Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 8/1 pp. 30-31
  • Taimaka wa Matasa da Gargaɗi a Kan Lokaci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Taimaka wa Matasa da Gargaɗi a Kan Lokaci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Dubi . . . Sababbin Shaidu 15,000!”
  • “Sun Zo a Lokaci da Ya Dace”
  • “Ya Ƙosar da Yunwarmu”
  • Ku Dage Kuna Cikakku Masu Haƙƙaƙewa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ku Taimake Wasu Su Yi Zaman Da Ya Cancanci Bautar Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Matasa, Ku Ƙarfafa Muradinku Na Bauta Wa Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 8/1 pp. 30-31

Ka Tsaya Cikakke Kana Tabbatawa

Taimaka wa Matasa da Gargaɗi a Kan Lokaci

ABAFARAS Kirista ne a ƙarni na farko wanda ya yi tafiya zuwa Roma. Domin wasu dalilai ya riƙa tunanin Kolossi, wani birni a Asiya Ƙarama. Ya yi wa’azin bishara a wajen kuma babu shakka ya taimake Kolossiyawa suka zama almajiran Yesu Kristi. (Kolossiyawa 1:7) Abafaras ya damu ƙwarai da ’yan’uwa masu bi a Kolossi, domin daga Roma manzo Bulus ya rubuta musu: “Abafras, . . . yana gaishe ku, kullum yana ƙwazo dominku cikin addu’o’insa, ku tsaya cikakku masu tabbatawa cikin dukan nufin Allah.”—Kolossiyawa 4:12.

Hakanan, iyaye Kirista mata da maza na zamani suke addu’a sosai domin ruhaniyar ’ya’yansu. Waɗannan iyayen suna ƙoƙari su saka ƙaunar Allah a zukatan ƙanƙanansu saboda su ma su tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya.

Matasa Kiristoci da yawa sun nemi taimako wajen bi da kalubale da suke fuskanta a makaranta da kuma wasu wurare. Wata yarinya ’yar shekara 15 ta ce: “Matsalolinmu suna ƙara muni. Rayuwa tana razanarwa. Muna bukatar taimako!” An amsa irin wannan roƙo na matasa da kuma addu’o’in iyaye masu ibada kuwa? E! An yi tanadin gargaɗi daga Littafi Mai Tsarki ta wajen “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Matta 24:45) Dubi wasu littattafai da suka taimake dubban matasa ‘su tsaya cikakku suna tabbatawa.’ Bari mu ga kaɗan daga cikin waɗannan littattafai.

“Dubi . . . Sababbin Shaidu 15,000!”

A Agusta 1941, masu sauraro 115,000 suka taru a St. Louis, Missouri, U.S.A., a taro mafi girma na Shaidun Jehovah da aka yi har zuwa lokacin. A ranar ƙarshe—“Ranar Yara”—yara 15,000 sun zauna suna sauraro kusa da dakalin magana yayin da Joseph F. Rutherford ya ba da jawabi a kan batun nan “Yaran Sarki.” Kusan ƙarshen jawabinsa, Rutherford ɗan shekara 71 ya faɗa da murya ta uba:

“Dukanku . . . yara da ku ka yarda . . . za ku yi wa Allah da kuma Sarkin da ya naɗa . . . biyayya, don Allah ku tashi tsaye.” Yaran suka tashi kamar mutum guda. “Duba,” in ji Ɗan’uwa Rutherford, “sababbin shaidu na Mulki fiye da 15,000!” Aka fashe da tafi. Sai mai jawabin ya daɗa cewa: “Dukan waɗanda za su yi iyakar ƙoƙarinsu domin su gaya wa wasu game da mulkin Allah, su ce E.” Yaran suka amsa da babbar murya “E!” Sai ya nuna sabon littafin nan Children, wanda aka yi masa maraba da tafi na dogon lokaci.

Bayan wannan jawabi mai motsawa, dogon layi na yara ya hau kan dakalin magana, inda Ɗan’uwa Rutherford ya ba su kyautar sabon littafin. Abin ya sa masu sauraro suka yi hawaye. Wani da ya ga abin da ya faru ya ce: “Sai dai zuciyar ƙarfe ce ba za ta motsa ba ganin matasa suna [nuna] cikakkiyar dogara da kuma bangaskiya ga Jehovah Allahnsu.”

A wannan taron da ba za a manta ba, matasa 1,300 suka yi baftisma domin keɓe kansu ga Jehovah. Yawancinsu sun kasance da ƙarfi cikin bangaskiya har zuwa yau. Suna ikilisiyoyi a yankuna dabam dabam, sun ba da kai a Bethel, ko kuma suna hidima na masu wa’azi a ƙasashen waje. Babu shakka, “Ranar Yara” da kuma littafin nan Children sun taɓa zuciyar yara da yawa!

“Sun Zo a Lokaci da Ya Dace”

A shekarun 1970, Shaidun Jehovah sun wallafa ƙarin littattafai uku da suka taɓa zukatan ɗarurruwan matasa. Sune Saurarawa ga Babban Malamin, Your Youth—Getting the Best out of It, da kuma Litafi Na na Labarun Bible. Kuma daga shekara ta 1982 talifin nan “Young People Ask . . . ” ya fara bayyana a jaridar Awake! Waɗannan suna taɓa zukatan yara da manya. “Kowane dare ina yi wa Allah godiya da ya sa ake buga su,” in ji wani ɗan shekara 14. “Ina son talifofin,” in ji wata ’yar shekara 13, “suna zuwa a lokaci da ya dace.” Iyaye da kuma dattawa Kiristoci da aka naɗa sun yarda cewa waɗannan talifofin suna zuwa a lokaci da ya dace kuma suna da amfani.

A shekara ta 1989 an riga an buga talifofin “Young People Ask . . . ” guda 200 a cikin Awake! A Taron Gunduma na “Ibada” a shekarar, aka fito da littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work. Ya taimake matasa su tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya kuwa? Matasa uku suka rubuta: “Wannan littafin abu ne mai kyau gare mu, wajen fahimtar damuwarmu da kuma sanin yadda za mu bi da su. Muna godiya domin damuwarku da mu.” Matasa da yawa da suke karatu a dukan duniya sun yarda da haka.

“Ya Ƙosar da Yunwarmu”

A shekara ta 1999, Shaidun Jehovah sun fito da wani salo na gargaɗi a kan lokaci domin matasa—kaset na bidiyo Young People Ask—How Can I Make Real Friends? Ya sa an yi na’am sosai da kyau. “Wannan bidiyon ya taɓa ni ƙwarai,” in ji wata yarinya ’yar shekara 14. “Zai kasance sashen abincinmu na ruhaniya a kai a kai,” in ji wata gwauruwa. “Yana daɗaɗa zuciya a sani cewa Amininmu, Jehovah, da gaske yana ƙaunarmu kuma yana kula da matasa da suke cikin ƙungiyarsa ta dukan duniya,” in ji wata mace.

Menene bidiyon ya cim ma? Matasa suka ce: “Ya taimake ni in yi hattara da abokane na, in yi abokane cikin ikilisiya, kuma in yi abokantaka da Jehovah.” “Ya taimake ni na tsaya tsayin daka ga tsararrakina.” “Ya ƙarfafa ni a ƙudurina na bauta wa Jehovah gwargwadon iyawa.” Kuma wasu mata da miji suka rubuta: “Muna yi muku godiya daga zukatanmu da yi mana tanadin wannan ‘abincin.’ Ya ƙosar da yunwarmu.”

Aminci da aikin da Allah ya ba shi “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi tanadin abinci na ruhaniya a kan lokaci ga dukan waɗanda za su karɓe shi. Kuma abin farin ciki ne a ga yadda wannan gargaɗi na Nassosi yake taimakon matasa a yau su “tsaya cikakku masu tabbatawa cikin dukan nufin Allah”!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba