Darassi Game Da Fahariya Dda Tawali’u
WANI abin da ya faru a rayuwar Sarki Dauda ya nuna bambancin tawali’u na gaskiya da mugun fahariya. Ya faru ne bayan da Dauda ya ci Urushalima kuma ya mai da ita babban birninsa. Dauda ya ɗauki Jehobah Sarkin Isra’ila na gaske, saboda haka ya shirya a kawo Sunduƙi da ke wakiltar kasancewar Allah, zuwa birnin. Wannan yana da muhimmanci ga Dauda, shi ya sa ya nuna farin cikinsa a fili sa’ad da yake bin firistoci da suka ɗauki Sunduƙin. Mazaunan Urushalima sun ga sarkinsu “yana tsalle” yana “rawa . . . da iyakacin ƙarfinsa.”—1 Labarbaru 15:15, 16, 29; 2 Samu’ila 6:11-16.
Amma, Mikal matar Dauda ba ta yi farin ciki ba. Da take leƙa daga taga, maimakon ta yi sha’awar yadda Dauda yake yabon Jehobah, “ta kuwa raina shi a zuciyarta.” (2 Samu’ila 6:16) Me ya sa Mikal ta ji hakan? Babu shakka, ta ɗauki matsayinta na ’yar Saul, sarkin Isra’ila na farko, kuma yanzu matar sarkin Isra’ila na biyu da muhimmanci ainun. Wataƙila ta ji cewa bai kamata mijinta sarki ya ƙasƙantar da kansa ya yi daidai da talakawa kuma yana biki da su ba. An ga wannan halin girman kai a yadda ta gai da Dauda sa’ad da ya dawo gida. Ta yi masa gatse ta ce: “Ina misalin darajar sarkin Isra’ila yau, da ya buɗe asirinsa yau a idanun kuyangin bayinsa, kamar yadda su ashararu su kan buɗe asirinsu babu kunya.”—2 Samu’ila 6:20.
Menene Dauda ya yi game da wannan sūkar? Dauda ya tsauta wa Mikal cewa Jehobah ya zaɓe shi a madadin mahaifinta Saul. Dauda ya daɗa cewa: “Sai kuma in ƙasƙanta gaban wannan, in ƙasƙanta kuma a wurin kaina: amma ga wajen kuyangin da kin ambata, a wajensu zan sami daraja.”—2 Samu’ila 6:21, 22.
Hakika, Dauda ya ƙuduri aniya ya ci gaba da bauta wa Jehobah da tawali’u. Wannan halin ne ya taimake mu mu fahimci abin da ya sa Jehobah ya kira Dauda “mutum gwalgwadon zuciyata.” (Ayyukan Manzanni; 1 Samu’ila 13:14) Hakika, Dauda ya bi misalin tawali’u mafi kyau, wato, na Jehobah Allah. An samu furci da Dauda ya yi amfani da shi sa’ad da ya ce wa Mikal, “in ƙasƙanta” daga wani aikatau na Ibrananci, da aka yi amfani da shi wajen kwatanta yadda Allah yake ɗaukan ’yan adam. Ko da Jehobah ne mafi girma a dukan sararin samaniya, Zabura 113:6, 7 sun kwatanta cewa yana “ƙasƙantarda [mutum ya rage matsayinsa ko daraja wajen sha’ani da talakawa] kansa domin ya duba abubuwan da ke cikin sama da duniya? Ya kan tada matalauci daga cikin turɓaya; ya kan ɗaukaka mai-mayata daga cikin jibji.”
Tun da yake Jehobah mai tawali’u ne, ba abin mamaki ba ne da ya ƙi “idanu masu-alfarma” na mutane masu fahariya. (Misalai 6:16, 17) Da yake ta nuna wannan mugun hali kuma ta yi rashin biyayya ga wanda Allah ya zaɓa ya zama sarki, an hana Mikal zarafin haifa wa Dauda ɗa. Ta mutu babu ’ya’ya. Wannan darassi ne mai muhimmanci a gare mu! Dukan waɗanda suke son su sami amincewar Allah dole ne su yi biyayya da wannan kalmomi: “Ku ɗaura wa gindinku tawali’u, da za ku bauta ma juna: gama Allah yana tsayayya da masu-girman kai, amma yana bada alheri ga masu-tawali’u.”—1 Bitrus 5:5.