aniya mu bauta wa Allah da zuciya ɗaya da ’yan’uwa masu bi, za mu guji kushe musu. Har ma za mu riƙa ba su girma. (Romawa 12:10) Hakika, za mu nemi abin da zai amfane su, ta yin ayyuka na tawali’u dominsu da farin ciki. (Yohanna 13:12-17; 1 Korinthiyawa 10:24) Ta yaya za mu ci gaba da irin wannan hali mai kyau? Ta tuna cewa kowane mai bi yana da tamani ga Jehovah kuma muna bukatar juna, yadda kowane ɓangare na jikin mutum ke dangana ga sauran.—1 Korinthiyawa 12:14-27.

20, 21. Wace ma’ana ce kalmomin 2 Timothawus 2:20, 21 suke da ita a gare mu?

20 Gaskiya, Kiristoci tukwane ne marasa ƙarfi da aka danka wa hidima mai ɗaukaka. (2 Korinthiyawa 4:7) Idan za mu yi wannan aiki mai tsarki ga yabon Jehovah, dole mu kasance da daraja a gabansa da Ɗansa. Sai kaɗai ta kasancewa da tsabta a ɗabi’a da kuma a ruhaniya za mu ci gaba da zama kaya mai daraja da Allah zai yi amfani da shi. Bulus ya rubuta game da wannan: “A cikin babban gida dai akwai kaya, ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma na itace da na ƙasa; waɗansu zuwa daraja, waɗansu kuwa ƙanƙanci. Idan fa mutum ya tsarkake kansa daga waɗannan, za ya zama santali na zuwa daraja, tsarkake, daidai ga aikaceyar ubangiji, shiryayye zuwa kowane kyakkyawan aiki.”—2 Timothawus 2:20, 21.

21 Mutane da ba sa bi da kansu su jitu da farillan Allah ba ‘kaya ne don ƙasƙantaccen aiki.’ Amma ta bin tafarki ta ibada, za mu zama ‘kaya zuwa daraja, tsarkake, ko a ware, don aikacen Jehovah, shiryayye zuwa kowane kyakkyawan aiki.’ Saboda haka zai yi kyau mu tambayi kanmu: ‘Ni “kaya ne zuwa daraja”? Ina rinjayar ’yan’uwa masu bi a hanya mai kyau kuwa? Ina cikin waɗanda suke aiki da zuciya ɗaya da ’yan’uwa masu bi a ikilisiya?’

Ka Ci Gaba da Bauta da Zuciya Ɗaya

22. Da me za a gwada ikilisiyar Kirista?

22 An tsara ikilisiyar Kirista kamar iyali. Akwai yanayi mai kyau, na taimako a cikin iyali sa’ad da dukan waɗanda suke ciki suna bauta wa Jehovah. Iyali ta ƙunshi waɗanda suke da mutuntaka dabam dabam, amma kowa yana da wuri mai daraja. Haka yanayin yake cikin ikilisiya. Ko da mun bambanta—kuma ajizai ne—Allah ya jawo mu ga kansa ta wurin Kristi. (Yohanna 6:44; 14:6) Jehovah da Yesu suna ƙaunarmu, kuma kamar iyali mai haɗin kai, ya kamata mu ƙaunaci juna.—1 Yohanna 4:7-11.

23. Me ya kamata mu tuna kuma mu ƙudiri aniyar yi?

23 Ikilisiyar Kirista da take kamar iyali wuri ne da za mu samu aminci. Manzo Bulus ya rubuta: “Ina ta so maza su yi addu’a cikin kowane wuri, suna cira hannuwa masu-tsarki, ba da fushi ba, ba kuwa da jayayya ba.” (1 Timothawus 2:8) Da haka Bulus ya haɗa aminci da addu’a “cikin kowane wurin” da Kiristoci suka taru. Maza masu aminci ne kawai za su yi addu’a ga jama’a cikin ikilisiya. Hakika, Allah na bukatar dukanmu mu kasance da aminci gare shi da kuma juna. (Mai-Wa’azi 12:13, 14) Bari mu ƙudiri aniyar yin aiki tare cikin jituwa, kamar ɓangarorin jikin mutum. Bari dukanmu mu yi bauta da haɗin kai na ɓangaren iyalin masu bauta wa Jehovah. Fiye da kome, mu tuna cewa muna bukatar juna kuma za mu more amincewar Allah da albarka idan mun ci gaba da bauta wa Jehovah da zuciya ɗaya.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene ke taimakon mutanen Jehovah su bauta masa da zuciya ɗaya?

• Me ya sa Kiristoci ke guje wa yin tara?

• Me ya sa gunaguni ba shi da kyau?

• Me ya sa za mu daraja ’yan’uwa masu bi?

[Hoto a shafi na 15]

Bitrus ya gano cewa “Allah ba mai tara ba ne”

[Hoto a shafi na 16]

Ka san abin da ya sa Allah ya wulakanta Maryamu?

[Hoto a shafi na 18]

Kiristoci masu aminci suna bauta wa Jehovah da zuciya ɗaya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba